‘Yadda muke gudanar da kasuwancin tumatir a Jos’
Kasuwar ’yan tumatur da ke Farar Gada a garin Jos a Jihar Filato, kasuwa ce da ta yi suna a jihar da jihohin da ke makwabtaka da jihar da kuma sauran sassan kudancin kasar nan. Ta shahara wajen gudanar da hada-hadar harkokin kasuwancin sayar da tumatur. Ita dai wannan kasuwa wadda aka kafa shekara 30 […]

Kasuwar ’yan tumatur da ke Farar Gada a garin Jos a Jihar Filato, kasuwa ce da ta yi suna a jihar da jihohin da ke makwabtaka da jihar da kuma sauran sassan kudancin kasar nan.
Ta shahara wajen gudanar da hada-hadar harkokin kasuwancin sayar da tumatur. Ita dai wannan kasuwa wadda aka kafa shekara 30 da ta gabata, tana ci ne a ranakun Litinin da Laraba da Alhamis da kuma Asabar.
Sai dai duk da haka kasuwar tana fama da matsalolin rashin kyawawan hanyoyi da magudanr ruwa da wutar lantarki da kuma ruwan sha.
Shugaban kasuwar Malam Aminu Yahaya Yunusa ya ce akalla mutane sama da dubu 20 wadanda suka kunshi kabilu daban-daban da mabiya addinai daban-daban da suke gudanar da harkokin kasuwancinsu a wannan kasuwa.
Ya ce duk da yawan mutanen da suke gudanar da harkokin kasuwancinsu a wannan kasuwa, “muna zaune lafiya da junanmu. Domin duk da rikice rikicen da aka samu a garin Jos ba mu taba samun wata sabani a wannan kasuwa.”
Malam Aminu ya yi bayanin cewa “muna samun kayayyakin tumatur daga kananan hukumomin Jos ta Gabas da Jos ta Kudu da Bassa da suke jihar nan da kuma yankin Toro da ke Jihar Bauchi da yankin Saminaka da ke Jihar Kaduna.
Ya ce suna samun masu zuwa suna sayen tumaturi daga kudancin kasar nan, kamar daga garuruwan Enugu da Fatakwal da Onaca da dai sauransu.
Ya ce ganin irin halin da suke ciki a kasar nan, suna da kyakkyawan tsaro a wannan kasuwa, domin akwai sojoji da ’yan sandan kwantar da tarzoma da kuma ’yan banga, kuma suna ba wadannan jami’an tsaro goyon baya da hadin kai.
Ya ce “A dukkan kasuwannin da suke karamar Hukumar Jos ta Arewa babu kasuwar da take samar da kudin shiga kamar wannan kasuwa ta ’yan tumatur.”
Ya ce “Amma duk da haka ba mu da kyawawan hanyoyi da magudanar ruwa. Ba mu da ruwan sha; babu wutar lantarki. Don haka muna rokon gwamnati ta taimaka mana da wadannan abubuwa da muke bukata a wannan kasuwa.”
Daga nan ya bukaci ’yan kasuwar su ci gaba da ba su goyan baya da hadin kai don ci gaban kasuwar.