Yadda na dauki nauyin karatuna da sana’ar aski – Daniel Paul

Wani matashi da ke sana’ar askin baba a garin Abuja mai suna, Daniel Paul, ya ce ya samu ci gaba mai yawa a sana’ar domin da ita ya rika biyan kudin karatunsa tun daga sakandare har jami’a.Daniel wanda dan asalin kauyen Gulak ne a cikin karamar hukumar Madagali da ke Jihar Adamawa, ya bayayana hakan […]

Yadda na dauki nauyin karatuna da sana’ar aski – Daniel Paul
Yadda na dauki nauyin karatuna da sana’ar aski – Daniel Paul

Wani matashi da ke sana’ar askin baba a garin Abuja mai suna, Daniel Paul, ya ce ya samu ci gaba mai yawa a sana’ar domin da ita ya rika biyan kudin karatunsa tun daga sakandare har jami’a.
Daniel wanda dan asalin kauyen Gulak ne a cikin karamar hukumar Madagali da ke Jihar Adamawa, ya bayayana hakan ne lokacin da yake tattaunawa da Aminiya a shagonsa da ke unguwar Jabi a Abuja, a karshen makon jiya.
Ya ce: “Tun ina karami na koyi sana’ar aski a wurin yayana. Na samu kwarewa a sana’ar na iya duk wani nau’i na askin zamani da ake yi a yanzu. Tun a wannan lokaci na fara tara kudi. A lokacin da na shiga sakandare ni na rika daukar nauyin kaina har na gama. Da na samu gurbin karatu a jami’ar Maiduguri a bangaren Harshen Turanci a shekarar 2007, sai na tsara lokutana ina karatu, ina aski a haka har na kammala a shekarar 2011.”
Daga nan ya ci gaba da cewa: “Duk lokacin da nake da darasi, sai na bari na tafi a ji don daukar darasi idan muka kammala kuma na ga ina da isasshen lokaci sai na dawo na ci gaba da aski. A yanzu gashi har na kammala bautar kasa na dawo na ci gaba da sana’ar.”
Matashin wanda har yanzu bai samu aikin albashi ba, ya bayyana cewa yana ci gaba da neman aiki.
“Har yanzu ina neman aiki. Idan na samu ba zan bar sana’ar aski ba. Zan ci gaba da yi domin ba zan bar sana’ar aski ba har abada kuma zan koya wa ’ya’yana su ma su ci abinci a ciki don sana’ar tana da rufin asiri sosai. Ka ga ni ma ba don na koyi sana’ar ba, da na sha wahala sosai. Don akwai abokaina da muka gama karatu tare, amma har yanzu ba su samu aiki ba kuma ba su iya wata sana’a ba. Ka ga dole mutum ya sha wahala,” inji shi.
Sai dai ya yi kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya ido dangane da guraben ayyukan da zai samarwa matasa don “kada ’yan ba-ni-na-iya su damfari jama’a.”
Ya yi kira ga matasa musamman ma wadanda suka kammala karatun zamani su koyi sana’a don a cewarsa ita ce mafita a zamanin da ake ciki.
Ya yi fatan idan ya samu aiki zai bunkasa sana’arsa ya kara jari don samarwa da matasa aikin yi.