Yadda mukarraban Gwamnan Bauchi 3 suka ajiye mukamansu cikin wata 8
Cikin wata takwas da hawa mulkin Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Mohammed mutum uku daga cikin na hannun damansa wadanda ke rike da mukaman siyasa suka ajiye aiki da gwamnatin ba tare da sun bayyana wa al’ummar jihar dalilin da suka dauki wannan mataki ba. Wadanda suka ajiye mukaman nasu sun hada da tsohon […]
Cikin wata takwas da hawa mulkin Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Mohammed mutum uku daga cikin na hannun damansa wadanda ke rike da mukaman siyasa suka ajiye aiki da gwamnatin ba tare da sun bayyana wa al’ummar jihar dalilin da suka dauki wannan mataki ba.
Wadanda suka ajiye mukaman nasu sun hada da tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Bauchi, wanda aka nada shi a Mai ba Gwamna Shawara ta Fuskar Siyasa, Alhaji Shitu Musa Zaki, wanda ya ajiye aikin wata biyu bayan nada shi. Sai kuma tsohon Kwamishinan Kudi na Jihar, Alhaji Nura Manu Soro, wanda ya ajiye aiki kwana 35 bayan rantasar da shi. Mutum na uku da ya ajiye aiki a baya-bayan nan, shi ne Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Jihar, Alhaji Abubakar Ahmadu Kari.
Dukkan su ukun sun ki fadin dalili ko dalilan da suka ajiye mukamansu, kamar yadda ita ma gwamnatin jihar ta ki bayyana wani dalili dangane da al’amarin. Haka Jam’iyyar PDP, da ke rike da jihar, ba wani abu da ta fada game da dalilin ajiye aikin da ’ya’yan nata suka yi. Al’amarin da ke jawo jita-jita da cece-kuce a tsakanin al’ummar jihar.
Duk kokarin da wakilinmu ya yi don jin ta bakin Alhaji Abubakar Kari ta tarho bai yi nasara ba, saboda wayarsa a kashe take. Kuma ya aika masa sakon waya amma har zuwa lokacin hada wannan rahoto ba a bude wayar ba balle sakon ya shiga.
Ajiye aikin na Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Jihar ya cusa tsoro a zukatan masu rike da mukaman siyasa kuma ya jawo cece-kuce a tsakanin al’ummar jihar, musamman jami’an gwamnati da kuma ’yan siyasa.
Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa wadansu na ganin abokan adawar siyasarsa ne suka shiga tsakanin Gwamnan da mukarrabansa ciki har da Kari kuma hakan ya sa suka ajiye aiki. Sai dai wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta ce, Abubakar Kari ya ajiye aiki ne saboda wani sabani da ake zargin ya shiga tsakaninsa da Gwamnan tun farkon kafuwar gwamnatin, kafin a dinke barakar da ta taso kan shugabancin Majalisar Dokokin Jihar.
Majiyar ta ce tun wancan lokacin ake ta rade-radin za a kori Kari daga mukaminsa , inda majiyar ta ce Gwamnan ya yi masa fada sosai a bainar jama’a, lamarin da ya sa ya yi fushi, ya yi tafiya na tsawon lokaci kafin ya dawo.
An ruwaito cewa lokacin da Gwamna Bala Mohammed ya samu nasara a Kotun Koli, ya yi barazanar sa kafar wando daya da dukkan wadanda suke yi masa zagon kasa a mulkinsa. Kodayake Gwamnan ya ce bai san wadanda ke yi masa zagon kasar ba, amma ya yi barazanar daukar matakin ba sani ba sabo, domin tabbatar da cewa ba wanda ya yi masa zagon kasa.
Da yawa daga cikin ’yan siyasa da jami’an gidan gwamnati suna zargin cewa duk da Kari na daga cikin wadanda suka shugabanci daidaita rikicin majalisar amma an samu abin da wadansu ke gani kuskure ne wajen aiwatar da umurnin da Gwamnan ya ba shi.
Wadansu daga cikin abokan tafiyar siyasar Gwamnan da suka ce a sakaya sunansu, sun ce an samu rashin jituwa a tsakanin Gwamna da Kari, sannan rashin gaskiya da cin amana da kasa aiwatar da umurnin da Gwamnan ke bayarwa, ya ba ’yan siyasa da wadanda ba su son Kari dama suka yi ta suka har ta shiga kunnuwan Gwamna ya amince da su, ya nemi ya ajiye aiki.
Masu goyon Alhaji Abubakar Kari da Aminiya ta zanta da su da suka nemi a sakaya sunansu, sun ce Kari ya ajiye aikin ne kawai don ra’ayin kansa, kamar yadda ita kanta gwamnatin ta tabbatar.
Jam’iyyar PDP a jihar ta bakin Kakakinta, Alhaji Yayanuwa Zainabari ya ce “Kowane mutum da jam’iyya ta bayar aka ba shi mukami yana iya ajiye aiki a duk lokacin da ya so. Wani sai in zai yi takara yake ajiye aiki, wani kuwa haka kawai zai ji abin ya ishe shi saboda haka dukkan mutanen da suka ajiye aiki, sun ajiye ne bisa radin kansu. A gwamnatance ba mu samu wani dalili da ya sa suka ajiye ba, su kuma ba su kawo mana dalilinsu na bari ba saboda haka mun dauka sun bi ’yancin da suke da shi ne na barin aiki a duk lokacin da suka ga dama.