‘Yadda muka yi fama da cutar shan-inna’

A ranar Talata Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta tabbatar da cewa da nahiyar Afirka ta fatattaki cutar Shan-inna. Hakan na zuwa ne bayan shafe kimanin shekara hudu rabon da a samu wanda ya sake kamuwa da cutar a Najeriya, wacce ita ce kasa ta karshe da aka samu mai cutar a fadin naihiyar a […]

‘Yadda muka yi fama da cutar shan-inna’

Wasu masu fama da cutar Shan-inna

A ranar Talata Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta tabbatar da cewa da nahiyar Afirka ta fatattaki cutar Shan-inna.

Hakan na zuwa ne bayan shafe kimanin shekara hudu rabon da a samu wanda ya sake kamuwa da cutar a Najeriya, wacce ita ce kasa ta karshe da aka samu mai cutar a fadin naihiyar a 2016.

A Jihar Kano da ke Arewacin kasar, wasu wadanda suka yi fama da cutar kafin daga bisani su warke sun shaida wa Aminiya yadda suka yi fama da cutar da kuma irin farin cikin da suka yi bayan an ce musu cutar ta tafi gaba daya.

Wani matashi mai suna Yahaya Yahaya ya bayyana yadda ya yi fama da cutar kafin ya warke.

Ya ce, “Idan ka kalle ni za ka ga alamar na yi fama da wannan cutar kafin daga bisani na samu afuwa. Gaskiya mun sha wahala sosai a lokacin.

“Kana ji kana gani kamar yadda ake kiran sunan cutar da shan-inna kafafunka za su shanye, shi ke nan ka zama gurgun dole. Ka kuma san abun da hakan ya ke nufi.

“Idan ba Allah Ne Ya kiyaye ba shi ke nan kuma sai mutum ya zama nakasashshe ya bige da yin bara. Amma Alhamdulillahi yanzu da aka ce cutar ta tafi gaba daya,” inji Yahaya.

Ya kara da cewa sun bayar da duk hadin kansu wajen samun nasarar, kuma za su ci gaba da yin hakan don ganin ba a sake samun mai dauke da ita ba.

Shi ma wani wanda ya yi fama da cutar mai suna Abdullahi Idris cewa ya yi farin cikinsa a wannan ranar ba zai misaltu ba.

Ya ce kasancewar ya yi fama da kalubale iri-iri kafin Allah Ya kawo musu mafita, babban farin cikinsa shi ne an kawar da cutar daga doron kasa bayan tsawon lokaci, kamar yadda aka yi wa cutar Bakon Dauro.

To sai dai duk da haka ya yi gargadin cewa dole iyaye su ci gaba da kai ‘ya’ayansu rigakafin cututtuka masu addabar yara matukar ana so nasarar ta dore.

“Ina kira ga iyaye da su kara jajircewa wajen yi wa yaransu rigakafi domin su girma cikin koshin lafiya ba tare da wata nakasa ba kamar yadda muke da ita yanzu,” inji Malam Abdullahi.

Shi ma wani wanda ya yi fama da cutar ya ce, “Kasancewar cutar kananan yara ta fi kamawa, masu dauke da ita sukan fuskanci tsangwama, wani lokacin ma har daga iyalai da ‘yan uwa.

“Ni kaina akwai lokutan da iyayena suka dan nuna min tsangwama da bambanci a kan ‘yan uwana, amma ba yadda na iya.

“Alhamdulillah ni na ma samu na yi karatu. Wasu daga cikinmu sun zama nakasassun karfi da yaji, yanzu bara suke yi,” inji shi.