Yadda na fara rubutun yaran bebaye a kasar Hausa – Dokta Constanza
Dokta Constanza Halima Schamailing, wadda ake yi wa lakabi da Halima ’yar Fulani ko ’Yar kamus, Bajamushiya ce da ta kware a harshen Hausa, kuma ta yi karatun digirinta na uku a Hausa. Ta shafe shekaru tana gudanar da nazari kan Harshen Bebaye a kasar Hausa. Baya ga kundin digirinta, Halima ta rubuta kananan litattafai […]
Dokta Constanza Halima Schamailing, wadda ake yi wa lakabi da Halima ’yar Fulani ko ’Yar kamus, Bajamushiya ce da ta kware a harshen Hausa, kuma ta yi karatun digirinta na uku a Hausa. Ta shafe shekaru tana gudanar da nazari kan Harshen Bebaye a kasar Hausa.
Baya ga kundin digirinta, Halima ta rubuta kananan litattafai daga ciki akwai Maganar Hannu: Harshen Bebaye na kasar Hausa, na daya da na biyu. Kuma a halin yanzu tana kan aikin littafi na uku.
Aminiya ta tattauna da Halima ‘Yar Fulani kan wannan gagarumin aiki da take gudanarwa. Ga dai yadda hirar ta kasance:
Aminiya: Masu karatunmu za su son jin tsakaitacccen tarihinki?
Dokta Constanza: Ni dai an haife ni a birnin Berlin babbban birnin kasar Jamus, a nan kuma na yi karatun Firame da Sakandare. Daga bisani na yi karatun harsunan Afirka a Hamburgh, sai kuma na taho Kano a Najeriya, inda na shiga Jami’ar Bayero a tsakanin shekarun 1988 zuwa 1989 na yi karatun digiri a Hausa a Sashen Nazarin Harsunan Najeriya. Sannan na je birnin Landan, inda na yi karatu a makarantar nazarin harsuna da al’adun Afirka, wato SOAS (School of Oriental and African Studies). Tun daga wancan lokaci nike zuwa Kano in yi watanni biyu zuwa uku, har na kammala karatun digirina na uku, inda na gudanar da bincike kan Harshen Bebaye na kasar Hausa a shekarar 1993.
Aminiya: Mene ne ya ja ra’ayinki kika yi sha’awar bincike a kan harshen Bebaye a kasar Hausa?
Dokta Constanza: Na zauna a cikin birnin Kano. Lokacin da nike zaune a cikin gari, akwai Bebaye kusa da gidanmu, gninsu ya sa na yi tunanin gudanar da bincike tare da walafa kamus na maganar bebaye a kasar Hausa.
Na rika zuwa wurraren da suke taruwa har da makarantar Shahuci. Na kuma je Tudun-Maliki da ma’aikatun gwamnati. Kai sai da ta kai ga na rika yin tafinta a ma’aikatu da wurarenh wa’azin Musulunci da bebaye ke yi.
A makarantar Tudun Maliki ne aka hada ni da wani dalibi Bebe mai hazaka, har na fara aikin kamus din maganar kurame. Muna cikiin aiki da wannan dalibi mai suna Lawan sai kwatsam ya rasu, wannan rasuwar tasa ta sa aikin namu ya tsaya. Amma a halin yanzu na samu ci gaba, kodayeke dama na yi littafi na farko da na biyu. Yanzu ina ci gaba da littafi na uku.
Aminiya: Wane ne ke daukar nauyin wannan aiki da kike yi?
Dokta Constanza: Ina samun tallafi ne daga Cibiyar yada Al’adun Jamusawa ta Goethe Institute. Duk wannan cibiyar ce ta dauki nauyin wallafa wadannnan littattafai na daya da na biyu. Kuma insha Allahu zan yi littafi na uku da na hudu. Koda yake a halin yanzu ma ina yin littafi na uku, amma na hudu in sha Allahu da kudin Sarkin Kano zan yi shi.
Aminiya: Mai martaba Sarkin Kanon ya ba ki kudin gudanar aikin littafin ne?
Dota Constanza: A’a, amma jiya na je Fada. Ba dai zan yi bayani ba sai littafina ya fito.
Aminiya: wadanne sakonni littattafan naki ke daukee da su?
Dota Constanza: Littafi na farko yana magana ne kan yadda bebaye ke nuni kan abin da ya shafi iyali, na biyu kuma kan Haduwa da Sadarwa, wannan na ujku da nike yi zai zama mai nuni da siffofi, shi kuwa na hudu ban sa masa suna bsa.
Aminiya: Wacce shawara za ki bai wa masu bincike?
Dota Constanza: a rika yin binciken da za a samar da dabarun amfani da sakamakomn binciken. Domin ina jin takaicin yadda ake yawan ajiye sakamakon bincike a dakin karatu, wato laburare wasu suna yin kura. Kuma akwai bukatar gwamnati ta rika zuba kudi don gudanar da binciken a cibiyoyin ilimi saboda su ne za su yi amfanai da sakamakon binciken. Kuma ta rika daukar nauyin binciken, domin akwai bukatar kudi ga masu yin aiki irin wannan.