“Yadda muke rayuwa a daular da ’yan Boko Haram suka ayyana’’

Tun bayan kwace yankunan kananan hukumomin Gwoza da Gamboru Ngala da ke Jihar Borno da kungiyar Boko Haram ta ayyana a makon jiya, inda shugabanta Abubakar Shekau ya ce garuruwan sun koma karkashin daula ta Musulunci kuma a  karkashin ikonsa, sauran mutanen da ke zaune a wadannan garuruwan a yanzu haka suna zaune a cikin  […]

“Yadda muke rayuwa a daular da ’yan Boko Haram suka ayyana’’
“Yadda muke rayuwa a daular da ’yan Boko Haram suka ayyana’’

Tun bayan kwace yankunan kananan hukumomin Gwoza da Gamboru Ngala da ke Jihar Borno da kungiyar Boko Haram ta ayyana a makon jiya, inda shugabanta Abubakar Shekau ya ce garuruwan sun koma karkashin daula ta Musulunci kuma a  karkashin ikonsa, sauran mutanen da ke zaune a wadannan garuruwan a yanzu haka suna zaune a cikin  zullumi da fargaba.
Wadannan mutanen dai sun kasance a cikin garurruwan ne saboda sun kasa gudu, kamar yadda akasarin al’ummomin yankunan suka yi.
Duk da cewa babu sauran maza matasa ko magidanta a garin Gwoza bayan aiwatar da wannan harin, amma akwai matan aure da kananan yara, musamman ma ’yan mata da rahotanni ke nuna cewa suna fuskantar musgunawa, a yayin da matan aure suka gaji da bizne gawarwakin mazajen garin da aka kashe, inda  kuma a yanzu haka rayuwarsu ke cikin wani matsanancin hali.
Wata mata mai suna Malama Fatima Ali ta shaida wa wakilinmu ta waya cewa, “Mu mata  a yanzu haka  a Gwoza muna fuskantar wani mawuyacin hali da sabuwar rayuwar da ba mu taba tunanin za mu iya tsintar kanmu a ciki ba. A yanzu haka muna cikin zaman zullumi da damuwa, domin kuwa baya ga juyayin rasa mazajenmu da ’ya’yayenmu da sauran ’yan uwa, muna kuma fargabar cewa wadannan ’yan bindiga suna iya shiga mana gidaje a kowane lokaci su ce wai za su tara da mu ko da ’ya’yanmu mata, domin suna yin haka a kowane lokaci kuma a kowace unguwa. Sannan kuma mafi akasarin abincin da muke da shi a yanzu haka ya kare, musamman ganin cewa shi ma sukan shigo su nemi abinci a wajenmu. Ga shi kuma babu kasuwanni, babu shaguna, balle mu fita mu je mu saya. Ruwan sha ma da kyar muke samu, domin kuwa kafin mu je mu diba har wadancan ’yan bindigar sun riga mu zuwa su diba, domin sun kafa shingayensu ne a ko’ina, kamar yadda soja suka yi a baya.
“Kuma sun kwace wadansu gidaje, sai abin da suka yi a garin, babu wanda ya isa ya tsawata musu. Amma a wadansu lokutan sukan fada mana cewa wai mu kwantar da hankalinmu ba za su yi mana komai ba. Amma a gaskiya suna musguna mana ta kowace fuska, baya ga zaman alhini da bakin cikin rasa mutanenmu, ga zaman zullumin zama tare da su. Kuma mu a yanzu haka ba mu ga wata shari’ar Musuluncin da suke aiwatarwa ba, mun gaji da zama a karkashinsu, ai gara zamanmu da sojoji.”
A garin Gamboru Ngala kuwa, wani mazaunin gari mai suna Mukhtar Aliyu Modu ya shaida wa wakilinmu cewa, “Mu a yanzu haka a garin Gamboru muna cikin zaman zullumi ne, domin kuwa  baya ga kauracewar da iyaye da ’yan uwanmu suka yi, wanda a yanzu haka ba mu san halin da suke ciki ba, mu kuma muna zaman zullumi da fargaba ne, na cewar watakila wadannan ’yan bindigan za su iya shigowa gidajenmu su kashe mu, ba zato, ba tsammani. Ga shi suna kewayawa kowace unguwa kuma suna kiranmu mu zo mu ji wa’azinsu. Saboda haka muna cikin fargaba, ga shi kuma abincinmu  ya kare, ga babu kudi, babu kasuwanni a bude, domin tun ranar da abin ya faru masu shaguna suka gudu.
“Idan ba ka manta ba, watanni hudu da suka wuce sun kawo mana hari, suka kuma yi mana ta’adi a garin namu, to ya zuwa wannan lokacin ba mu gama farfadowa ba, kuma kwatsam sai ga wannan. Saboda haka a yanzu haka muna cikin wani mawuyacin hali, domin kuwa mu wadanda muka rage a garin ba mu da sana’a kuma ba mu da aikin yi, kuma ko muna da shi ai ba wani wanda zai shigo daga wani wuri ya sayi abin da muke da shi ko ya ba mu abinci, su kuma wadannan ba ba mu suke yi ba. Mu dai kawai muna nan ba mu san yadda halin da rayuwarmu za ta kasance ba.’’
Shi ma Malam Kime, wani magidanci ne a garin Gamboru, ya bayyana wa Aminiya cewa, “Mu dai ba mu ga wani tsarin Musulunci a tattare da wadannan mutanen ba, domin kuwa suna sanya mutane cikin fargaba, su ma kuma ba su da natsuwa, sannan kuma a yanzu haka muna cikin matsananciyar bukatar abincin da za mu ci ne da kuma wuraren da za mu kwana, domin duk sun kwace mana gidaje, ba mu da matsuguni, ba mu da abinci, kuma ba mu da aikin yi, ga shi muna zaman zullumin abin da zai iya faruwa da mu, wato za su iya kashe mu a kowane lokaci. Domin ka san babu jami’an tsaro, ga shi kuma iyalanmu wadansu sun gudu, wadansu kuma suna nan, amma cikin wahala.
“Kuma wani abin fargaban shi ne muna jin tsoron kada su rinjayi matasanmu su yarda  da irin akidarsu na kashe mutane. Duk da cewa a yanzu ba su kashe mu ba, amma ai a baya sun kashe mutanenmu, to mu dai a yanzu haka muna neman taimakon gwamnati da ta zo ta agaza mana ta kori wadannan mutane.’’
Shi kuma wani magidancin da bai amince a bayyana sunansa ba, cewa ya yi, “Ni dai ba na cikin hayyacina a yanzu haka, domin iyalina da ’ya’yana duk sun tsere, ban kuma san halin da suke ciki ba, ga shi mu ma muna cikin rashin tabbas game da rayuwarmu, domin za su iya kashe mu a kowane lokaci. Sannan kuma ba mu da aikin yi, babu abinci, ba kwanciyar hankali, ba kasuwanci, kuma ba mu ga wadansu alamu na gudanar da shari’ar Musulunci a wajensu ba. Kai ai wahala suka kawo mana ba Musulunci ba. Idan haka ne ai gwamnati ta bar kowa ya gudanar da addininsa babu tsangwama, kuma ba ta tursasa mana a kan abin da muke nema mu ci, a saboda haka mun fi bukatar zama da gwamnati a bisa wadannan, domin su ba hukumomi ba ne.”
A wata hira da sashin Hausa na gidan rediyon BBC ya yi da wani mazaunin garin Gomburo-Ngala ta waya ya ce, suna cikin mawuyacin hali tun bayan da ’yan Boko Haram suka kwace iko da garinsu, wanda a yanzu da kyar suke ci, suke sha.
Ya ce, “Da farko ’yan Boko Haram ba sa taba ’yan gari, daga baya suka je neman wani malamai ba su same shi ba, sannan suka samu wani suka yanka shi, yanzu haka muna cikin halin wahala, ci da sha ma da kyar muke yi. Ba hanyar shiga ko fita.”
Ya ce mutane suna fita jam’i a masallatai, sai dai ’yan Boko Haram suna sallarsu daban ne, kuma ba su tara jama’a don yi musu wa’azi ba.
Ya ce ba a bude kasuwanni ba, idan ka samu shago a bude ma, za ka samu a kulle yake ta ciki saboda tsoro. Ana ciniki ne cikin tsoro.
“Daga farko jama’a suna fita, amma yanzu da suka fara taba mutane jama’a suna cikin gida saboda tsoro. Da yawa mutane sun gudu, amma mu muna cikin gari. Idan mun leka mukan gan su a kan babura da kekuna, wadansu kuma a kafa dukkansu rike da bindigogi.” Inji shi.
Ya ce a yanzu babu jami’an tsaro a garin, sun rushe duk wani wuri na jami’an tsaro.
A Jihar Yobe kuma ’yan Boko Haram sun mamaye kananan hukumomin Gujba da Gulani, inda suka mayar da manyan garuruwan Buni Yadi da Goniri da Buni gari da Gujba da dai sauransu karkashin ikonsu. Sai kuma hedkwatar Gulani, watau Bara da Bularafa, da dai sauran kauyuka.
Garin Buni Yadi, watau inda suka kafa tuta, shi ne hedkwatar karamar Hukumar Gujba da ke da nisan akalla kilomita 60 daga cikin garin Damaturu. Jami’an tsaro sun kaurace wa yankin zuwa wani gari da ake ce wa Katarko, mai nisan kilomita 21 daga garin Damaturu, amma duk da haka ’yan  Boko Haram din ba su bar su ba. A ranar 30 ga watan Yuli da ta gabata, sun kara kai wa sojojin farmaki a sansaninsu na Katarkon, inda suka fatattake su, suka kashe mutane shida tare da awon gaba da wani malami da matarsa da wasu mutum biyu, sa’annan suka karya babbar gadar da ta hada kudancin Yoben da sauran sassan jihar. Wannan al’amari ya sanya mutanen yankin hijira, sakamakon haddi da ’yan kungiyar suka cigaba da yanke wa al’ummar yankin da suka hada da kisa da bulala da kona gidaje da wuraren kasuwanci da karbar kudade a hannun masu hannu da shuni.
Malam Baaka, wani mazauni garin ne da ya yi hijira zuwa Damaturu, ya bayyana wa Aminiya cewa ban da tsofaffi da fakirai babu wanda ya yi saura a garin.
Ya ce, “Ina mai tabbatar maka cewar duk wani wanda yake da dan uwa a wani gari sabanin kudancin Yobe ya bar garin nan, haka nan masu hannu da shuni da masu karamin karfi duk sun fice zuwa Gombe da Biu da Damaturu da Maiduguri da sauran kauyukan da ke zagaye da mu.  
“To, yara ne, sun hana duk wani mai sana’a sakewa, manomi ba ya da damar zuwa gona, haka nan ma’aikacin gwamnati bai isa ya fito aiki ba, idan ma suka fahimci kai ma’aikaci ne to ka shiga uku.”