Yadda muka yi da masu harin bam – Sheikh dahiru Bauchi
Sheikh dahiru Usman Bauchi babban jagora ne a darikar Tijjaniyya a duniya, kuma daya daga cikin malaman da ke da dimbin mabiya da ake girmamawa a Najeriya. Shi ne Mataimakin Shugaban Kwamitin Fatawa na Majalisar koli kan Harkokin Addinin Musulunci, ya tattauna da Aminiya a daidai lokacin da yake aikin Umara a Makka bayan ya […]
Sheikh dahiru Usman Bauchi babban jagora ne a darikar Tijjaniyya a duniya, kuma daya daga cikin malaman da ke da dimbin mabiya da ake girmamawa a Najeriya. Shi ne Mataimakin Shugaban Kwamitin Fatawa na Majalisar koli kan Harkokin Addinin Musulunci, ya tattauna da Aminiya a daidai lokacin da yake aikin Umara a Makka bayan ya tsallake harin bam da aka yi yunkurin halaka shi da kuma kokarinsa na sulhunta yan Boko Haram da gwamnati:
An samu tashin bam a garin Kaduna ranar da kuka rufe tafsirin azumin watan Ramadan da mutane da dama ke gani kai aka yi niyyar kashewa, yaya lamarin ya faru?
Muna godiya ga Allah Madaukakin Sarki Wanda Ya karemu, hakika bam ya tashi kusa da motata a kan hanyarmu ta komawa gida daga wajen da muka rufe tafsiri, ba abin da ya samu motar sai dai ta komade, kuma gilasan motar sun fashe, amma duk motocin da ke bin mu
Allah Ya kiyaye mu ba abin da ya same mu har muka isa gida. Hakika muna godiya ga Allah da Ya karbi addu’o’inmu, domin in mutum ya ga yawan mutanen da suka halarci rufe tafsirin ya kwatanta da abin da ya faru, hakika zai san Allah Ya karbi addu’armu Ya kiyaye mu sai dai muna jan hankalin jama’a mu kara yin addu’o’i domin samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya.
Ko ka taba samun wata barazana daga wasu da suke cewa za su kawo maka hari ko wani abu?
Ban taba samun wata barazana ba, su ’yan Boko Haram na ainihi shekara biyu da rabi da suka wuce sun ce idan na shiga tsakaninsu da gwamnati za su yarda a yi sulhu da su, saboda suna yarda ba zan yaudare su ba kamar yadda wasu suka yaudare su sau biyu. Kuma suna ganin ni ma gwamnati ba za ta yaudare ni ba, a lokacin Boko Haram da gaske suke yi, sai suka ce ka gaya wa gwamnati in suna so mu yi sulhu su ba mu takarda a rubuce, na gaya wa gwamnati kuma suka
yarda suka ba ni takardar sai aka yi kamar wata hudu ba a ce komai ba, na ce ya ya mun yi alkawura da ku iri-iri har yanzu ba a yi komai ba. Na ce za mu gaya wa gwamnati kada a kara kama kowa a cikinku, ku kuma kada ku sake kai hare-hare ko’ina har mu kai ga cimma yarjejeiyar yin sulhu. A cikin gwamnatin akwai wadanda ba sa son a yi sulhu kuma suna da
karfi, sai Boko Haram suka gane haka sai suka ja da baya. Kuma sun ce mini suna bukata a sa wannan takarda da gwamnati ta ba su a cikin Jarida don kowa ya karanta, na sa a ka sa wannan takarda a cikin jarida kowa ya karanta. Sai wadannan mutane da suke cikin gwamnatin suka lalata harkar, saboda Musulmi ake kashewa su kuma suna da ajanda mai karfi, kuma akwai samun kudi a ciki. Kuma tun lokacin da harkar ta lalace na daina magana da su tunda dama su ne suka neme ni.
Wa kake zargi da kai maka wannan hari?
Ba na zargin kowa.
Ba ka gani ko sabanin da ke tsakaninku da ’yan Izala zai sa su saka maka bam?
A’a sabanin da ke tsakanina da ’yan Izala irin su Bala Lau bai kai su sa mini bam ba, sai dai ’yan Izalar siyasa, amma ’yan Izala masu da’awar malanta cacar baki ne kawai muke yi. Su sun san inda suke mu kuma mun san inda muke amma gabarmu ba ta kai su sa mini bam ba, wani lokaci ma in mun hadu muna yin raha ne muna dariya, a tsaninmu da su kamar jirgin sama ne da mota suna tsere a filin jirgin sama in an kai gaci jirgi zai tsere ya bar mota, su sun san inda muke, gabarmu ba ta kai su sa mana bam ba, sai dai ’yan Izalar siyasa, komai za su iya yi.
Me kake nufi da ’yan Izalar siyasa?
Abin da nake nufi mu ’yan Tijjaniyya a Najeriya ba mu da wanda muka kullata a zuciyarmu cewa abokin gabanmu ne da Musulmi da Kirista, muna zaman lafiya da kowa, duk da cewa akwai sabanin ra’ayi a tsakaninmu. Kiristocin sun kasu kashi biyu, Musulmin ma haka, cikin Kiristoci akwai masu kaunar zaman lafiya da muke zaman lafiya da su irin su Janar Yakubu Gowon da Barista Solomon Dalung da RabaranYohanna Buru da mutanensu. Muna zaman lafiya da su har ma suna karrama mu suna zuwa muna shan ruwa da su da azumi, amma akwai wasu Kiristocin da shi Shugaban kasa ya san su Kiristocin siyasa ne da su ne suke sama wa Musulmi bam a Borno da Yobe da Adamawa da Taraba da sauran wurare, bukatarsu da yake zabe ya zo a karkashe Musulmi a ba kowa tsoro a raunata su don Kirista ya karbi mulkin Najeriya. Cikin Musulmin ma akwai ’yan Izalar siyasa da niyyarsu a karkashe ’yan Tijjaniyya da sauran Musulmi su kafa gwamnatin da za su kira Gwamnatin Sunnah a Najeriya. Wadannan komai za su iya su ne sharrin Najeriya, lalle ne Shugaban kasa ya sa ido ya ga cewa wadannan kashe- kashe an daina in dai har yana so Najeriya ta zauna lafiya.
Kwanakin baya an buga hotunanka da Shugaban kasa kun sha ruwa, ko ya yi maka maganar sulhu da ’yan Boko Haram?
A gaskiya ba mu yi wata magana da shi ba, an gayyace mu shan ruwa da wasu malamai, ya sha nemana fiye da sau goma ban je ba sai wannan karo. Lokacin Obasanjo ma na taba amsa irin wannan gayyata sau daya da ya yi min ta hannun marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero, amma da muka je watakila Shugaban kasa ya san abin da ya faru har wancan maganar sulhun ta lalace, don haka bai min maganar ba, an dai sa na yi addu’a a wurin, daga nan suka yi ta magana da Ingilishi ni kuma ba na ji.
A yanzu mene ne matsayin wannan sulhu?
Na fada maka ba wata maganar sulhu duk ta lalace, saboda wadansu mutane da suke cikin gwamnati ba sa goyon bayan abin, kuma suna da karfi, maganar ta lalace ba wanda ya san inda take bakiddaya yanzu. Zan yi amfani da wannan dama in sanar da ’yan Najeriya cewa mu ’yan Tijjaniyya ba mu da abokin gaba, kullum rokonmu ’yan Najeriya su zauna lafiya da juna. Kuma muna rokon al’ummar Musulmi mu yi ta addua Allah Ya ba mu lafiya da zama lafiya, Ya kawo karshen tashe-tashen hankula da kashe-kashe a Najeriya. Masu neman mu da sharri Allah Ya mayar musu da sharrinsu kansu. Allah Ya saukar da alheri da zama lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya.