Yadda muke gudanar da kasuwanci a Saudiyya- ’Yan Najeriya
Wadansu mata ’yan asalin Najeriya da ke gudanar da kasuwanci da kuma kananan sana’o’i a birnin Makka da ke kasar Saudiyya sun ce suna fuskantar tsangwama daga hukumomi daban-daban na kasar, amma duk da haka ba sa sha’awar dawo wa Najeriya sakamakon yadda Saudiyya ke kula da al’ummarta, akasin haka a Najeriya.Matan wadanda wakilin Aminiya […]

Wadansu mata ’yan asalin Najeriya da ke gudanar da kasuwanci da kuma kananan sana’o’i a birnin Makka da ke kasar Saudiyya sun ce suna fuskantar tsangwama daga hukumomi daban-daban na kasar, amma duk da haka ba sa sha’awar dawo wa Najeriya sakamakon yadda Saudiyya ke kula da al’ummarta, akasin haka a Najeriya.
Matan wadanda wakilin Aminiya ya gana da su a wata karamar kasuwa da ke gefen titi a kusa da Masallacin bin Laden a kan Titin Ummul kura a cikin Birnin Makka, sun ce suna gudanar da kasuwancinsu ne a cikin halin rashin kwanciyar hankali a sakamakon kama su da jami’an tsaro ke yi a kullum, inda ake sake su a kan beli, baya ga gidajensu da dama da aka rushe a unguwar, wanda a baya ta kasance babbar matattarar al’ummar Hausawa a Birnin Makka.
Wata mata mai suna Maryam Ibrahim da ta fito daga Garin Birnin Kudu a Jihar Jigawa, ta ce, adalcin da suke samu daga gwamnatin kasar inda ’ya’yansu ke halartar makarantu daya da sauran al’umma da kuma ciyar da marasa galihu kyauta ya sanya suka gwammace ci gaba da zama a Saudiyya, kasancewar ba a samun haka a kasarsu, wanda a yanzu kuma ga kuma matsalar rashin tsaro a wasu sassan Najeriya.
Ta ce “Suna sayar da sutura, inda ta rabu kashi biyu, akwai wanda ake kira jadid (sabo), sai kuma wanda ake kira Gumama, wanda na hannu ne da muke samu daga gidajen da muke yi wa ayyuka.”
Sun ce kayayakin da suke sayarwar suna tattalin tarawa a tsawon shekara guda, suna samun damar sayar da shi ne a lokacin da mahajjata suka cika unguwannin birnin Makka, inda suke baza hajarsu a kusa da masaukansu har zuwa lokacin da mahajjatan suka kammala aikin hajji, ko kuma a lokacin da suka je gida Najeriya ziyara.
Wani dan asalin garin Tsafe a Jihar Zamfara mai suna Muhammadu Auwal da ya kasance namiji guda a kasuwar tare da matan, ya ce dumbin ’yan Najeriya da dama sun bar kasar a ’yan shekarun nan, a sakamakon rashin cikakkun takardu izinin zama a kasar.
Da Aminiya ta nemi jin ta bakin wani Balarabe dan asalin Saudiyya a kan ko ya zai bayyana yanayin makwabtan nasa, Yahya Hassan Ali cewa ya yi: “Yan Najeriya na da kazar-kazar wajen neman abin hannu, sannan ga kula da addini, muna jin dadin zama da su.”