Yadda muka tsira daga harin Boko Haram – wani Direba
Wani Direba mai suna Muhammadu Adamu dan asalin jamhuriyar Benin, mai zirga-zirga tsakanin kasashen Najeriya da Kamaru, wanda ya samu tsira daga harin da ‘yan kungiyar Boko Haram suka kai garin Gamboru Ngala makon da ya gabata, inda mutanen garin da dama suka tsere zuwa kasar Kamaru , don ceton rayukansu daga masu tada kayar […]
Wani Direba mai suna Muhammadu Adamu dan asalin jamhuriyar Benin, mai zirga-zirga tsakanin kasashen Najeriya da Kamaru, wanda ya samu tsira daga harin da ‘yan kungiyar Boko Haram suka kai garin Gamboru Ngala makon da ya gabata, inda mutanen garin da dama suka tsere zuwa kasar Kamaru , don ceton rayukansu daga masu tada kayar bayan, inda ya bayyana abin da ya gani ya farun da cewa tashin hankali ne da bai taba gani ba a rayuwarsa.
Malam Muhammadu Adamu, ya ce, wannan abin da ya faru wani tashin hankali ne mai ban tsoro, domin abin ya zo mana ba zata. Muna nan da misalin karfe hudu na yamma, muka fara ji garin Gamboru ya rude da harbin bindigogi babu kakkautawa ko ta ina, kuma ba irin kananan bindigogi ba ne; suna ta barin wuta, kafin ka ce kwabo mutanen gari sai suka fara gudu ba shiri suna shigar jamhuriyar ta kamaru, wasu kuwa suka fada daji basu san ko ina suka nufa ba.
A cewarsa: “ Cikin dare suna ta harbin mutane ido a rufe sai gawarwaki kake ganinsu birjik akan titunan garin da waje.”
“Kuma wadannan da kuke jin cewa Boko Haram, matasa ne dauke da bindigogi a cikin maye suke, suna bin mutane suna harbinsu, tare da kwashe ganima da kona gidajen jama’a a cikin garin. Ni kaina sai da suka kuskure ni da harbin bindiga, ka ga hannuna na fadi kasa na rika ina mirgina cikin duhu, a tsakanin wasu motocin da muka ajiye su, har sai da na samu na fita bakin daji, sai na fara gudu a firgice, ban tsaya ba, har na tadda wasu mutanen suma suna kokarin tsirar da ransu . Sai muka hadu, muka ci gaba da tafiya a cikin dare, cikin daji, har Allah ya taimake mu muka fada wata hanya kusa da wani kauye, ban san sunan wannan kauyen ba. A cikin Kamaru a nan ne gari ya waye mana,” inji shi.
Ya ce, bayan wayewar gari sai muka kara yin gaba direbobi na Kamaru su ne suka taimakemu, da suka ga halin da muke ciki suka daukemu zuwa garin Duwala, inda suka kaimu wurin Sarkin Hausawa na garin, kuma wannan Bawan Allah ya yi mana alheri ba kadan ba.
Daga baya na ji labarin cikin motocin da suka kona har da motata da lodin da ke ciki, sai dai Alhamdu lillahi, tunda na samu na tsira da raina , zan koma kasar mu, Jamhuriyar Benin domin kafin in bar garin Gamboru babu wani sojan Najeriya daya da na gani a garin, ko kafin haka ya faru ma, muna zaman dar dar ne babu tabbas, a cewarsa.