…‘Yadda muka tsira daga Bama’

Mutanen da suka yi hijira daga garin Bama zuwa Maiduguri sakamakon harin da’yan kungiyar Boko Haram suka kai a garin a ranar Litinin, na ci gaba da bayyana yadda harin ya gudana da kuma yadda aka yi suka zille daga garin. ’Yan bindigar dai sun kai hari barikin sojoji na bataliya ta 202 da ke […]

…‘Yadda muka tsira daga Bama’
…‘Yadda muka tsira daga Bama’

Mutanen da suka yi hijira daga garin Bama zuwa Maiduguri sakamakon harin da
’yan kungiyar Boko Haram suka kai a garin a ranar Litinin, na ci gaba da bayyana yadda harin ya gudana da kuma yadda aka yi suka zille daga garin.
’Yan bindigar dai sun kai hari barikin sojoji na bataliya ta 202 da ke Baman inda suka kwace shi a yunkuri na biyu, kamar yadda wani ganau mai suna Kachalla Modu ya shaidawa wakilinmu cewa “sun shiga barikin sojan sun kashe sojoji da fararen hula sun kuma sun kame muhimman wurare.”
Wani wanda ya yi gudun hijira daga Bama mai suna Bana Bukar, ya ce, “Sun kawo mana hari a Bama mun gudu zuwa barikin soja domin mu fake amma suka biyo mu muka shiga fito da bindigogi su ka yi ta kashe mutane har da sojoji da kyar na tsira na bi ta Konduga na shiga ta Kawuri na shigo Maiduguri, kuma muna da yawa wadanda muka shigo Maiduguri domin neman tsira, a yanzu haka ban san inda iyalina suke ba, domin ina ta buga wayarsu amma ban samu ba.”
Shaidu sun ce akasarin jami’an tsaro da jama’ar garin Bama sun yi gudun hijira zuwa Maiduguri da wasu wuraren.
Bayanai sun ce ’yan bindigar ba su kame garin Bama ba, kungiyar Sibiliyan JTF ta Jihar Borno ta karyata jita-jitar cewa ’yan Boko Haram sun kwace garin Bama, kamar yadda kakinsu Barista Jibrin Gunda ya shaida wa manema labarai a garin Maiduguri.
Barista Gunda, ya ce, “Babu shakka’yan bindigar sun kai hari Bama, to, amma babu wani abu makamancin kwace garin Bama, wannan zance karya ne babu kanshin gaskiya, yaranmu sun je Bama da suka ji abin ya faru kuma sun kwana sun dawo sun tabbatar mana cewa babu wani abu mai kama kwace garin Bama.”
Ya ce a yanzu haka mutanen da suka gudu daga Bama suna komawa gida, maganar kwace garin ba gaskiya ba ce kamar yadda Sanatan Borno ta Tsakiya Khalifa Ahmed Zanna da wani da ya fito daga Bama suka fada wa Rediyon BBC ba.
Ita ma gwamnatin Jihar Borno ta musanta kame garin Bama da aka ce Boko Haram sun yi, inda Mataimakin Gwamnan Jihar Alhaji Zanna Umar Mustafa ya fada wa manema labarai a Maiduguri. Ya ce jami’an tsaro sun tabbatar musu cewa iko da garin Bama na hannun soja, kuma yanzu haka sun karbi ’yan gudun hijira sama da dubu biyu daga Bama.
Rundunar sojojin Najeriya ta ce ta kashe maharan sama da 50 a gumurzun na Bama, a yayin kuma da jiragen yaki ke ta shawagi a sararin samaniyar garin.

An fara sana’ar hayar Fawa-bank a Kano

’Yan sanda sun kama fasinja ya ɓoye bindiga a cikin burodi 

An kama fasto kan kashe ’yar shekara 13 da duka

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya