Yadda na ƙi karɓar cin hancin N5bn a gwamnatin Tinubu – Tsohon Hadimi

Tsohon hadimin ya ce halaye masu kyau da gaskiya ne kaɗai za su hana mutum karɓar cin hanci a Najeriya.

Yadda na ƙi karɓar cin hancin N5bn a gwamnatin Tinubu – Tsohon Hadimi

Tsohon Hadimin Shugaban Ƙasa a fannin Ƙimar Ƙasa da Zamantakewa, Fela Durotoye, ya bayyana yadda ya ƙi karɓar tayin cin hancin Naira biliyan biyar yayin da yake aiki a Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Yayin da yake jawabi a wani taro a Abuja, Durotoye ya ce wani jami’i da ya ce shi limamin coci ne, ya matsa masa lamba domin ya ƙara farashin wani shirin horo da gwamnati ta shirya.

Ya bayyana cewa tawagarsa ta ƙiyasta kuɗin aikin zuwa Naira biliyan 1.3, amma bayan kwana uku, aka ce masa ya gabatar da takardar lissafi zuwa Naira biliyan biyar.

“Sun ce kuɗin da na nema ya yi kaɗan, sun ce za su ƙara shi zuwa Naira biliyan biyu.

“Daga nan ne suka buƙaci na ƙara lissafin zuwa Naira biliyan biyar,” in ji shi.

Lokacin da ya tambayi dalilin ƙarin kuɗin, sai jami’in ya ce masa kada ya damu.

“Ya ce min, ‘Ba wani laifi a ciki. Ka yi wa Najeriya hidima sosai, yanzu lokaci ya yi da Najeriya za ta saka maka da alheri,’” in ji Durotoye.

Ya ce ya ƙi yarda da tayin, kuma don guje wa damunsa, sai ya kashe wayarsa.

Watanni kaɗan bayan haka, ya samu labarin cewa an kama wasu jami’an gwamnati da suka wawure Naira miliyan 426 daga kuɗin wani shirin horo da aka shirya.

Durotoye, ya jaddada cewa gaskiya da ɗa’a ne kaɗai za su taimaka wa mutum gujewa cin hanci a Najeriya.

“Idan muna da kyawawan halaye, ba za a samu cin hanci da rashawa a ƙasarmu ba,” in ji shi.

Babban layin wutar lantarki ya faɗi karon farko a 2025

Na yi nadamar yi wa Tinubu kamfe a 2023 — Ɗan Bilki Kwamanda

Yadda na ƙi karɓar cin hancin N5bn a gwamnatin Tinubu – Tsohon Hadimi

Zulum ya bai wa sabon Shehun Bama sandar sarauta