Yadda na ba Ibro umarni a fim dinsa na karshe – Darakta Tantiri
Fitaccen daraktan fina-finan barkwanci Iliyasu Abdumumini Tantiri ya bayyana yadda ya ba jarumin barkwanci marigayi Rabilu Musa Ibro umarni a fim dinsa na karshe mai suna ‘Babban Direba’. A hirar da Mujallar Fim ta watan Fabrairu, 2015 ta yi da daraktan ya ce shi ne darakta na karshe da ya ba marigayin umarni, inda suka […]
Fitaccen daraktan fina-finan barkwanci Iliyasu Abdumumini Tantiri ya bayyana yadda ya ba jarumin barkwanci marigayi Rabilu Musa Ibro umarni a fim dinsa na karshe mai suna ‘Babban Direba’.
A hirar da Mujallar Fim ta watan Fabrairu, 2015 ta yi da daraktan ya ce shi ne darakta na karshe da ya ba marigayin umarni, inda suka kammala daukar fim din a ranar 26 ga Oktoba, 2014.
Ya ce: “Mun gama daukar fim din a ranar 26 ga Oktoba, 2014, kuma na san shi ne fim dinsa na karshe, daga nan sai ya kwanta rashin lafiya. Nakan kira shi a waya, sai ya ce da ni ya samu sauki, amma idan na kira Malam Dare sai ya ce yana jin jiki, ka san shi mutum ne da ba ya son a san ba shi da lafiya, har aka kai shi Indiya.
Ya ce ya fahimci marigayin ba shi da lafiya ne a lokacin da suke daukar wata fitowa ta fim din ‘Babban Direba’ a Tiga, inda marigayin ya yi wani irin amai.
“Abin da zan iya tunawa a game da al’amarin aikinmu shi ne, ka san Ibro mutum ne da yake da juriya, don zai iya zuwa aiki ba shi da lafiya ba tare da ya sanar da kai ba, sai dai idan kuna da kusanci da shi, to shi ne zai fada maka. A lokacin da muke aikin ‘Babban Direba’, mun kai kwana biyar muna aiki ban san ba shi da lafiya ba. Abin da zan tuna akwai lokacin da muke daukar wata fitowa a Tiga, sai aka kawo mini kifi, sai ya ce in dan yaga masa, yana ci sai ya ce a nuna masa wajen zagayawa. Kafin a samu sai na ga ya yi wani irin amai wanda duk wanda ya gan shi sai ya tausaya masa. To sai a nan ne na san ba shi da lafiya. Sai na ce ko akwai maganin da za a kawo masa? Sai Manajansa Malam Dare ya ce akwai maganin da ake ba shi, da aka kawo aka ba shi sai ya ci gaba.” Inji Tantiri.
Daraktan ya ce abin mamakin shi ne yadda marigayin ya rika yin aiki kamar yana da cikakkiyar lafiya, inda ya rika tuka babbar mota har nake cewa da shi ko za a daga aikin ne? Sai ya ce a ci gaba. Shi dai yana so a kammala da shi a ranar. Har zuwa goma na dare muna aiki. Muna gamawa sai ya jefe ni da riga ya ce ga kayanka nan. Sai nake cewa da shi, kai da ba ka da lafiya idan na zo ma zaluntar ka zan yi, daga nan ban kara ganinsa ba sai a cikin likkafani.”
Batun ma’amala tsakanin daraktan da marigayin sai ya ce, “to ina daya daga cikin mutanen da muke wasa da tsokanar juna da shi, abin da na sani shi ne, shi mutum ne da ba ya magana, kuma ba ya shiga harkar da ba tasa ba, don haka idan yana waje zai yi wahala ka ji yana magana, amma idan aka dora masa kyamara duk sai ya buwayi mutane, kuma yana da saukin kai.”