‘Yadda muka tsira daga gobara a makarantarmu’
Kimanin ’yan mata 7 ne suka rasa rayukansu a sakamkaon gobarar da ta tashi a daya daga cikin dakunan kwanan dalibai da ke Makarantar ‘Yan mata ta Gwamnati da ke Jogana a yankin karamar Hukumar Gezawa, cikin Jihar Kano. Rahotanni sun bayyana cewa gobarar ta tashi ne da misalin karfe 8: 00 na dare daidai […]
Kimanin ’yan mata 7 ne suka rasa rayukansu a sakamkaon gobarar da ta tashi a daya daga cikin dakunan kwanan dalibai da ke Makarantar ‘Yan mata ta Gwamnati da ke Jogana a yankin karamar Hukumar Gezawa, cikin Jihar Kano.
Rahotanni sun bayyana cewa gobarar ta tashi ne da misalin karfe 8: 00 na dare daidai lokacin da daliban suka kwanta barci.
Har zuwa yanzu dai ba a gano musababbin faruwar wutar ba, kasancewar daliban sun bayyana cewa a lokacin da wutar ta tashi babu ma wutar lantarki a makarantar. Sai dai an gano cewa wutar ta ci gaba da ruruwa ne sakamakon narkewa da kwanukan alminiyon na rufin dakin suka yi.
Baya ga daliban da suka kone sakamakon wutar, wasu kuma sun sami raunika a lokacin da suke kokarin gudu don neman tsira.
Hadiza Muhammad tana daga cikin daliban da suka samu raunuka, ta shaida wa Aminiya cewa suna kwance a daki, ba su san me ke faruwa ba, sai suka ji hucin wuta yana tashi. “Ni dai ba mu san hawa ba, ba mu san sauka ba, muna kwance mun fara barci sai hucin wuta muka ji, baya ga ihun ’yan uwanmu dalibai. Hakan ya sa muka fito da gudu, sai dai ko kafin mu fita daga dakin tartsatsin wutar ya kona mini jiki” Inji ta.
Wata daliba da ta samU raunika sakamakon gudun tsira da ta yi mai suna Fatima Abdullahi, ta shaida wa Aminiya yadda lamarin ya faru inda ta ce: “Kasancewar muna da tes ranar Litinin, idona biyu ina karatu sai na ji ana ihu a dakin kwana na 2. Hakan ya sa mu ma muka fito daga namu dakin muka nufi kofar fita. To sakankon gudun da muke yi na fadi inda kuma wasu suka fado min a kafa, wanda hakan ya sa na samu rauni a kafata.” Inji ta.
Binciken Aminiya ya gano cewa wanann shi ne karo na hudu gobara tana tashi a wannan makaranta, wadda mafi yawan jama’ a suke danganta lamarin da aljanu. Wani wanda ya nemi a boye sunansa wanda kuma uba ne ga daya daga cikin daliban makarantar, ya bayyana cewa: “Wanann shi ne karo na hudu gobara tana tashi a wanann makaranta saboda haka muke kira ga gwamnati da ta tsaya ta binciko dalilin da yake kawo wanann wuta. Wasu kuma suna fadin cewa aljanu ne ke tayar da wutar, to idan an bincika hakan ne to ya kamata shugabar makarantar ta rika sanya wa ana saukar karatun Alkur’ani don neman tsari daga shaidanu.”
A lokacin da ya kai ziyara makarantar da kuma duba daliban da suka sami raunika, Mataimakin Gwamnan Jihar Kano Farfesa Hafiz Abubakar wanda kuma shi ne Kwamishinan Ma’aikatr ilimi ta jihar, ya jajanta tare da yi wa iyayen da ’ya’yansu suka rasu ta’aziya; inda kuma ya bayyan cewa gwamnati za ta dauki nauyin magungunan daliban da suka sami raunika a dalilin tashin gobarar.
Ya bayyana cewa har yanzu ba a gano dalilin faruwar wutar ba, sai dai a cewarsa nan ba da dadewa ba za a kafa kwamitin da zai binciki dalilin tashin gobarar tare da bayar da rahoton yadda za a gyara dakunan kwanan daliban da suka kone. Ya kuma bayar da umarnin rufe makarantar har zuwa wani lokaci da ba a ambata ba, domin ba iyaye da daliban makarantar damar jajanta rashin da suka yi.