Yadda Muzaharar ’yan Shi’a ta haifar da hatsaniya da zubar da jini a Abuja

A ranakun Asabar zuwa Talatar da suka gabata ne aka yi arangama a tsakanin jami’an tsaron soja, ’yan sanda da kuma ’yan kungiyar Harkar Musulunci A Najeriya ko kuma ’yan Shi’a a takaice, inda al’amarin ya haifar da asarar rayuka daga bangaren ’yan kungiyar, kamar kuma yadda wasu jami’an tsaro suka samu raunuka da kuma […]

Yadda Muzaharar ’yan Shi’a ta haifar da hatsaniya da zubar da jini a Abuja

A qasa, an banka wa motar ‘yan sanda wuta. A sama, wasu daga ‘yan shi’a da aka kama da bama-baman kwalba

A ranakun Asabar zuwa Talatar da suka gabata ne aka yi arangama a tsakanin jami’an tsaron soja, ’yan sanda da kuma ’yan kungiyar Harkar Musulunci A Najeriya ko kuma ’yan Shi’a a takaice, inda al’amarin ya haifar da asarar rayuka daga bangaren ’yan kungiyar, kamar kuma yadda wasu jami’an tsaro suka samu raunuka da kuma yadda aka kona motar ’yan sanda.

Tun a ranar farko na tattakin “Arba’ina” wato ranar Asabar da ta gabata ce aka samu asarar rayuka 6 na wasu ’yan kungiyar a garin Zuba-Abuja, bayan wata arangama a tsakaninsu da kuma wani ayarin soja kuma daga ranar ce sojojin suka kara damarar killace daukacin mashigogin birnin na Abuja don hana mabiyan kai wa ga cikin kwaryar birnin.

Xaya daga cikin ‘yan Shi’a da aka harba a yayin arangamar Abuja

Sai dai duk da karin matakan tsaron, mabiya Sheikh Ibrahim Elzakzaki din sun samu damar kutsawa cikin kwariyar birnin tare da gudanar da “Tattakin” a yankin Unguwar Wuse 2 a ranar Talata da ta gabata, wanda ke matsayin muzahara ta karshe daga ranaku hudu da suka diba domin aiwatar da ita.

’Yan kungiyar kamar yadda suka fitar da sanarwa tun a farko, sun bayyana cewa za su gudanar da tattakin ne na tsawon kwana 4 wato daga ranar Asabar zuwa Talata a matsayin mataki na nuna alhini ga mutuwar jikan Manzon Allah, Annabi Muhammad SAW, wato Imam Hussain, kan kisan gilla da aka yi masa a birnin Karbala tare da tilasta wa mabiyansa ciki har da wasu Ahlil bait yin tattaki zuwa kasar Sham daga kasar ta Iraki a shekara ta 61, kamar yadda suka bayyana.

Haka nan sun ce za su yi amfani da wannan damar wajen ci gaba da fafutikar ganin an sako jagoransu Sheikh Ibrahim Elzakzaki kamar yadda kotu ta ba da umarni, wanda jami’an tsaro suka kama a shekarr 2015, a lokaci irin wannan a birnin Zariya; bayan samun wata arangamar tsakanin sojoji da mabiyansa, al’amarin da ya samo asali daga hana ayarin Babban Hafsan Sojin Najeriya Janar Tukur Yusuf Burtai wucewa ta wata hanya da suke gudanar da al’amuransu a birnin na Zazzau.

Ko a yayin wannan tattakin ma, sojoji sun yi zargin cewa mabiya Zakzakin ne su ka fara takalarsu ta hanyar jifar su da duwatsu a garin na Zuba, a daidai lokacin da suka bukaci su buda hanya a kusa da gadar sama da ke garin, inda suka taru kusa da wajen sannan aka samu cunkoson ababen hawa. Sojojin, wadanda ke tafiya a cikin wasu motocinsu uku da suka hada da babbar mota da ke dauke da harsasai, sai kuma motocin A-kori-kura biyu da ke yi wa kayan rakiya; kamar yadda sanarwar da suka fitar ta bayyana. Sun yi zargin cewa mabiya kungiyar ta ’yan Shi’a sun yi ta jifar su da duwatsu a lokacin, inda ta kai ga jami’ansu biyu fuskantar raunuka kamar yadda bayanin nasu da ke dauke da sa hannun Kwamandan sojoji a babbar hedkwatarsu ta kasa, Manjo-Janar James Nyam ta bayyana.

Sai dai a nasu bangaren, kungiyar ’yan Shi’an ta ce sojojin sun kashe masu mutum 6 baya ga mutane 10 da suka yi wa rauni, sannan ba su tashi jifar sojojin da duwatsu ba sai bayan da sojojin suka harbe su da bindiga, inda su kuma suka mai da martani da jifa a matsayin kariya kamar yadda wani jagoransu mai suna Malam Aliyu Umar ya bayyana wa Aminiya.

Haka nan kungiyar ta yi zargin cewa harbi a kan mutanen nata da sojin suka yi bai da nasaba da yunkurin kare kai kamar yadda sojojin suka yi korafi, illa dai wata kulalliya ce aka tsara tun a farko, inda suka ce sun faro tattakin daga sarin Suleja, suka bi ta unguwar Madalla, sannan suka isa garin Zuba, duk ba tare da yin wani fito-na-fito da jami’an tsaro ba, sai wadanda suka yi kicibis da su a kan hanya. Sun ce al’amarin ya faru ne a lokacin da suke shirin rufe taro da addu’o’i don watsewa.

A rana ta biyu, wato Lahadi da kuma ta Litinin, ’yan kungiyar sun samu damar matsawa gaba, inda suka gudanar da tattakinsu a kan babban titin Kubwa zuwa Abuja bayan sun rika shigowa a ababan hawa a daidaikunsu a maimakon tahowa cikin ayari kamar yadda majiyoyi suka bayyana. Haka nan Aminiya ta samu labarin cewa wasu mabiyan kungiyar da suka taho daga wasu jihohin kasar nan daga kusuruwar Maraba, idan za a shigo Abuja.

Sun fara tattakinsu ne daga garin Masaka ta Jihar Nassarawa, sannan suka yada zango a wani babban sansanin kungiyar da ke kusa da kasuwar Kara da ke garin Maraba, inda daga can ne kuma suka taso kashegari ranar Litinin da nufin gama kai da wadanda ke fitowa daga bangaren Kubwa, wadanda suka taso daga jihohin kasar nan da ke wannan kusuwar don taron babban gangami na innanaha a tsakiyan birnin Abuja, wanda aka bayyana da na sai-baba-ta-gani.

Sai dai a wannan yinin na Litinin, an samu mummunar arangama a tsakanin ’yan Shi’an da kuma sojoji da suka ja daga a shingensu da ke kusa da gadar Karu-Abuja, inda aka karfafa matakan tsaro. A wani jawabi da wani jagoran ’yan kungiyar mai suna Malam Muhammad Gamawa ya yi ta kafar talabijin din Chanells, wanda kuma wani jagoransu Malam Abdulhamid Bello ya kara tabbatarwa a yayin zantawa da Aminiya, sun bayyana cewa an fuskanci asarar rayuka masu yawa a ranar daga bangarensu, sai dai ba a samu sanarwa daga bangaren soja ba a kan lamarin, kasancewar mai magana da yawun rundunar, Birgediya Janar Tedas Chukwu ya ce ba ya gari a lokacin da aka tuntube shi, a don haka ba zai ce komi ba.

Haka nan shi ma mai magana da yawun ’yan sanda na Abuja DSP Anjuguri Manzah, a lokacin da Aminya ta tuntube shi kan lamarin, ya ce wannan al’amari ne na soja, a saboda haka su ne ya kamata a tuntuba ba ’yan sanda ba. Sai dai a daya bangaren na masu tattakin na babban titin Kubwa-Abuja, an tashi taron a ranar lafiya ba tare da samun wata hatsaniya ba, inda sojoji da suka ja daga a yankin Katampe don ganin  cewa ’yan Shi’an ba su tsallaka shingensu ba. Sannan su kuma mabiyan suka watse da misalin karfe 5 na maraice.

A ranar Talatar da ta gabata kuwa, wadda ke matsayin rana ta karshe a tsarin tattakin, ’yan kungiyar sun bai wa jami’an tsaro mamaki, inda suka kai ga shiga tsakiyar kwaryar birnin, a sakamakon shigar basaja da suka yi, sannan suka fara tattakinsu daga ofishin hukumar kare hakkin bil’Adama (National Human Right Commission). Majiyoyi sun bayyana cewa ’yan kungiyar wanda a yayin tattakin farko yawancinsu na sanya bakaken kaya ne da ke alamta abin da suke yi, wato nuna bakin ciki, sun surka yanayin suturarsu a ranar, inda hakan ta sa jami’an tsaro da ke sa ido a kan motoci da ke wucewa, inda a wani zubin sai an fitar da wadanda ke cikin mota tare da bincika abin da suka riko, ko za a ga wani abu da ke da nasaba da su, ta sa ba a iya gane su ba.

Malam Abdulhamid Bello, yana Sallatar gawarwaki 6 na ‘yan Shi’a da aka kashe a Zuba, Abuja

Haka nan bayanai sun ce wasu sun kama hayar dakuna a otal-otal na cikin birnin, sannan da gari ya waye aka hade a mahada, a daidai lokacin da aka ajiye za a hadu. Sai dai a arangamar cikin gari, wadda dama yawanci jami’an tsaron ’yan sandan kwantar da tarzoma ne da ke sa ido a kai, ya fi karfi ne wajen watsa wa mabiyan barkonon tsohowa a maimakon harsashin bindiga da ake zargin bangaren soja da yi, a yayin da su kuma mabiyan ke maida martani da jifa a kan hanyarsu ta kai wa ga babbar Sakatariyar Abuja, wurin da ya kunshi ofisoshin gwamnati mafi yawa, sannan ba ya da nisa da majalisar kasa da kotun koli da kuma fadar Shugaban Kasa.

A yayin arangamar, an ga wata motar ’yan sanda na ci da wuta bayan zargin jefa mata nakiyar kwalba da ke dauke da fetur daga bangaren masu tattakin. Sai dai bangaren ’yan Shi’an ko a ranar sun yi zargin an kashe masu wasu mambobi a lokacin kamar yadda wani jagora a harkar ya bayyana. Haka nan sun ce an kama masu mabiya sama da 700 daga matsayoyin mota ko kan titi bayan an tashi taron.

Sai dai a sanarwar da ’yan sanda su ka fitar, sun ce mutum 400 ne suka kama, ciki har da wani saurayi mai shekara 20 mai suna Mustafa Abdullahi da ya fito daga Unguwar Gwari cikin Garin Suleja wanda suka ce sun same shi da kwalabe 18 da ke dauke da fetur bayan tsayar da motar tasi da ya dauko shata a daidai yankin Tifa-Gareji na mashigar Abuja. Sai kuma wani mai suna Abdullahi Umar mai shekara 22 da ya taho daga Gadan Karte da ke Karamar Hukumar lllela Jihar Sakkwato, wanda ’yan sandan suka ce sun kama shi dauke da irin kwalaben guda 13 a shingensu da ke tsakanin garin Dakwa a yankin Abuja, kamar yadda su ka sanar.

Tattakin wanda ya jawo asarar rayuka daga bangaren ’yan Shi’a, sai kuma cunkoson ababan hawa na tsawon lokaci tare da barazanar fashewar gilasan mota a wani zubin, ’yan kungiyar sun ce ba za su daina yinsa ba a kowace shekara, kasancewar tamkar addini ne a gare su kamar yadda wani babban malami a kungiyar ya shaida wa Aminiya a yayin wata zantawa. Haka nan wata majiya a kungiyar ta ce duk da cewa tattakin “Arba’ina” ya kare, za ta ci gaba da muzahararta ta yau da kullum da ta saba yi a cikin Abuja na lallai sai an sako mata jagoranta kamar yadda kotu ta ba da umarnin a yi.