Yadda N50 ta yi ajalin mai sayar da sigari
Canjin Naira 50 ne ya yi sanadin kaurewarsu da fada.
’Yan sanda a Jihar Ogun sun cafke wani mutum da ya yi wa mai sayar da sigarin dukan kawo wuka, wanda ya yi ajalinsa kan canjin Naira 50.
An cafke matashin da ke zaune a yankin Oladun a Ikotun na Jihar Legas, bayan shigar da kara da mahaifin mamacin, Adamu Abubakar ya yi.
- An kaddamar da Shafin kallon fina-finan Hausa zalla a Intanet
- Tinubu ya yi ganawar sirri da Shekarau
Dan sanda mai shigar da kara, ya shaida wa kotu cewa matashin ya zo shagon dan nasa da ke unguwar Ajegunle a Idiroko don siyan sigari.
Ya kara da cewar matashin ya dawo daga baya don karbar canjinsa na Naira 50 a wajen dan nasa.
A cewarsa, lamarin ya kai su ga cece-kuce, har ta kai ga matashin ya hau dansa, Mukaila Adamu, da duka.
Kazalika, ya ce nan take dan nasa ya yanke jiki ya fadi, wanda hakan ya sa suka garzaya da shi asibiti wanda a can ne aka tabbatar da rasuwarsa.
Kakakin ’yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi ya ce bayan samun rahoton faruwar lamarin, aka aike da jami’an ’yan sanda wanda suka yi nasarar cafke wanda ake zargin da silar rayuwar mai sayar da sigarin.
Kakakin, ya ce an kai gawar zuwa dakin ajiye gawarwaki don gudanar da bincike.
Oyeyemi ya ce Kwamishinan ‘yan sandan jihar, ya bayar da umarnin mayar da lamarin zuwa babban sashen binciken manyan laifuka don zurfafa bincike.