Yadda mutum 3,150 ke rayuwa da masai 13 da rijiya daya a Bauchi

A karamar Hukumar Tafawa balewa da ke Jihar Bauchi, al’ummar garin Kutaru da Tsohon Fada su kimanin 3,150 ne suke amfani da shadda 13. Haka kuma duk yawan jama’ar garuruwan biyu, a rijiya daya da famfon tuka-tuka daya suke shan ruwa. Al’ummar kauyen Kutaru, suna rayuwa cikin kunci, domin ko asibiti babu, ga kuma yawan […]

Yadda mutum 3,150 ke rayuwa da masai 13 da rijiya daya a Bauchi
Yadda mutum 3,150 ke rayuwa da masai 13 da rijiya daya a Bauchi

A karamar Hukumar Tafawa balewa da ke Jihar Bauchi, al’ummar garin Kutaru da Tsohon Fada su kimanin 3,150 ne suke amfani da shadda 13. Haka kuma duk yawan jama’ar garuruwan biyu, a rijiya daya da famfon tuka-tuka daya suke shan ruwa.

Al’ummar kauyen Kutaru, suna rayuwa cikin kunci, domin ko asibiti babu, ga kuma yawan bayan gida da suke yi a bainar jama’a, wanda hakan na iya haifar musu da cututtuka.

Wakilanmu sun gano matsalolin wannan al’umma ce lokacin da wata kungiya mai zaman kanta NEWSAN ta za ga da su, a kokarin da take yi na samar wa jama’a ruwan sha mai tsabta. Jama’ar kauyukan sun nuna damuwa kwarai kan halin da suke ciki na rashin ruwa da na tsabtar muhalli.

Da yake bayyana halin da suke ciki, Sarkin Kutaru mai suna Boso Baba Boza ya ce hatta shi kansa a matsayinsa na Sarki, gidansa babu bayan gida, inda ya ce sukan shiga daji ne kawai su yi bayi. Ya ce, “Adadinmu zai haura mutum 1,650 da muke rayuwa a wannan kauyen na Kutaru. Muna da rijiya guda daya ce tak da famfon tuka-tuka guda daya. A da famfon tuka-tuka guda uku ne amma biyu sun lalace sai ya zamana saura daya ne ke aiki.”

Ya kara da cewa, “Akalla gidaje sama da 150 ne a wannan kauye, muna matukar shan wuya kan samun ruwa. Idan ka zo kauyen nan da rani sai ka tausaya mana, domin wahalar da muke sha wajen neman ruwa ba a magana.”

A cewar Sarkin, “Ni da iyalaina idan muna jin bayan gida, muna shiga cikin daji ne mu yi; kuma kusan dukan gidajen da suke kauyen nan haka muke yi. Gidajen da suke da masai a cikinsu ba su wuce goma ba, mafi yawa daga cikinsu ma sun lalace.”

Mai garin Kutarun ya ce, “Muna neman agajin hukumomin da abin ya shafa, su tausaya mana su dubi yadda muke rayuwa domin kawo mana dauki. Tabbas ba mu jin dadin yadda muke fama da kuma shan wuya kan sha’anin ruwa ba.”

Wani magidanci da ke zaune a kauyen na Kutaru mai suna Birsu Mato, ya bayyana yadda suke cikin ukuba kan sha’anin ruwa da tsabtar muhalli, “Ba za mu iya sanin adadin yaran da suke rayuwa a wannan kauyen ba; amma mu manya mun haura 1,500, gidaje kuma za su doshi 150. Muna rayuwa ne a cikin wahalar ruwa sosai, domin a ce mana wannan adadin amma muna amfani ne da rijiya daya da rijiyar tuka-tuka daya tak; masai kuwa babu a gidaje da dama; kai kanka ka san akwai matsala,” inji shi.

Birsu ya roki gwamnatoci da su kawo musu dauki domin ceto su daga kamuwa daga cututtuka. “Ba mu da asibiti a wannan kauye, idan mun samu rashin lafiya, mace ko yaro, mukan tafi Tafawa balewa ne ko Zwall,” inji shi.

kauyen Tsohon Fada da ke makwabtaka da Kutaru kuwa, lamarinsu ya fi kazanta. Da yake bayyana halin da suke ciki, Madaki Iliya na kauyen Tsohon Fada ya ce, “Da mazanmu da matanmu za mu kai mutum 1,500 da muke rayuwa a wannan kauye. A duk fadin kauyen nan babu rijiya ko famfon tuka-tuka ko guda daya.”

Madaki ya ce a baya wata gwamnati ta samar musu famfon tuka-tuka guda daya, shi din ma sun roka ne a wajen wani tsohon shugaban karamar hukumar, sai dai shi din ma famfon yanzu haka ba ya wani aiki sosai.

Ya ce ba su da masai, mutanensu na kutsawa cikin daji ne mazansu da matansu don yin bayan gida saboda masai guda uku ne kacal a duk fadin kauyen.

Da ya juya kan ruwan sha, Madaki ya ce “Mukan je wani kauye ne mai nisa kusa da mu idan muna bukatar ruwa a can muke debowa, kullum haka muke fama. A zahirin gaskiya muna shan wuya kan hidimar ruwa da kuma bayan gida. Muna yin bahaya a cikin daji amma mu ma hakan na damunmu.”

Ya ce sau tari idan ’yan siyasa suka je neman kuri’arsu, sukan shaida musu halin da suke ciki, sannan sukan yi musu alkawari amma da zarar sun ci ba su sake ganinsu sai wani zaben kuma. Madaki ya yi amfani da wannan dama ya roki gwamnati kan halin da suke ciki. “Muna roko don Allah in dai ana gwamnatin adalci ne, a zo a dubi yadda muke rayuwa a cikin kauyuka domin a inganta mana rayuwa,” inji shi.

Da yake jawabi kan dukan wuraren da aka ziyarta, jagoran tafiyar na shirin samar da ruwan sha mai tsabta da bayan gida, Mista Dabid Ayodele ya ce babbar hikimar da ke cikin wannan zagaye domin duba halin da jama’ar kauyuka suke ciki kan sha’anin ruwa da tsabtar muhalli, shi ne domin a fadakar da su, su nemi hakkinsu a wajen ’yan siyasa na tilasta musu kan su inganta musu sha’anin ruwa da tsabtar muhalli.

Ayodele ya ce da zarar aka kyautata sha’anin ruwa da muhalli, hakan zai kawo raguwar kamuwa da cututtuka da ake fama da su a cikin al’umma. Ya bayyana cewa sun kaddamar da wani kamfen mai suna “Wanda zai samar mana da ruwan sha mai tsabta kawai za mu zaba.”

Sai ya shawarci jama’ar kauyukan su yi amfani da kuri’arsu domin a kyautata musu harkar ruwa da muhalli. “Idan muka dauki kuri’armu a matsayin hanyar da za a kyautata mana sha’anin ruwa da tsabtar muhalli, shi ke nan sai mu zabi dan takarar da muka gamsu ya yi mana alkawarin idan ya ci zai inganta mana sha’anin ruwa, a dukan mukaman siyasa, kama daga dan Majalisar Jiha ko na Tarayya ko Sanata  ko Gwamna ko Shugaban kasa, idan sun zo mu yi alkawari da yarjejeniya da su a rubuce; su sa hannu mu sa hannu cewa idan sun ci zabe ga abin da za su yi mana. Idan ba haka ba ba za mu zabe su ba,” inji shi.