Yadda muka yi bukukuwan Sallah – ’Yan gudun hijira
Akalla ’yan gudun hijira da yakin Boko Haram ya daidaita ya kuma raba su da muhallansu, sama da miliyan biyu ne suke zaune a sansanoni sama da 20, a Maiduguri inda suke gudanar da rayuwarsu cikin yanayi na ban tausayi kan yadda suka tsinci kansu a halin rayuwa na hannu baka hannu kwarya.Wakilinmu ya kewaya […]

Akalla ’yan gudun hijira da yakin Boko Haram ya daidaita ya kuma raba su da muhallansu, sama da miliyan biyu ne suke zaune a sansanoni sama da 20, a Maiduguri inda suke gudanar da rayuwarsu cikin yanayi na ban tausayi kan yadda suka tsinci kansu a halin rayuwa na hannu baka hannu kwarya.
Wakilinmu ya kewaya wasu daga cikin sansanonin da ke garin Maiduguri, don jin yadda suka gudanar da bukukuwan Sallah, inda daya daga cikinsu mai suna Malam Kachalla Ali, wanda ya fito daga yankin Kukawa kuma yake zaune a sansanin ’yan gudun hijira na Gidajen Malamai da ke Unguwar Bulunkutu, ya shaida masa cewa “A gaskiya babu abin da za mu ce sai godiya, mun gudanar da azumi cikin kwanciyar hankali da lumana duk da cewa akwai matsaloli da ba a rasa ba kamar karancin abinci da ruwan sha da kiwon lafiya ga yara da mata da tsofaffi. A gaskiya muna cikin mummunan yanayi a sansanonin nan, tunda ba gidajenmu ba ne, mun yi Sallah lafiya, amma yanzu babu abin da muke so illa mu koma garuruwanmu.”
Ita kuwa Malama Falmata Modu, ta ce ta gudanar da bikin Sallarta cikin mummunan yanayi ne, “Wallahi ni da ’ya’yana muna fama da karancin abinci da wahalar kayan bukatun yau da kullum. Duk da gwamnati tana kokari ana dafa mana abinci amma ba ya isarmu kuma sau daya ake raba mana abincin a wuni, kuma ba a ba mu a kan kari. Ga yawan rashin lafiya ga yara ga rashin ruwa, ’ya’yana bakwai, babansu Boko Haram sun kashe shi, mun zo nan sansanin gudun hijira ba mu da komai. Duk da mun tsira da rayukanmu, amma har yanzu muna ganin mutuwa a kusa da mu saboda mawuyacin halin da muka shiga na rayuwar hannu baka hannu kwarya. A lokacin azumi wata rana mukan yi bude baki ba tare da samun abin da za mu yi sahur ba, ko mu yi sahur ba bude baki,” inji ta.
Malam Musa Ali, wanda ya fito daga yankin Gwoza kuma yake zaune a sansanin gudun hijira na Bakassi, ya ce sun yi bukukuwan Sallar ba yabo ba fallasa. Ya ce “A gaskiya cikin azumi mun samu isashen abinci domin kafin azumi gwamnatin jiha da dangote sun raba mana kayan abincin da zai daukemu tsawon wata daya zuwa biyu mu da iyalanmu, yanzu dai abin da yake damunmu shi ne na yawan rashin lafiyar yara wadda za a iya cewa ciwon yunwa ko rana saboda rashin isashen abinci da zafin rana, amma mun gudanar da Sallah lafiya sai dai dan abin da ba a rasa ba.”
Ita kuwa Malama Adama cewa ta yi Sallar ta zo mata da ba-zata domin ba ta taba yin Sallah a wani wuri ba sai a gida. Ta ce “A gaskiya ban yi tsammanin zan yi Sallah a nan ba domin na saba duk shekara a gida nake Sallah amma saboda lalura bana na samu kaina a wannan sansani da ’ya’yana, kuma gaskiya ban ji dadin yin Sallah a nan ba, ban samu abincin da nake so a Sallah ba kuma ban dinka wa ’ya’yana kayan Sallah ba, hatta sahur da bude bakin da muke yi ba yadda rai ya so ba ne. Sai dai mun gode Allah tunda muka kubuta da rayukanmu sauran duk mai sauki ne, muna fata Allah Ya kawo karshen wannan bala’i mu koma gidajenmu.”
A Abuja inda bayanai suka nuna cewa akwai sansanonin ’yan gudun hijira 13, Aminiya ta ziyarci uku daga cikinsu da suka hada da na Durumi da na Sabuwar-Kuchigoro da kuma na Karmajiji, inda ’yan gudun hijirar daya daga cikin sansanonin suka yaba da yadda suka ce an taimaka musu a lokacin azumi da kuma bukukuwan Sallah, yayin da biyun suka koka kan yadda lamarin ya kasance musu.
Hadiza Umar da ke tare da mijinta a sansanin Durumi da ke daura da Eriya 1 a Abuja, ta yaba yadda aka taimaka musu a lokacin azumi da bikin Sallah inda ta ce wasu kungiyoyin da’awa sun taimaka musu da kayan abinci a tsawon watan azumi da kuma yanka musu shanu biyu a kullum. Ta ce a lokacin Sallah Shugaban karamar Hukumar Birnin Abuja, Malam Addullahi Adamu Candido ya kai musu shanu hudu da kayan abinci, kuma sun samu kyautar sutura don bikin Sallah daga wadansu bayin Allah.
Sansanin wanda ya kasu kashi biyu, killatacce da bangaren bacoci, yana da ’yan gudun hijira da suka haura dubu kamar yadda mazaunansa suka fadi, kuma matasa maza kan shiga gefen gari suna sana’ar kabu-kabu yayin da yawancinsu ke zaman kashe wando a cewarsu.
Sai da lamarin ba haka yake ba ga sansanin Sabuwar-Kuchigoro. Mataimakin shugaban mazauna sansanin, Malam Usman Adamu ya ce sun yi bikin Sallah cikin yunwa kamar yadda suka yi azumi ba tare da tallafin abinci ko abin yanka ba. Ya ce taimakon da ’yan gudun hijirar da ke Durumi suka samu daga kungiyoyin Da’awa ne ba gwamnati ba, don haka ba su yi yunkurin neman su ma sai an ba su ba.
Wakilinmu ya gano cewa ba wani abu da ke nuna ’yan gudun hijira da ke wurin na yin bikin Sallah sabanin na Durumi da ya samu suna dafe-dafe. Yawancin ’yan gudun hijirar da aka ce galibinsu mabiya addinin Kirista ne daga garin Gwoza kamar na yankin Durumi, suna zaman hira ne kawai, a yayin da wasu kuma ke wasan dara, yaransu kanana kuma ke tsalle-tsalle. Haka akwai tarin mata da ke layin dibar ruwa a wani buhol wanda mataimakin jagoran ya ce yana da karancin ruwa sakamakon karancin rana saboda damina.
Malam Usman Adamu ya ce rayuwa ta yi tsauri a tsakanin al’ummarsu kasancewar ’yan ayyukan leburanci da gine-gine da suka saba samu a sababbin yankunan da ake gina rukunin gidaje a yanzu sun ja baya, bayan kafuwar wannan gwamnati. Ya ce kokarin da Gwamnatin Tarayya ke yi na samar da tsaro musamman a Borno, zai fi ma’ana idan aka hada da taimaka musu. Ya ce za su koma yankunansu ne kawai idan sun kasance a raye yunwa ba ta kashe su ba.
Al’amarin duk kusan daya ne da sansanin ’yan gudun hijirar da ke Karmajiji, wadanda suka ce sun yi bikin Sallarsu ce cikin kunci ba babu abinci kamar yadda suka kasance a lokacin azumi, inji jagoransu Malam Saleh Musa.