Yadda muka yi ido biyu da mutuwa -Wanda ya tsira a harin Potiskum
Al’ummar garin Potiskum sun wayi gari ranar Litinin da ta gabata cikin firgici da juyayi lokacin da wani dan kunar bakin-wake ya tada bam a cikin dandazon mutane bayan kammala jerin-gwano, watau Muzaharar lumana ta Ashura da mabiya akidar Shi’a suka gudanar a garin Potiskum ta Jihar Yobe, da ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane […]

Al’ummar garin Potiskum sun wayi gari ranar Litinin da ta gabata cikin firgici da juyayi lokacin da wani dan kunar bakin-wake ya tada bam a cikin dandazon mutane bayan kammala jerin-gwano, watau Muzaharar lumana ta Ashura da mabiya akidar Shi’a suka gudanar a garin Potiskum ta Jihar Yobe, da ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane akalla 26 tare da jikkata mutane sama da 60, akasarinsu kananan yara ne maza da mata ’yan kasa da shekara 18.
Wata majiya a garin Potiskum ta bayyana wa Aminiya cewa dan kunar bakin waken ya kai wannan harin ne da misalin karfe 11 na safiyar ranar wannan Litinin din, jim kadan da kammala muzaharar da ’yan uwa Musulmi suka yi na Ashura, kamar yadda suka saba yi a duk shekara.
A tattaunawar da Aminiya ta yi da wani da ya nemi a sakaya sunansa, da shi ma ya ji rauni a kafarsa sanadiyyar wannan harin da ya rutsa da shi, ya bayyana cewa,”har mun kammala muzaharar Ashura wadda muke gudanarwa a duk shekara a nan yankin, mun gama lami lafiya, muna kan hanyar zuwa masauki, bayan mun wuce tsohuwar kasuwa kawai sai na ji daram! kafin in ce kwabo sai na ga mutane a kwakkwance a kan titi a gabana, bayan tashin wata kara mai tsananin gaske a gabanmu, nan da nan sai mu ka ga sojoji sun zo makaranatar Fudiyya suka fara bude wuta cikin dandazon jama’a, kuma a nan ma sun kashe wadansu tare da ji wa wadansu raunuka, shin wannan wane irin rashin imani ne, kuma me hakan ke nunawa?”
Malamin wanda jini ke bulbula a kafarsa ana kokarin daure masa, ya bayyana cewa, “kuma mafi yawan wadanda wannan al’amarin ya rutsa da su yara ne kanana wadanda shekarunsu bai wuce 8 zuwa 14 ba,su ne suka fi yawa, wallahi kuma idan ka kalla dole hankalin ka ya tashi, saboda akwai wata yarinyar da tsoka-tsoka ake tattara naman jikinta, yayin da shi kuma dan kunar bakin-waken shi ma nama jikinsa ya yi kaca-kaca da har sai a kan baranda aka tsinto naman jikinsa.”
Jama’a da dama da Aminiya ta tatauna da su a garin na Potiskum sun nuna bacin ransu matuka dangane da wannan aika-aikar da kuma wannan matakin da sojoji suka dauka na bude wuta ga masu jerin-gwanon lumana.
Wani magidanci wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya ce,”gaskiya wannan mataki na bude wuta bayan tada bam din da ya zama musababbin kashe wadannan mutanen bai kamata ba sam, sannan wani abu mai daure kai shi ne, mene ne dalilin zuwan sojojin cikin dandazon talakawa wadanda ba su da ko kara a hannun su ballanatan bindiga?
Gwamnatin Jihar Yobe ta bakin mai ba gwamna shawara na musamman kan harkokin yada labarai Alhaji Abdullahi Bego ta tabbatar da faruwar lamarin, tare da bayyana alhininta, kuma ta bada umarnin a bada magani kyauta ga duk wadanda suka samu raunuka.
A ranar Talata kuma Gwamnan Jihar Yobe Ibrahim Gaidam ya je garin Potiskum din ya yi wa shugaban ’yan Shi’a na Potiskum Malam Mustapha Nasidi ta’aziyyar rasuwar jama’arsa, a cikin ayarin nasa akwai Mataimakin Gwamna Injiniya Abubakar D.Ali da Sarkin Fika Alhaji Muhammad Abali Ibn Muhammadu Idrissa. Tare da bayar da tabbacin cewa za a binciki zargin da aka wa sojoji na kashe mutane.
Ya zuwa lokacin rubuta wannan rahoton dai an ce mutanen da suka rasu sun kai 30, wadanda kuma suka samu raunuka sun kai 119.
Sojoji muke zargi da kai mana hari ba ’yan Boko Haram ba -Mustafa Potiskum
Malam Mustafa Lawan Nasidi Potiskum shi ne wakilin ’yan Shi’a magoya bayan Sheikh Zakzaky a garin Potiskum, ya tabbatar wa Aminiya a tattaunawar da ta yi da shi bayan wani dan kunar bakin wake ya tayar da bam a cikinsu cewa, “jami’an tsaro ne suke zargin sun turo wanda ya tada wannan bam din bayan sun tashi daga jerin-gwanon Ashura na lumana da ya ce sun dade suna aiwatar da irin wannan muzahara ta Ashura kuma kowace shekara sukan yi lami-lafiya ba tare da wata matsala ba, Malam Mustafa ya kara da cewa, suna da shaida, domin bayan tarwatsa bam din suna cikin tattara wadanda suka rasu da wadanda suka ji raunuka,sai ga sojoji dauke da muggan makamai sun zo har makarantar Fudiyya suka bude musu wuta suka kashe wadansu tare da ji wa wadansu munanan raunuka. Ga karin bayanin da Malam Mustafa ya yi wa Aminiya:
Aminiya: Ko gawarwaki nawa kuka tara na wadanda suka rasu?
M. Mustafa: Ya zuwa yanzu dai mun samu tattara gawarwakin ’yan uwa kusan 26 tare da wadanda suka ji raunuka daban-daban sama da 80, kuma ana kokarin kai masu raunukan asibiti.Aminiya: Ko wannan harin da aka kawo muku na da alaka da ’yan kungiyar Boko Haram, idan haka ne me ya hada ku da su, tun da akalla ya kai kamar sau uku ko hudu ana kai muku irin wannan makamancin harin?
M. Mustafa:To lallai kan an kawo irin wannan hari a kan ’yan uwa har sau hudu, amma kuma mu mun tabbatar da cewa dukkanin hare-haren da ake kai mana ba ma zargin kowa illa sojojin Najeriya, don su ne suke kai mana hari, tun na farko da na biyu da kuma harin da suka kai mini har kofar gidana da kuma na baya-bayan nan, duk su ne suke kai mana harin, don muna da cikakkun shaidu.
Aminiya: Wane irin shaidu?
M. Mustafa: Shaidu na hakika kuwa, domin kuwa muna da hotuna da suke nuna sojojin ne ke aikata mana hakan tun da ga su nan da inifom, kai hatta harin da aka kawo mana ma na ranar Litinin su suka sa aka dasa mana wannan bam kuma daga bisani suka bi mu da harbi da bindiga har suka kashe mutane kimanin 6, to ai ka ga mudalakan babu wadanda muke cewa suna kai mana wadannan hare-hare in ba sojojin gwamnatin kasar nan ba. Don haka mu ba ’yan kungiyar Boko Haram ne ke kai mana hare-hare ba, a’a sojojin Najeriya ne ke kai mana hare-haren kisan gilla.
Aminiya: To ko wane irin kira kuke da shi ga gwamnatin Najeriya dangane da wannan lamari?
M. Mustafa: Ai mu babu wani kira ko roko da za mu yi ga gwamnatin kasar nan kan wannan lamari, tun da ’ya’yanta ne suke kai mana wadannan hare-haren, kuma ma dama ai tsohon gwamnan Adamawa Murtala Nyako ma ya fada a baya kan cewar PDP ne Boko Haram, haka nan shi ma marigayi Azazi ya fadi haka, don haka gwamnati ita take dukkanin wadannan hare-hare. Don haka ba mu zargin kowa da kai wannan hari in ba gwamnati ba, don muna da shaidu tuli, don da gwamnan jahar Yobe Alhaji Ibrahim Gaidam ya zo mana jaje ma mun nuna masa wadannan shaidu namu.