Yadda Musulmi ke yin sallar Juma’a a coci a Amurka

Wata coci mai suna Church of the Epiphany wadda take birnin Washington DC na kasar Amurka ta kasance wani wuri da daruruwan Musulmi suke zuwa kowace ranar Juma’a don gudanar da sallar Juma’a.Musulmin sun kwashe kimanin shekara takwas suna halartar cocin duk ranar Juma’a, kamar yadda kafar yada labarai ta CBS News ta bayyana kwanakin […]

Yadda Musulmi ke yin sallar Juma’a a coci a Amurka
Yadda Musulmi ke yin sallar Juma’a a coci a Amurka

Wata coci mai suna Church of the Epiphany wadda take birnin Washington DC na kasar Amurka ta kasance wani wuri da daruruwan Musulmi suke zuwa kowace ranar Juma’a don gudanar da sallar Juma’a.
Musulmin sun kwashe kimanin shekara takwas suna halartar cocin duk ranar Juma’a, kamar yadda kafar yada labarai ta CBS News ta bayyana kwanakin baya.
Kafar ta ruwaito cewa a kowace ranar Juma’a, ana samun wani ladani da zai kira sallah, inda Musulmi masu yawa suke amsa kiransa zuwa cikin cocin don fara sauraron huduba gabanin fara sallah.
Cocin Epiphany ta bambanta da sauran takwarorinta ne saboda wani wuri ne da mabiya addinin Kirista da kuma Musulunci suke yin ibada a lokuta daban-daban.
Farook Syed shi ne wanda yake jagorantar shirya sallar, ya ce, cocin ta ba su damar ne bayan da ta fahimci cewa suna neman wurin gudanar ibadar sallah Juma’a.
Daga nan ya bayyana cewa lokacin da suka fara sallah a cocin sun fara ne da matune 50, amma yanzu sun fi su 300. Har ila yau, ya ce sallar Juma’ar da suke yi a kowane mako ya fi yawan Kiristocin da suke halartar cocin a ranar Lahadi.
Farook wanda irin mutanen nan ne da ba su da muhalli, ya Musulunta ne kimanin  shekara 15 da suka wuce. Kuma yana daya daga cikin dimbin mutanen da ba su da muhalli wadanda suke sallar Juma’a a cocin.
A cikin cocin dai akwai hotunan da ke nuni da gicciyar Isa Almasihu. Hakazalika, akwai lokutan da akan ji karar kararrawa cocin yayin da ake cikin sallah, kamar yadda kafar yada labaran ta bayyana.
Farook ya ce wannan abin mamaki ne “saboda akwai ranar da ana cikin huduba, sai kawai kararrawar cocin ta fara kadawa,” inji shi.