Yadda mutanen Jigawa suka ƙi fita zaɓen ƙananan hukumomi 

Wasu sun bayyana cewar yin al’amuransu na yau da kullum ya fi musu komai.

Yadda mutanen Jigawa suka ƙi fita zaɓen ƙananan hukumomi 

An samu ƙarancin fitar masu kaɗa ƙuri’a a zaɓen ƙananan hukumomi da ya gudana a Jihar Jigawa.

An yi tsammanin mutane za su fita zaɓen domin kaɗa ƙuri’arsu, duba da yadda suka dinga ɗaukin zuwan ranar zaɓen.

Wakilin Aminiya, ya samu damar wasu mazaɓun jihar, sai dai ya lura cewa al’umma na ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum kamar yadda su ka saba, a yayin da malaman zaɓe suke jira masu zaɓen su fito.

Wasu da aka tattauna da su a yayin zagayen, sun nuna cewa sun manta cewa a wannan ranar ce za a gudanar da zaɓen.

Wani matashi mai suna Hamisu Adamu, wanda ya ce, “Wai dama yau ake zaɓen? Ni ai kwata-kwata na manta ma yanzu ka ganni shago zan tafi don ya fi mun mutunci, tun da ko ba komai zan samu na cefane, amma idan na tafi zaɓe wanda na zaɓa ba shi za su ba wa ba.

’Wannan zaɓen da shi da naɗi duk ɗaya ne, don haka babu buƙatar ɓata lokaci, kowa ya yi abin da zai fishe shi.”

Shi ma Muhammad Zulyadaini, ya ce bai ga amfanin zuwa zaɓen da babu abokan hamayya ba.

“Ni ka ganni ma wallahi yanzu daga filin ƙwallo na dawo, ina sane an ce yau za a yi zaɓe, amma ina amfanin ɓata lokaci?

“To kai ɗan jarida na tambaye ka ma, duk inda ka zaga ka ga inda wasu suka fito zaɓen? Ai wannan zaɓen kawai suna ne”, in ji shi.

Zaɓen ƙananan hukumomi na ci gaba da zama batun mahawara a Najeriya, inda wasu ke ganin duk da an bai wa ƙananan hukumomin ’yancin cin gashin kai ba lallai gwamnoni su bar su, su numfasa ba.

Masu son Abba ya tsaya da ƙafarsa za su cuce shi – Kwankwaso

Matatar Warri ta fara aiki bayan shekara 9

’Yan sara-suka sun yi wa tela kisan gilla a Jos

Bakanuwa ta zama ’yar Arewa ta farko da ta zama Kwamishinan ’yan sanda