Yadda Musulunci ya ’yanta mace (5)
Mutumin da ba ya da kishi shi ake kira da Larabci da Duyus, wato mai tabbatar da kazanta a cikin iyalinsa, wato mutum ya zamo gaso-rogo ko mijin Hajiya, babu ruwansa da masu shiga kan iyalinsa ko masu hulda da su. Malamai sun ce: “Duyus shi ne wanda ba ya kishin iyalin gidansa, kuma an […]

Mutumin da ba ya da kishi shi ake kira da Larabci da Duyus, wato mai tabbatar da kazanta a cikin iyalinsa, wato mutum ya zamo gaso-rogo ko mijin Hajiya, babu ruwansa da masu shiga kan iyalinsa ko masu hulda da su. Malamai sun ce: “Duyus shi ne wanda ba ya kishin iyalin gidansa, kuma an samu gargadi mai tsanani tare da yi masa tattalin azaba a kan haka. An karbo daga Abdullahi dan Umar (RA) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Mutum uku Allah Madaukaki ba zai dube su (da idon rahama) ba a Ranar Alkiyama: Mai guje (saba) wa iyayensa da mace mai shigar maza da kuma Duyus (namiji marar kishin matarsa)” (Ahmad da Nisa’i suka ruwaito).
Nuna kishi ga hurumin kamewa rukuni ne sananne da ke kare martaba da dabi’un mutane a zamanin Jahiliyya da kuma bayan zuwan Musulunci. Domin shi, wata dabi’a ce da dan Adam ya ginu a kanta, dabi’a ce mai kyau da tsabta. Duk mutumin da ba ya da kishin iyalinsa, ba ya da bambanci da dabba. Domin dabba ce kawai ba ta kishin muharraminta.
A wannan fage ne Musulmi da sauran masu addinai suka sha bamban da masu rajin kare hakkin dan Adam da suke so su mayar da mutane tamkar dabbobi, inda a sakamakon haka yau aka wayi gari namiji yana auren namiji, mace tana auren mace. Sai suka zamanto mafi kaskancin masu kaskanci ma’ana suka fi dabbobi kasakanci wajen harkokin da suke gudanarwa a tsakanin jinsin halittarsu.
Ya kamata mata Musulmi su guji ruduwa da masu irin wannan kamfe da sunan ’yancin mace da suke neman sanya su fada da addini. Su je su karanci manufofin addinin Musulunci game da hakkokin maza da mata da ma hakkokin kowa domin su zauna a bisa basira da haske a kan gudunmawar da Musulunci ya bayar wajen ceto mata ga ’yantar da su.
Allah Ya shiryar da mu zuwa ga abin da yake daidai.