Yadda mutane ke kokarin sauya sunan wani layi zuwa ‘Layin ’Yan Koken a Legas
Titin 21 Road da ke tsakiyar Unguwar Festac a karamar Hukumar Amuwo Odofin da ke Jihar Legas zai ba ka sha’awa saboda gine-gine na zamani da ke wurin amma da ka ji cewa mutane suna kiransa da unguwar ’yan koken sai abin ya ba ka mamaki domin mutanen Festac suna kiran wurin da Cocaine Abanue […]

Titin 21 Road da ke tsakiyar Unguwar Festac a karamar Hukumar Amuwo Odofin da ke Jihar Legas zai ba ka sha’awa saboda gine-gine na zamani da ke wurin amma da ka ji cewa mutane suna kiransa da unguwar ’yan koken sai abin ya ba ka mamaki domin mutanen Festac suna kiran wurin da Cocaine Abanue wato Layin ’yan Koken.
Wani da ya shafe shekara 28 a unguwar mai suna Adamu Aliyu ya ce “Gaskiya ne ana kiran 21 Road da Cocaine Abanue saboda akwai masu harkar hodar Ibilis a wurin. Yawanci su ne suke da gidaje a wurin. Za ka rika ganinsu da manyan motoci. Shi ya sa mutane suka sanya wa wurin wannan suna, amma yanzu sun tashi sun koma wani wuri. Da layin shi ne ya fi kowanne cika a Unguwar Festac. Wuri ne da ake sheke aya, amma mu ba mu taba ganin ana sayar da hodar Ibilis ba, sai dai mun tabbatar cewa wadanda suke shigo da ita daga kasashen waje su ne a wurin a da. Sun tashi daga unguwar ne saboda sun fahimci mutane sun gano harkar da suke yi.”
Shi kuwa mai unguwa Buda Amadu da ya yi shekara 32 a wurin ya ce “Manyan mutane da ma’aikata da gwamnoni da ministoci suke zaune a unguwar. Ba a taba sayar da hodar Ibilis a wurin ba kawai suna ne mutane suka sanya wa wurin saboda manyan mutane da suke zaune.”
Ita ma shugabar ’yan kasuwa da ke yankin Festac Misis Abosade Ogunlaye da ta shafe shekara 36 a layin ta ce ana kira layin unguwar koken ne saboda irin mutanen da ke zaune a cikinsa.
Ta ce “Tun lokacin da na zo unguwar Festac na ji ana kiransa da sunan koken amma gaskiya mafi yawan masu zuwa suna shaye-shaye duk baki ne daga wurare daban-daban ba ainihin mazauna wurin ba.”
Sarkin Hausawan Festac, Alhaji Umaru Yunusa ya ce “Babu shakka na san ana kiran wurin haka amma ban taba kawo shi a kaina ba, amma ba zan iya gaya maka dalilin da ya sa mutane suke kiran sunan wurin unguwar ’yan koken ba.”
Da dama daga cikin mazauna wurin da Aminiya ta tattauna da su sun tabbatar da cewa masu harkar hodar Ibilis sun taba zama a unguwar shi ya sa mutane suke kiran ta da sunan.