‘Yadda muka tsira daga matasa ‘yan ta’adda a Samarun Kataf ’
A ranar talatar makon da ake ciki ne da misalin karfe uku na rana wadansu gungun matasa dauke da wukake da adduna da itatuwa suka afka wa masu zuwa cin kasuwa a garin Samarun Kataf da ke karamar hukumar Zangon Kataf a kudancin jihar Kaduna, ba tare da sanin hawa ba balle sauka, inda suka […]

A ranar talatar makon da ake ciki ne da misalin karfe uku na rana wadansu gungun matasa dauke da wukake da adduna da itatuwa suka afka wa masu zuwa cin kasuwa a garin Samarun Kataf da ke karamar hukumar Zangon Kataf a kudancin jihar Kaduna, ba tare da sanin hawa ba balle sauka, inda suka tarwatsa jama’ar da ke cin kasuwar bayan sun sassari mutane suka kona musu kayayyaki, sannan suka sace na sacewa, sai dai babu wani takamaiman bayani da ke nuna cewa an yi asarar rai.
A lokacin wannan hari da babu wanda ya san dalilin yinsa, an ji maharan na cewa su ma an kashe musu dan uwa ne a rikicin da ya faru a Gidan Waya a farkon makon nan, don haka su ma suke daukar fansa, kamar yadda wadanda Aminiya ta zanta da su suka bayyana.
Aminiya ta zanta da wadansu daga cikin wadanda suka sha da kyar a garin na Samaru Kataf. Malam Sunusi Isa, dan shekara ashirin da biyar, wanda ya kwashe shekaru biyar yana zuwa cin kasuwar Samaru, wacce take ci duk ranar talata, ya shaida wa Aminiya cewa haka kawai suka ga an fara guje-guje, “muna tsakar cin kasuwa sai aka ce mana garin nan fa ba lafiya, shine sai na buga wa wani dan uwana mai suna Rabi’u waya, wanda har ya zuwa yanzun da nake hira da kai ba mu san inda yake ba. To da na kira shi a waya ya dauka na fada masa halin da ake ciki sai ya fito ya same mu, daga nan muka dunguma zuwa wajen da za mu buya, sai muka ga gungun matasan ta wajen, shi ne sai muka dawo da baya. Muna tsaye dai muna jiran hukuncin Allah, sai ga wani direba nan ya taho, shi ne sai muka roke shi ya dauko mu ya fara tafiya da mu. Mun wuce shinge na farko da suka saka a kan titi, mun wuce na biyu, to da muka iso na ukun shi ne suka fito da mu suka yi ta dukanmu, nan take suka jawo shi dan uwanmu da ba mu sake jin labarinsa ba, wani ya daga adda zai sare shi ya yi ta rokonsu, to bayan sun sake shi sh ine ya firgita ya tsallaka hanya to da ya yi nisa ya juyo ya hango mu daga can, shi ne sai ya yi yunkurin dawowa wajenmu, nan wasu gungun suka sake tare shi, mu kuma daga baya motar ’yan sanda ta kwaso mu da daddare ta dawo da mu Kafanchan, shi kuma dan uwanmu har yanzu ba mu san wane hali yake ciki ba, ko yana da rai ko ya mutu,” inji shi.
Shi ma Muhammadu Hamisu, wanda aka fi sani da Baban Umma ya ce suna tsakar cin kasuwa aka shaida musu cewa gari fa ba lafiya, daga nan sai ya fito bakin hanya don ganin abin da ke faruwa, ai ko nan take ya yi arba da gungun matasan dauke da sanduna da wukake da adduna, da zaran sun fahimci kai ba dan yankinsu ba ne sai su kama ka da sara da duka, suna lalata kayan sayarwanka.
Ya ci gaba da cewa, daga nan sai matasan suka shiga cikin tasha suna tambayar masu motocin, idan mota bat a dan yankinsu ba ne sai su sa mata wuta, “da yake muna daukar shatar mota ne daga Kafanchan zuwa cin kasuwannin kauyuka. To da muka ga direbanmu sai muka ce masa tunda Allah Ya sa ba a sa wa motarka wuta ba, to ka zo ka kwashe mu mu tafi, shi ne ya kwashe mu, da yake mu ne farko-farkon fita, haka muka yi ta wuce shingayen da suka sassanya a kan titi, da zaran sun tsare mota sai su tambaya idan akwai irin mutanen da suke nema a ciki sai su jawo shi su yi ta dukansa, mu ma sun tsare mu, amma dai Allah Ya kwace mu a hannunsu, bayan sun tambaye mu muka ce musu mu ’yan kasuwa ne sai suka bar mu muka wuce, amma a kan idona na ga motoci na cin wuta.”
Shi kuwa kabiru Hamisu, dan shekara talatin da takwas, yana kai atamfofi ne da sauran yadudduka kasuwar duk sati. Shi ma a nasa bayanin, ya bayyana wa Aminiya cewa, a lokacin da ya ga an fara kona taya ana saran mutane sai ya gudu zuwa shagon wani dan kabilar Ibo inda ya boye shi har zuwa lokacin da kura ta fara lafawa “sannan aka kira sojoji suka iso suka dauke ni tare da wasu, da misalin karfe sha daya na dare, mun je daukar motarmu a cikin tasha sai muka ga an riga an kona, shi ne sojojin suka dawo da mu ofishin ‘yan sanda aka debi wasu da suka samu mafaka a wajen suka kai su Zangon Kataf, mu kuma aka dawo da mu Kafanchan, wajajen karfe sha biyu na dare Ka ji yadda aka yi muka tsira. Amma wasu daga cikin ’yan uwana sun fantsama daji ne suna ta gudu har dare yayi musu kafin Allah Ya taimake su ya bullar da su daidai rugar wasu Fulani a wani waje da ake kira Kankada, bayan gari ya waye shi ne jami’an tsaro suka je suka kwaso su.”
Kasancewar garin na Samaru wata mahada ce, ta sanya motoci da yawa da suka fito ta hanyar Kaduna zuwa Kafanchan suka yada zango a Kachiya, bayan sun samu labari haka su ma wadanda suka fito ta hanyar Kano ta Unguwan Bawa suka yada zango a Zangon Kataf, yayinda wadanda suka fito daga Abuja ta hanyar Keffi ko wadanda suka fito ta Gidan Waya suka yada zango a Kafanchan.