Yadda muka tsira a harin Boko Haram a Masallacin Sarki — Babban Limamin Kano
Ya ce har Bebeji kakatar shi ta bi shi don kula da shi a makaranta.
- ‘Abin da na ji lokacin da aka nada ni Liman’
- Yadda kakata ta bi ni Bebeji don kula da ni a makaranta
Farfesa Sani Zaharadden shi ne Babban Limamin Kano, a tattaunawarsa da Aminiya ya tabo tarihin kujerar babban limamin Kano da yadda aka yi ya tsira daga harin bam din da ’yan Kungiyar Boko Haram suka kai Babban Masallacin Kano a shekarar 2016 a daidai lokacin da ya tayar da Sallah da sauran batutuwa:
Mene ne takaitaccen tarihin rayuwarka?
An haife ni a cikin birnin Kano. Amma na tashi a garin Kura a hannun kawuna dan uwan mahaifiyata Alhaji Mustapha Usman. A can na yi firamare bayan na yi aji daya. Daga nan sai aka yi masa canjin aiki zuwa Bidda hakan ya sa na koma makarnatra elemantare ta Bebeji ina aji uku, sai aka yi masa canjin aiki ya dawo Kano don haka muka koma Kano, inda na karasa karatun firamarena a Makarantar Shahuci.
Sai na shiga Makarantar Sakandare ta Rumfa a 1961 zuwa 1963 daga nan sai na samu shiga Makarantar SAS inda na zurfafa karatuna na gaba da sakandare a bangaren Larabci da Nazarin Addinin Musulunci.
Lokacin da zan fara karatun digiri sai na nemi Jami’ar Ibadan kasancewar a lokacin su kadai ke yin kwas din Larabci da Addinin Musulunci. To ina niyyar tafiya sai kuma Jami’ar Ahmadu Bello ta bude Sashen Larabci da Addinin Musulunci inda aka bude a Kano da sunan Kwalejin Abdullahi Bayero.
Mu ne dalibai na farko a nan na yi digirina na farko daga 1964 zuwa 1966. Da muka gama sai aka dauke mu aiki a wannan wurin ni da marigayi Farfesa Umar Gwandu da Farfesa Abubakar Balarabe muka fara koyarwa.
Daga baya kuma sai muka tafi Jami’ar Khartum da ke Sudan muka yi digiri na biyu. Da muka gama sai muka dawo muka ci gaba da koyarwa. Muna nan a Jami’ar Bayero muka ci gaba da aikin koyarwa inda har muka kai matsayin Farfesa. Bayan mun taka makamai dabandaban daga baya kuma na zama Shugaban Jami’ar Bayero.
Ko za mu san yawan iyali?
Ina tare da matata guda daya wacce ’yar uwata ce kuma har yanzu muna tare. Mun yi aure a 1966 zuwa yanzu shekara 55 ke nan. Muna da ’ya’ya takwas. Daya ya rasu mai suna Usman Allah Ya gafarta masa. Saura bakwai na raye. Maza biyu ne sauran duk mata ne. Ina da jikoki kusan 23.
Me za ka iya tunawa na kuruciya?
Lokacin da nake makaranta a Bebeji sai kakata ta taso daga Kiru ta dawo Bebeji saboda ni. Saboda haka ba zan taba manta wannan ba. Kuma har gobe ina yi mata addu’a, saboda ta sadaukar da ranta da rayuwarta duk saboda ni. Haka kuma da muka dawo Kano tare da ita muka taso. Haka ta ci gaba da kulawa da ni.
Ta yi min kyakkyawan raino, ta rike ni sosai. Haka shi ma kawuna ya dauke ni kamar dansa, ya dauke ni kamar ni ne babban dansa, duk da cewa yana da babbar ’yarsa. Haka muka taso a gidan daga ita sai ni.
Yawanci sai kawuna ya ce ai ita baiwata ce, to ni ban san ma’anar hakan ba, kin san ana cewa hakan a tsakanin abokan wasa, ’ya’yan mata da ’ya’yan maza. Idan kawuna ya fadi haka sai in ce masa, to ashe zan iya dukanta tunda baiwata ce.
Haka kuma zan iya tuna abokaina na kuruciya musamamn wadanda muka yi karatu tare a makarantar Midil wadansu har yanzu muna tare. Kamar su Malam Mijinyawa Allah Ya gafarta masa, shi ne mahaifin Farfesa Muhammad Sani Mijinyawa. Akwai Alhaji Aminu Wali, shi ma dan ajinmu ne.
Akwai kuma Alhaji Gwadabe Satatima, shi ya yi kokarin shiga siyasa Allah Ya yi masa rasuwa. Sai Musa Kofar Mata, sai Abdulhamid Hassan, muna tare da shi, shi ya karbi Kwamishinan Ilimi a hannuna a 1979.
Mene ne tarihin wannan kujera ta Babban Limamin Kano?
Kakanmu shi ne Muhammad Zara yana tare da Sheikh Usman Dan Fodiyo sai ya ce masa Muhammadu ina so ka tafi Kano, ina so ka rika yi musu Sallah a can. Wannan shi ne asalin zuriyyarmu.
Da ya zo Kano tare da dansa Muhammadu Hammadu wanda shi ne kakan kakana. To sai ya zauna a nan Yakasai yana zuwa Yola yana yin Sallah sai daga baya Muhammad Jali dan uwa ne gare shi, ya tambayi Shehu Usman cewa shi bai taba haihuwa ba, sai shi Jalli ya ce Allah Ya gafarta Malam idan mutum ba ya da ’yan uwa yaya zai yi zuriyarsa ta ci gaba, don kada sunansa ya bata. Sai ya ce masa ai kawai ka gina masallaci.
To shi ne ya zo ya gina Masallacin Juma’a a nan Yakasai shi ne za ku ji ana cewa Masallacin Jalli. Shi kuma da yake Muhammad Zaharadden dan uwansa ne, sai ya ce Muhammad ga masallaci mun gina, ai ba sai ka rika tafiya zuwa Yola ba, to shi ke nan sai yake Sallah a nan. Bayan nan, sai Sarkin Kano Dabo ya nada shi Limamin Kano, ya yi shekara 28 yana limanci.
Bayan ya rasu sai dansa Hamman ana ce masa Muhammadu Hamman ya gaje shi, bayan Hamman ya rasu a zuriyarsa sai Umaru wanda yake shi ne kakan su marigayi Liman Kuliya da Dan Ammar na yanzu Ali Harazumi, wanda yake mahaifin Dokta Bashir na Masallacin Al-Furkan, duk dai zuriyarmu daya. Ina ganin yanzu mun samu limamai 8 ko 9 daga zuriyarmu.
Alhamdulillah Umar da Hamman duk ’ya’yan Zara ne. Umar su ne kakan Kuliya a ’ya’yansa akwai Muhammad Dikko ya yi Limamin Kano, akwai Umaru da Usman shi ne ake kira Limamin Kano Manu, shi ne kakan Kuliya mahaifinsa ne, sannan Kuliya ya yi, sannan na yi.
Wani abu a zuriyar nan shi ko da ka gaji limanci ba sai kana da ilimi. Kuma alhamdulillahi, Allah Ya yassare mana akwai yaranmu har yanzu suna karatu, kuma ga Dokta Bashir kwanan nan zai zama Farfesa a Nazarin Addinin Musulunci, Allah Ya yi masa yalwar ilimi a fannin Larabci da Ingilishi.
Kodayake da farko shi Bashir ya fara zama injiniya ne, sannan ya bari ya koma fannin addini. Lokacin da aka nada ka Babban Limamin Kano yaya ka ji? Na ji dadi sosai.
Wani abun burgewa shi ne an haife ni a ranar 22 ga Yuni an kuma sanar da ni an ba ni Limamin Kano a ranar 23 ga Yunin 2011. Zan iya tunawa a ranar ina gida sai ga marigayi Malam Isa Waziri ya zo gidana.
Da aka gaya min na yi mamaki yadda Wazirin Kano zai zo har gidana? Na zo na same shi muka gaisa ya sanar da ni cewa Sarki ne ya turo shi ya sanar da ni cewa ya nada ni Limamin Kano. Ya ba ni alkyabba da rawani da kandirina. Wannan ya faru ne bayan rasuwar Limamin Kano Kuliya.
Akwai lokacin da kana jan Sallah ’yan Boko Haram suka kai hari a kan masallata inda mutane da dama suka rasu, yaya aka yi ka tsira daga harin?
Zan iya tunawa lamarin ya faru a ranar 28 a Nuwamban shekarar 2014. Bayan na yi huduba na sauko, an tayar da Ikamar Sallah, na ce Allahu Akbar ke nan, sai na ji hayaniya a baya, can sai na ji tashin bam.
Sai na ji mutane suna cewa Allahu Akbar! Allahu Akbar!! Daga can baya wuri ya yamutse. Sai na ji mutane suna La’ilaha illallah suna matsowa gaba suna matsowa jikinmu.
Muna jiyowa suna harbi. Mu dai muna nan muna ta salati can sai dana wanda yana wajen masallacin ya shigo yana ta cewa a koma ciki, harbi ake yi a waje. Ashe mu ba mu suni ba sun raba kawunansu, wadansu suna waje, wadansu kuma suna ciki, ba su yi harbi a ciki ba, amma sun sa bam a ciki.
Wuri ya hargitse sai can d wuri ya lafa sai dana ya ce za mu iya fitowa, muka fito muka shiga mota ya fitar da mu ta bayan masallaci, a gaskiya mun auna arziki. Daga baya muka samu labarin cewa mutane da yawa sun rasu.
Wani ma’aikacin jinya ya gaya min cewa wajen mutum 500 ne suka rasu. Ban da Allah Ya sa dakin masallacin daki ne irin na da, yana da kwari matuka, to da Allah ne kadai Ya san abin da zai faru.
Mu dai mun samu mun tafi gida a ranar sai a gida muka yi Sallar Azahar saboda wurin ne ya hargitse. Ba masallacin da abin ya faru ba hatta masallatai na kusa ma sun samu rashin natsuwa.
Wane sako kake da shi ga al’umma?
Sakona shi ne kamata ya yi matasa ku tsaya ku zama masu jajircewa a cikin sha’anin rayuwa gaba daya. Su tsaya kan gaskiya, idan aikin za ka yi ka yi shi bisa amana, duk abin da aka ba ka rike amana.
A kullun ya zama kana aiki da wani Hadisi na Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi, inda yake fadi lokacin da wani mutum ya tambaye shi ya ce ‘Me zan yi ya Rasulillah? Sai ya ce masa “Ka yi imani da Allah sannan kuma ka zama mai fadin gaskiya. Wani abu mummuna ka rufe shi da mai kyau.”
Matasanmu ku rike amana, abin da muka rasa ke nan, ko’ina babu amana, babu a wajen aiki, babu a wajen ciniki ko a wajen siyasa. Karya ta yi yawa, shugaba ya rika karya, ba ya sassautawa. Saboda haka komai za ku yi, ku yi gaskiya. Sannan a yi ta addu’a.