Yadda muke yaki da talauci a Jihar Bauchi

Barrista Ahmed Umar Faruk shi ne Shugaban Hukumar Bunkasa Harkokin Matasa da Mata ta Jihar Bauchi, a tattaunawarsa da Aminiya ya yi karin haske kan hadin gwiwar gwamnatin jihar take yi da Bankin Duniya, inda suka bullo da wani shiri na tallafa wa mata da matasa mafiya talauci da yadda shirin ke gudana:   Mene […]

Yadda muke yaki da talauci a Jihar Bauchi

Barrista Ahmed Umar Faruk shi ne Shugaban Hukumar Bunkasa Harkokin Matasa da Mata ta Jihar Bauchi, a tattaunawarsa da Aminiya ya yi karin haske kan hadin gwiwar gwamnatin jihar take yi da Bankin Duniya, inda suka bullo da wani shiri na tallafa wa mata da matasa mafiya talauci da yadda shirin ke gudana:

 

Mene ne makasudin tara dubban mata da matasa da kuka yi a nan garin Bauchi?

Alhamdulillahi, abin da ya jawo wannan taro da ka gani wani kokari ne na Gwamnatin Jihar Bauchi a karkashin jagorancin Gwamna Mohammed Abdullahi Abubakar, na ganin an taimaka wa talakawa na can kasa zuwa sama, wato wadanda suka fi fama da talauci domin samar musu da aikin yi. Wannan shirin hadin gwiwa ne a tsakanin gwamnatin da Bankin Duniya, kuma shirin ya kai ga zakulo mata da matasa da dattawa fiye da mutum dubu 16, domin samar musu da ayyukan yi a yankunansu. Ba kawai a kananan hukumominsu ba, a yankunansu, kowace al’umma da ka sani a Jihar Bauchi an dauko daga cikinta, kuma a kowane gari da kowace unguwa da kowane yanki an zakulo mutanen ne daga cikin wadanda ake ganin sun fi fama da talauci. Kuma a yanzu haka an zakulo mahalartar ne daga kananan hukumomi 12 da suke fadin jihar nan a matsayin kashi na farko. Mutum dubu 11 ne in sun koma kuma za a sake zakulo wadansu mutanen daga sauran kananan hukumomi takwas domin a samu saukin gudanar da shirin,

Ta yaya kuka gano cewa wadannan su ne wadanda suka fi kowa talauci?

Wannan shiri hadin gwiwa ne da Bankin Duniya kuma Bankin Duniya ne ya sanya ido ya ga yadda aka zakulo wadannan mutane kamar yadda suka bayar a cikin ka’idodinsu. Yanda aka yi kuwa shi ne mun yi amfani ne da masu unguwanni da limamai da shugabannin al’umma na kowane yanki don gano fitattun gidajen da suka fi kowanne talauci domin a dauko wadannan mutane da su ne suka fito daga gidajen da suka fi talauci a unguwanninsu. Daga farko sun tara sunayen mutanen bayan an fito da sunayen mutanen da suka bayar sai aka zauna da shugabannin al’umma da na addinai da sauran masu ruwa- da-tsaki a unguwar suka zauna suka tantance kowane gida don a samu adalci da daidaito kan kowane gida. Kowane gida in an kira sunan gidan sai an daddale, in shugabannin sun duba sai su dauki wanda ya fi talauci kafin a sa shi cikin shirin. Haka suka yi ta yi a duba wannan gidaa duba wancan, wannan sun fi wancan talauci ko wancan ne ya fi, haka suka yi ta yi har aka dauki wadanda suka fi kowanne talauci sannan aka kawo sunayensu. Shi ya sa za ka ga koda wadannan mutane da suke nan ko a fuska sun fi kowa talauci.

Da yake shirin na hadin gwiwa ne da Bankin Duniya nawa za a kashe kuma nawa Bankin Duniya ya bayar kuma nawa Gwamnatin Jihar Bauchi ta bayar?

Gwamnatin Jihar Bauchi ta sanya Naira miliyan 50 domin dinka wa yaran rigunan sanyawa na bai-daya wato yunifom da samar musu da kayan aiki, kuma kowannensu ta dauki nauyin zuwansa Bauchi domin ba su horo na musamman kuma gwamnati ne ta dauki nauyin da masaukin kowannensu  da abincinsu kuma ana sa ran bayan sun gama wannan aiki na samun horo kowannensu zai koma yankinsa. Gwamnatin Jihar Bauchi ce za ta ba su kudin motar komawa gida sannan kowannensu za a rika biyansa alawus na Naira dubu bakwai da dari biyar a kowane wata na tsawon shekara biyu da rabi. Bayan shekara biyu da rabi za a sake komawa wadandan yankuna kuma a sake zakulo wadansu iyalai mafiya talaucin domin a debo wadansu da suka gaza su. Ba zan iya tuna yawan kudin da Bankin Duniya ya sa a cikin shirin ba amma yana da yawa kuma zai wadatar da shirin.

Mene ne dalilin yin wannan shiri?

Dalilin yin wannan shiri shi ne, gwamnati tana da kyakkyawan zaton cewa bayan an gama shirin ana sa ran talaucin wadanda suka ci gajiyarsa zai ragu. Saboda haka sai a koma a dauko wadansu domin su ma su dandana ta haka za a rika rage wa jama’a talauci da matsi da kuncin rayuwa da suke fama da shi. A takaice manufar shirin ita ce a tabbatar da cewa an rage talauci a fadin Jihar Bauchi, kuma wannan tsarin ya saba wa sauran tsare-tsaren da aka yi a baya. Domin babu wanda zai ce maka ni dan wani ne cikin dukan wadanda ka gani, babu wani dan babban mutum ko wani ma’aikacin gwamnati ko dan wani mai hali ko wani mai taka rawa a cikin gwamnati, illa dai shirin talakawa ne su ma na can kasa. Sannan duk unguwanni da za ka iya sani a cikin Jihar Bauchi kowace unguwa an bi wadanda suka fi kowa talauci ne aka dauko su.

Ganin cewa mutanen nan daga kauyuka suke wadansu ma ba su da ilimin zamani wani irin aiki za su yi ga alummarsu? Kuma ta yaya kuke jin za su iya cin moriyar shirin ba tare da an cuce su ba?

Alhamdulillahi kamar yanzu wadanda kuke ganin a nan mun tantance su kowa zai zo da sunansa akwai hotonsa da sa hannunsa. Zai zo a tantance shi idan an tantance shi kuma zai zo akwai kudin mota Naira 2,500 da za a bai wa kowa domin ya koma gida, amma kafin ya koma gida za a nuna musu ayyukan da za su yi, kuma aiki ne wanda ya shafi al’ummar da suka fito daga cikinta, su al’ummar ne za su fadi irin aikin da suke so wadannan mutane su yi. Kamar sharar magudanun ruwa na unguwarsu da sharar asibitin unguwa da gyaran makabarta. Mutanen unguwar ne za su ba da aikin da za su yi musu gwargwadon irin matsalar da suke fuskanta. Saboda haka za su yi wannan aiki ne da al’ummarsu suke so, ba hannun gwamnati a cikin fitar da wannan aiki. Ta haka ne al’ummar za su san cewa su ma sun ci gajiyar dimokuradiyya. Bayan sun gama tantancewa ne za a fada musu irin ayyukan da za su yi idan suka koma garuruwa ko unguwanninsu, kuma gwamnati za ta sai do, akwai jami’an da gwamnati ta nada da za su tafi kowane yanki domin su ga yadda suke gudanar da ayyukansu, kuma kowane wata ba wanda za a dauki kudinsa a hannu a ba shi, kudinsu ba zai bi hannun wani jami’in gwamnati ba, kowannensu kudinsa za a sanya masa ne a asusun ajiyarsa na banki. Yanzu haka ka ga jami’an bankuna mun kira su ne suna kuma bude wa kowanne daga cikinsu asusun ajiya. Duk wanda aka tantance shi take a wajen ake bude masa asusun ajiya a ba shi lambar asusun ajiyarsa ta banki, kowanne a cikinsu a kowane karshen wata zai ji karar shigar kudinsa cikin asusunsa na banki.

Ganin yadda matsalar tsadar rayuwa take ba za a iya cewa Naiar 7,500 ta kasa ba?

To idan ka yi la’akari da yadda kasar take a da, a baya ma ba a kwatanta haka ba, muna fata idan gwamnati ta samu karin kudi za a iya yin kari. Amma yanzu a ganinmu ba karamin kokari gwamnati ta yi ba da ta zakulo wadannan mutane kuma za a fara biyansu wannan kudi, na tabbata zai rufa asiri da yawa. Kuma wannan kudi fa an riga an cire shi an biya Bankin Duniya,  Bankin Duniya ma ya sa kudin a cikin asusun banki mai suna  bankin Skye Bank, illa kawai in wata ya yi a fara biya. Kudin shekara biyu da rabin nan na hannun banki.