Yadda muke rayuwa cikin aminci a Arewa — Ibo

Wani dan kabilar Ibo mai suna Ogochukwu ya sauya sunansa zuwa Ciroma.

Yadda muke rayuwa cikin aminci a Arewa — Ibo

Nen da Ike da suka ce su ma ’yan Kano ne saboda a nan aka haife su

A yayin da jihohin Ibo da ke Kudu maso Gabas suke fama da hare-haren ’yan bindiga da ake alakanta su da matasan yankin masu fafutikar kafa kasar Biyafara a karkashin Kungiyar IPOB,  a nan Arewa ’yan kabilar Ibo da dama sun ce, suna zaune cikin amincin da ko an raba kasar nan ba za su koma Kudu ba.

Aminiya ta ruwaito yadda rikicin Kudu maso Gabas yake rikidewa zuwa irin na Boko Haram, inda matasan suke kai hari kan ofisoshin ’yan sanda da su kansu ’yan sandan da sauran jami’an tsaro  da sauran ofisoshin gwamnati suna konewa da kashewa.

Sannan a lokuta da dama sukan tare hanya su kwace kayayyakin Hausawa a wasu lokutan ma su kashe su.

Hakan ya sa Aminiya ta zagaya domin jin yadda ’yan kabilar Ibo mazauna Arewa suke rayuwa da gudanar da harkokinsu.

‘Ba na son komawa Kudu da zama’

Nonso Ekekwe Ibo ne mai kimanin shekara 45 wanda ya shafe sama da shekara 30 yana zaune a Jihar Kano yana gudanar da kasuwancinsa a Kasuwar Sabon Gari.

Ya shaida wa Aminiya cewa yana zaune cikin aminci da amana wanda hakan ya sa ba ya ma son ya koma garinsu na asali saboda sabon da ya yi da zaman Arewa.

Ya ce “Duk da cewa da wayona na zo Kano, amma a yanzu babu abin da zai mayar da ni gida Kudu.

“Na fi jin dadin zama a nan don ina gudanar da kasuwancina cikin kwanciyar hankali.

“Ina da abokai Hausawa masu yawa da muke gudanar da abubuwa tare. Nakan je har gidajensu idan suna wani sha’ani.

“Kai ta kai a yanzu su ma idan wani abu ya taso min a gida musamman biki ko mutuwa sukan yi min kara su je har can kauyenmu a Jihar Anambra.”

A cewarsa yanzu haka yana zaune da matarsa wacce ita ma a Jihar Kano ya aure ta da ’ya’yansu uku wadanda suke karatu a yanzu.

‘Na riga na zama dan Kano’

“Ni fa a yanzu ina jin na zama cikakken dan Kano don a nan na yi aure kuma nake zaune da iyalina da ’ya’yana wadanda kuma a yanzu haka suke karatu tare da ’ya’yan Hausawa da muke tare da su.

“Babu wani abu da ke damunsu. Su kansu suna jin dadin rayuwarsu domin a nan suka taso. kuma ba na jin za su iya rayuwa a wani wuri ba Kano ba.

“Domin ko tafiya muka yi da su sun rika damuna a dawo gida,” inji Nonso.

‘Ba ni da gidan da ya wuce Arewa’

Maman Esther wacce ita ke da Kamfanin Wutar Sola na Zeek Solar a Kasuwar Sabon Gari da ke Kano wacce kuma take magana da Harshen Hausa sosai, ta ce ta shafe kimanin shekera 40 a Jihar Kano don haka tana daukar Arewa a matsayin gida.

Ta ce, “A yanzu ba ni da wurin zama kamar Arewa don a nan na yi aure na zauna da mijina na haifi ’ya’yana wadanda a yanzu yawancinsu sun gama karatu sun yi aure.

“Kai duk da mijina ya rasu amma ina ci gaba da zama a Kano tare da gudanar da harkokin kasuwancina. To ki gaya min ina zan je. Ai ni Arewa ta zama gida a wurina.”

A cewarta, Arewa ta fiye mata Kudu inda ta fito domin ta hadu da mutanen da a yanzu take ganin sun fi ’yan uwanta kusanci da ita.

“A yanzu haka akwai Hausawan da muke tare da su wadanda kuma muka zama kamar ’yan uwa.

“Wallahi akwai daga ciki wadanda nake gaya musu sirirna da ba zan gaya wa ’yan uwana ba.”

‘Idan na koma Kudu me zan yi?’

Shi ma wani dan kasuwa mai suna Hyginius Offor, ya ce ya shafe shekara 30 a Kano don haka ba ya da wurin zama da ya fi Jihar Kano.

 Ya ce, “Yanzu idan na koma Kudu me zan yi? A nan komai nawa yake.

“Kin gan ni bai fi sau biyu ko uku ba nake zuwa kauyenmu a shekara. Ina zuwa lokacin Kirsimeti sai bikin Ista sai kuma idan wani abu ya taso.

“Kuma har ga Allah na fi jin dadin zama a nan Arewa fiye da Kudu domin na tabbatar mutanen Arewa suna son baki suna da juriyar zama da mutane ba su da kyama da sauran miyagun halaye.

“An ce ba ka sanin mutum sai ka zauna da shi. To ni a yanzu ko ’ya’yana ba na yi musu fatar su koma garinmu.

“Domin ba su san komai na can ba. Da nan suka saba tun daga kan dabi’unsu da yanayin kasa da sauransu.”

‘Ko an raba Najeriya a nan za mu zauna’

Wadansu matasa su biyu da suke kula da shagon mahaifinsu a Kasuwar Sabon Gari, masu suna Nen da Ike wadanda kuma suka ce duk a Kano aka haife su, sun shaida wa Aminiya cewa a halin yanzu ba za su iya zama a kowane gari idan ba Kano ba.

Sun ce “Duk da cewa asalinmu ’yan Jihar Anambra ne, amma zan iya cewa mun fi shekara 10 ba mu je kauyenmu ba kuma idan ma ya kama iyayenmu ne kadai suke zuwa.

“A nan aka haife mu a nan muka yi wayo. A nan muka yi karatu har ga shi mun shiga harkar kasuwanci.

“To ina za mu je? Ai mu ko raba kasar aka yi, a nan za mu ci gaba da zama don nan ce mahaifarmu babu inda za mu je.”

‘Ba ma jin dadin rikicin da ke faruwa a Kudu’

Dukkan ’yan kabilar Ibon da Aminiya ta tattauna da su sun nuna takaicinsu game da abubuwan da suke faruwa a Kudu, inda matasan Kungiyar IPOB mai fafutikar kafa kasar Biyafara suke kashe-kashe.

Sun bayyana su da mutane masu neman fitina da neman kudi.

“Ai mun san duk abin da suke yi ba gaskiya ba ne, domin kuwa suna yi ne don neman kudi.

“Idan suka ci gaba da yin barna sai gwamnati ta kira su ta ba su kudi don su daina, sannan bayan kwana biyu su sake dawowa wannan ba daidai ba ne.

Muna ta addu’ar a samu zaman lafiya a kasar nan daga ’yan Boko Haram da masu garkuwa da mutane da kuma wadanda ke tayar da kayar baya a Zamfara sai kuma mu ji wadansu sun fito neman kafa wata kasa?

“Ya kamata gwamanti ta yi da gaske wajen ganin ta hana su kai hare-haren da suke yi,” inji su.

‘Hausawa ba sa daukar fansa’

“Mu da muke zaune a Arewa duk da cewa a Arewar ma akwai matsalar tsaro amma muna cikin zaman lafiya tunda dai babu wani rikici na kabilanci ko na addini a tsakaninmu da mutanen da muke zaune da su.

“Kowa ya san cewa Kano tana cikin zaman lafiya domin kowa ya san yadda Kano take a baya a duk lokacin da ake rikici irin wannan, amma yanzu mun gode wa Allah Hausawa sun fahimci cewa yaki ba abin yi ba ne, domin a kan talaka abin yake karewa shi ya sa yanzu duk rigimar da za a yi ba za ka ga Bahaushe ya shiga ciki ba.

“To haka muke fata su ma matasan Kudu su fahimci gaskiya cewa babu komai a cikin yaki sai wahala da rashin kwancinyar hankali.

“Muna addu’ar Allah Ya kawo mana karshen lamarin,” inji su.

‘Ogochukwu ya koma Ciroma’

Aminiya ta samu labarin cewa wani matashi dan kabilar Ibo mai suna Ogochukwu ya sauya sunansa zuwa Ciroma domin jin dadin zama da Hausawa da yake yi.