Yadda N200 ta yi sanadin mutuwar masu tura baro 2 a Aba

Wata takaddama mai zafi da ta kai ga fada tsakanin wasu masu tura baro su biyu a birnin Aba na Jihar Abiya, ta yi sanadiyyar mutuwar duka su biyun a ranar Talata. Da take tabbatar da labarin a ranar Laraba a ofishinta da ke Aba, rundunar ’yan sandan Jihar ta ce takaddamar da ta barke […]

Yadda N200 ta yi sanadin mutuwar masu tura baro 2 a Aba

Wasu masu tura baro (tsohuwar ajiy)

Wata takaddama mai zafi da ta kai ga fada tsakanin wasu masu tura baro su biyu a birnin Aba na Jihar Abiya, ta yi sanadiyyar mutuwar duka su biyun a ranar Talata.

Da take tabbatar da labarin a ranar Laraba a ofishinta da ke Aba, rundunar ’yan sandan Jihar ta ce takaddamar da ta barke tsakanin mutanen ta rikide zuwa fada daga bisani kuma ta kai ga mutuwar daya daga cikinsu.

Kakakin rundunar a Jihar, SP Geoffrey Ogbonna ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) cewa mutuwar daya daga cikin masu fadan ce ta tunzura wasu suka fusata sannan suka kashe daya abokin fadan shi ma.

Ya ce tuni ’yan sandan suka kai gawarwakin mutanen zuwa dakin adana gawarwaki a asibiti.

Wani ganau a inda lamarin ya faru ya shaida wa manema labarai cewa a ranar Talata ne wasu masu tura baron suka shiga cacar baki kan wanda zai dauki kayan wani kwastoma a kasuwar makabarta da ke birnin na Aba.

Hakan, a cewarsa ya sa mutanen sun fara fada da makamai a kan wanda ya kamata ya karbi N200 daga hannun kwastoman da suka taimaka wa wajen daukar kayan.

Sai dai fadan ya kara kamari ne lokacin da mutanen suka ki jin hakurin da mutane da ma mai kayan suka hadu suna basu a kan lamarin.

A cewar ganau din, daya daga cikin masu fadan ya caccaka wa abokin fadan nasa wuka a ciki da kuma wuya da ma wasu sassa na jikinsa, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa.

Ganin cewa abokin fadan nasa ya mutu ne ya sa mutumin ya yi kokarin tserewa, amma jama’ar da ke wurin suka yi masa kofar rago shi ma suka kashe shi nan take. (NAN)