‘Yadda muka tsira daga harin Dalori’

Da yammacin ranar Asabar din da ya gabata ne wadansu ‘yan bindigan da ake zaton ‘yan kungiyar Boko Haram ne suka kai hari kauyen Dalori da ke yankin karamar Hukumar Konduga  a cikin jihar Borno, wanda ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane da dama tare da raunata dimbin mutane  da kone akasarin gidajen kauyen.kauyen Dalorin […]

‘Yadda muka tsira daga harin Dalori’
‘Yadda muka tsira daga harin Dalori’

Da yammacin ranar Asabar din da ya gabata ne wadansu ‘yan bindigan da ake zaton ‘yan kungiyar Boko Haram ne suka kai hari kauyen Dalori da ke yankin karamar Hukumar Konduga  a cikin jihar Borno, wanda ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane da dama tare da raunata dimbin mutane  da kone akasarin gidajen kauyen.
kauyen Dalorin dai bai wuce nisan kilomita 6 daga garin Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno ba, kuma hanya ce ta zuwa garuruwan Bama da Gwoza, wadanda a da suke karkashin Boko Haram.
Malam Yusuf Muhammad, yana daya daga cikin wadanda suka kubuta daga wannan mummunan harin, ya bayyana wa Aminiya cewa, ’’Su dai wadannan mahara sun shigo ne da yammaci, da misalin karfe 6, sanye da kayan soja da motocinsu  A-kori –kura kirar Toyota HILUd guda 9 da kananan motoci da babura da kuma wata motar Igwa, kai da dai muggan kayan yaki. Mu mutanen gari muna zaton sojoji ne, har mun saki jiki, amma daga baya sai muka ga abin ba haka ba ne. Sai suka dunfari mutane suna ta harbi na kan mai-uwa-da-wabi tare da kona gidaj.’’
“A lokacin da suka harbi wani makwabcina sai muka kai gudunmuwa wurin, kafin ai haka, sai wadansu mata suka shiga cikin mutane suka tayar da bam, a nan ne aka samu rasuwan akasarin mutane. Ni ban riga na isa wurin ba, kawai sai na ji tashin ba, a nan na fadi, saboda duk mun rude babu wani wanda yake cikin hayyacinsa.’’
“Ganin sun zagaye garin babu inda mutum zai fita, da na tashi sai na haye itace a nan bakin gari, ina ta kallon irin barnar da suke yi, idan suka kashe mutane sai su je su kona gidajensu, sannan sai su kwashe kayayyakin abinci su jefa a motocinsu. A gaskiya mutanen da suka kashe sunfi 100, amma ni na yi sa’a Iyalina su ma sun tsira, kodayake ni ma na tsira, amma da kyar. Domin wadannan maharan sun kwashe sama da sa’o’i uku suna kashe mutane da kone gidaje. Wanda kuma da kwanansa a gaba to yana cikin wahala, ni dai na sha wahala ne a saman itace, domin kuwa ban ci ba kuma ban shaba ba har garin Allah ya waye, ga Sanyi.’’
Ita ma Malama Falmata cewa ta yi ta tsallake rijiya da baya, amma  a kan idonta aka harbe wata makwabciyarta, ta kara da cewa, ’’Wallahi wannan kisan da suka yiwa makwabciyata ya girgiza ni, ba ni da abin da zan iya cewa, domin ni ma na dauka na mutu ne, amma Allah da ikonSa wannan hari bai same ni ba. Haka nake ta ganin ana harbe mutane suna fadi, gashi ana cinna wa gidaje wuta, amma ba abin da zan iya yi, ni dai kawai na sadakar  sun kashe ni.’’
“Ana cikin haka sai na ji tashin bam a bayanmu, ashe mutane da dama sun rasu, a ciki akwai yara biyu  kuma da surukata, to amma mu wadanda muka rage ba mu mutu ba mun kwana cikin wahala da jimami da kuma firgici, domin su wadannan maharan sun kwashe tsawon sa’o’i hudu suna barna a wannan kauye namu, domin kuwa sun kashe mutanen da babu adadi, sun kona gidaje kuma sun sace mana kayayyakin abinci, baya ga wancan bam din da suka tayar. Kai abin babu kyan gani, ni dai haka na kwana idona biyu kuma a wani cikin gidan da ba su kona ba. Ina kyautata zaton mutanen da suka kashe sun fi 100, ni ma da kyar na sha, domin kowa suka gani kashewa suke yi, babu babba babu yaro, ba namiji ba mace, domin suna harbin kan mai-uwa-da-wabi ne, kodayake wadansu sun fantsama cikin daji ne domin tsira da rayukansu. Kai na ga mutuwa kiri-kiri, ina rokon kar Allah Ya sake nuna mini irin wannan abu. Yanzu dai ka ga ba mu da ,komai babu kowa, wato ba mu da abinci kuma ba mu da muhali. Don haka muke rokon gwamnati ta taimaka mana ta tsamo mu daga irin wannan mummunan yanayi da muka shiga ciki babu zato babu tsammani, domin a yanzu haka ban san inda Maigidana yake ba, kuma yara guda biyu na fada maka an kashe ,su don ni na ga gawarwakinsu.’’
Wannan harin dai na zuwa ne a daidai lokacin da hukumomin tsaro ke ikirarin cewa suna samun nasara a yakin da suke yi da kungiyar Boko Haram din, sai dai kuma masana na ganin  akwai bukatar a kara matsa kaimi don kawo karshen wannan bala’in.