Yadda muke rayuwa bayan mutuwar mazajenmu —Matan sojoji

Matan tsofaffin sojoji da waɗanda mazajensu suka rasu yayin bauta wa ƙasa sun koka kan yadda gwamnati ta yi watsi da su, musamman a wannan lokaci da tsadar rayuwa ta ƙara tsanani.

Yadda muke rayuwa bayan mutuwar mazajenmu —Matan sojoji

Matan tsofaffin sojoji da waɗanda mazajensu suka rasu yayin bauta wa ƙasa sun koka kan yadda gwamnati ta yi watsi da su, musamman a wannan lokaci da tsadar rayuwa ta ƙara tsanani.

Sun bayyana cewa ko da mazajen nasu suna raye, rayuwarsu ba ta da sauƙi, balle yanzu da komai ya yi tsauri.

Malama Solomi Titus Ishaya, shugabar ƙungiyar matan tsofaffin sojoji a Jihar Gombe, ta bayyana cewa rayuwarsu ta kasance hannun-baka, hannu-kwarya saboda ba su da wata dama ko taimako daga gwamnati.

A wata hira da ta yi da wakilinmu bayan kammala bikin Ranar Tunawa da Mazan Jiya na shekarar 2025, Malama Solomi ta ce Gwamnatin Tarayya da ta jiha sun yi watsi da su, ba tare da wani tallafi na koyon sana’o’i ko taimako ba.

“Tun lokacin da mazajenmu suka mutu, muka rasa madogara. Ba ma samun tallafi na koyon sana’o’i kamar gyaran gashi, kiwon kifi ko ɗinki da ake bayarwa ga wasu matan.

“Wannan rana, a garemu, rana ce ta baƙin ciki da jimami. Amma duk da haka, muna gode wa Allah domin mazajenmu sun mutu ne wajen bauta wa ƙasarsu,” in ji ta.

Malama Solomi ta bayyana cewa ƙalubalen rayuwarsu ya ƙara yawa, musamman wajen biyan kuɗin makarantan ’ya’yansu, ciyarwa, da sauran buƙatun yau da kullum.

Ta ce idan har yaran nasu sun kammala makaranta, amma samun aikin yi na zama ƙalubale saboda rashin wani gata.

A cewarta, rayuwar zaman kaɗaici ta fi zama tsanani domin kaɗan ne daga cikinsu suke iya dogaro da kansu. Ta kuma koka kan yadda wasu mutane ke yawan zargin waɗanda ke zaman kaɗaici da cewa suna neman maza, wanda ya ƙara zama damuwa a rayuwarsu.

Ta yi kira ga gwamnati da masu hannu da shuni su kawo musu tallafi ta hanyar samar da kayan koyon sana’o’i da sauran nau’o’in taimako domin rage musu wahalar rayuwa.

Ta bayyana cewa, a tsawon shekaru uku da ta yi tana shugabancin ƙungiyar, ba su taɓa samun wani tallafi ba, ko da kuwa na ƙananan abubuwa ne.

Malama Solomi ta ce, a halin yanzu, mambobin ƙungiyar da ke da rajista a Ƙaramar Hukumar Gombe su 104 ne, amma a faɗin jiha ba su gama tantance yawansu gaba ɗaya ba.

Ta ba da shawarar cewa ya dace a ware wata rana musamman domin matan tsofaffin sojoji, inda za a ba su tallafi ko koya musu sana’o’i ba tare da haɗa su da sauran matan aure ba. Hakan a cewarta, zai ba su ƙwarin gwiwa kuma ya taimaka wajen inganta rayuwarsu.