Yadda mutuwar ’yar aiki ta janyo cece-kuce a Kano
An dai zargi matar da lakadawa Khadija dukan tsiya sannan daga bisani ta zuba mata yaji a matancinta.
- Matar da muke wa aiki ce ta yi ta dukanta har ta mutu – Abokiyar aikin yarinyar
- Cizon muzuru ne ya yi sanadin mutuwarta – Inji wacce ake zargi da ’Yan Sanda
Ana ci gaba samun cece-kuce a jihar Kano bayan mutuwar wata yarinya mai kimanin shekaru 16 da haihuwa a gidan da take aikatau, inda bayanan musabbabin rasuwarta ke cin karo da juna.
Yayin da wata abokiyar aikinta a gidan da lamarin ya faru ta ce matar da suke yi wa aiki ce ta yi ta dukanta har sai da ta ce ga garinku nan, amma ’yan sanda sun ce binciken farko-farko ya nuna musu cewa cizon wani muzuru ne ya kashe ta.
- Magidanci ya caka wa matarsa wuka a kotu a Kano
- Buhari ya ba ’yan kasuwar da suka yi gobara a Sakkwato tallafi
Kazalika, ita ma matar, wacce har yanzu ba a fadi cikakken sunanta ba ita ma ta shaidawa Aminiya hakan.
Lamarin dai ya faru ne a unguwar Salanta dake yankin Sharada a Karamar Hukumar Birnin Kano da Kewaye, lokacin da matar gidan ta dawo ta ga yarinyar mai suna Khadija Rabi’u ba ta yi ayyukan da ta umarceta ta yi ba.
‘Ta yi ta dukanta, sannan ta zuba mata yaji a matancinta’
An dai zargi matar mai ’ya’ya hudu wacce yanzu haka take tsare a hannun ’yan sanda a shalkwatarsu dake Bompai da lakadawa Khadija dukan tsiya sannan daga bisani ta zuba mata yaji a matancinta.
Wata shaidar gani da ido, wacce ita ma ’yar aikin matar ce, Rafi’a Muhammad ta shaidawa Aminiya cewa sai da uwar dakin nasu ta gayyace ta don ta taya ta dukan Khadijan.
Ta ce, “Mun dawo daga unguwa tare da uwar dakin namu sai ta tarar Khadijan ba ta yi aikin da ta sa ta ba. Ko da ta tambaye ta me ya sa sai ta ce ba ta da lafiya ne, inda nan take ta fara zaginta, kafin daga bisani ta dauki tabarya ta fara dukanta da ita.”
‘Sai da ta gayyace ni in taya ta dukan yarinyar’
“Dagan an sai ta kira ni don in dauko mata wata sandar don in taya ta wajen dukan. Har na fara dukan nata nima, amma da na ga tana kuka sai na daina.
“Ta yi amfani da wani karfe wajen ji mata rauni a matancinta, sannan kuma ta umarce ni da na dauko mata yaji a dakin girki, wanda shine ta barbada mata a matancin nata.
“Nan take ta fadi a sume, tana numfashi da kyar inda ta garzaya da ita asibiti kafin daga bisani ta mutu a can.
“Ko bayan kai ta asibitin, ma’aikatan wurin sai su ka ki bata kulawa la’akari da yanayin da take ciki inda suka ce dole sai an kawo musu rahoton ’yan sanda kafin ma su taba ta,” inji Rafi’a.
‘An ji mata raunuka a sassa da daman a jikinta’
Aminiya ta gano cewa yarinyar, wacce ’yar asalin jihar Kwara ce ta ji munanan raunuka a sassa da dama na jikinta kafin ta mutu, kamar yadda wadanda suka yi mata wankan gawa suka tabbatar.
Daya daga cikinsu, Malama Ummulkhairi Shehu ta ce sun yi matukar kaduwa da irin raunukan da suka gani a jikin gawar yarinyar.
“Akwai raunuka da dama a jikinta; tun daga goshinta har fuskarta. An kuma ji mata rauni a hannunta, sannan kuma akwai tabbai a cinyarta.”
Mai anguwar Salanta, inda abin ya faru, Malam Magaji Garba ya ce shine ya jagoranci yi wa gawar yarinyar jana’iza kamar yadda iyalanta daga can jihar Kwara suka roke shi.
Shi kuwa a nasa bangaren, mai gadin gidan, Zakariyya Mamman ya ce ba shi da masaniya ko kadan kan abinda ya faru tsakanin uwar dakin nasu da kuma yarinyar.
“Gaskiya ni ban san komai ba a kan lamarin, kawai Hajiya ce ta bani labarin mutuwarta, inda ta ce min muzuru ne ya cije ta,” inji shi.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce sun fara gudanar da cikakken bincike a kan mutuwar yarinyar, ko da yake binciken farko-farko ya nuna musu ta mutu ne sanadiyyar cizon muzuru.