Yadda na gano cewa sunayen Allah 29 cikin 99 ba su da inganci – Shaikh Ahmad Saleh
Aminiya ta samu tattaunawa da Shugaban Majalisar Malamai na kungiyar Izalatul Bid’a Wa’ikamatus Sunnah reshen kasuwar Alaba, Shaik Ahmad Saleh Waff, wanda ya wallafa littafin da ya tace sunayen Allah ingantattu da marasa inganci da ma irin sunayen Allah, wadanda nazarin malamin ya nuna cewa ba su dace mutane su rika sanyawa ’ya’yansu ba. Ga […]
Aminiya ta samu tattaunawa da Shugaban Majalisar Malamai na kungiyar Izalatul Bid’a Wa’ikamatus Sunnah reshen kasuwar Alaba, Shaik Ahmad Saleh Waff, wanda ya wallafa littafin da ya tace sunayen Allah ingantattu da marasa inganci da ma irin sunayen Allah, wadanda nazarin malamin ya nuna cewa ba su dace mutane su rika sanyawa ’ya’yansu ba. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
Kwanakin baya ka wallafa littattafai, ko za ka yi mana bayani game da su?
Na wallafa littafi mai suna ‘Yadda Ake Daidaita Sahu A Sallah’ da kuma littafin ‘Sunayen Allah Ingantattu Da Wadanda Ba Ingantattu Ba.’ Dalilin da ya sa na rubuta littafin shi ne, akwai sunayen Allah dari ba daya da ake rokon Allah da su amma jama’a ba su san akwai sunayen da ba su inganta ba kuma ma har akwai sunayen da ba ingantattu ba da mutane suke sanya wa ’ya’yansu. Sannan kuma akwai sunayen Allah da mutane bai dace su sanya wa ’ya’yansu ba.
Shi wannan littafi na Sunayen Allah, ya aka yi ka wallafa shi?
Kamar yadda na fada, malamai tun kusan a karni fiye da 100 bayan hijira suka tace hadisin da Imamul Turmizi ya ruwaito daga wasu malamai wadanda a cikinsu akwai wadanda suke da rauni. Shi Imamul Turmizi ya kawo hadisin da yake lissafa sunayen Allah 99. To sai malamai irin su Imamul Zahabi da Shaik Hajarul Askalani da Ibni Taimiyya da su Shaik Nasiruddinul Albani suka yi bincike suka gano cewa daga cikin sunayen Allah 99, akwai 29 da ba su da inganci. Sannan kuma akwai wadansu sunayen Allah masu inganci da ba a sanya su cikin jerin 99 ba. Daga cikin sunayen Allah da ba su da inganci akwai misali ‘Alhadi.’ Shi ya sa idan aka ce maka sunan ‘Alhadi’ ba sunan Allah ba ne, za ka yi mamaki ka rika cewa ai an dade ana karanta shi a cikin sunayen Allah kuma an dade ana sanya wa yara sunan ‘Abdulhadi.’ Hakazalika sunayen ‘Almaajidu’ da ‘Alwajidu’ da ‘Almuntakimu’ da ‘Alwaalee’ da ‘Zuljalali Wal’ikram’ duk ba su da inganci.
Malam ba ka ganin cewa lokaci bai yi ba na fitar da irin wadannan littattafai, ganin irin karancin ilimi da jama’a suke da shi?
Ai ta hanyar karatu ake iya gane gaskiya. Kamar yadda na yi bayanai, haka shi ma Shaikh Ibn Kasir ya fada kamar sauran malamai. Malamai da yawa sun yi kokarin tantance sunayen don su fadakar da jama’a. Mun gode wa Allah, a yanzu da yake akwai kayan bincike da na’ura mai kwakwalwa, a yanzu an riga an tantace sunayen baki daya saboda haka ba abu ne mai wahala ba. Manzon Allah bai rufe kofar bincike ba kuma malamai sun nuna cewa Ijtihadi ba zai taba gushewa ba har zuwa ranar tashin kiyama.
Sunayen Allah masu rauni da bincikenka ya gano, guda nawa ne?
Kamar yadda na yi maka bayani a baya, guda 29 ne amma zan bayyana maka wasu daga ciki. Misali ‘Al’adlu’ da ‘Almumitu’ da ‘Almuntakimu’ da ‘Almugni’ da ‘Annuru’ da ‘Alkhabitu’ da ‘Arrafidhu’ da ‘Almu’izzu’ da ‘Almuzillu’ har zuwa ‘Aljalilu’ da ‘Badi’u’ da ‘Almugni’ da A’rrashidu’ da ‘Albaaki’ da ‘Alhaadi’ da ‘Assaburu’ da wasu da dama, duk malamai sun ce ba su daga cikin sunayen Allah ingantattu. Kuma bincike ya nuna cewa akwai sunayen Allah masu inganci da ba a shigar da su cikin 99 ba, su ne ‘Jameelu’ da ‘Witrun.’ Manzon Allah yana cewa a cikin ingantattun hadisai: “Innallaha Witrun yuhibbul witara.” Ka ga ke nan Allah Witrun ne haka nan Jameelu. Manzon Allah ya ce: “Innallaha Jameelun yu hibbul jimaal.” Ka ga ke nan sunan Allah Jameelun.
To yanzu ke nan idan ka cire sunaye 29 daga cikin sunayen 99 nawa ke nan suka rage masu inganci?
Idan ka debe sunaye 29 daga cikin sunaye 99 ya zama saura sunaye 70 ke nan. Kuma za a nemo sunaye 29 ingantattu a sanya cikin 70 su cika sunaye 99. Ka ga wannan yana da muhimmanci idan muka yi la’akari da muhimmancin sunayen.
Ko za ka yi mana karin bayani kan malaman da suka yi wallafe-wallafe kan wannan batu?
Akwai malamai da yawa da suka yi magana a kan wannan al’amari. Malamai kamar su Ibn Taimiyya sun bayyana cewa hadisin Turmizi da ya ruwaito batun sunayen Allah 99 a wurin ruwaya ba shi da inganci. Shi kuwa Shaikh Nasiruddin Albani da ya zo wurin ‘Innallaha rafikun yuhibbul rifka,’ sai ya ce to ashe sunan Allah Rafiikun. Sannan sunan Al’aala wasu malamai sun ce shi ma yana daga cikin sunayen Allah ingantattu don Allah Ya ce: “Sabbi hisma rabbikal aala.” Da sunan ‘Arrabbu’ duk suna ne na Allah. Kuma malamai da dama sun ce ruwayar Buhari da take cewa Allah yana da sunaye 99 duk wanda ya kiyaye su zai shiga aljanna, ya inganta, sai shi kuma Tirmizi ya kara da lisssafa sunayen. To wannan karin da ya yi shi ne ba shi da inganci daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.
Tun lokacin da ka wallafa wannan littafi, shin ka samu wanda ya yi maka raddi ya ce abin da ka fada ba haka yake ba?
Akwai malamin da muka hadu cikin manyan malumammu amma ba sai na fadi sunansa ba, ya zo mani da littafi kan maganar da na yi na cewa ‘Zuljalali wal’ikram’ ba sunan Allah ba ne, siffar Allah ne, sai ya yi musu sai na ce masa idan ya ce haka ya zai yi da ‘kabiduttaubi shadidul ikabi? Ka ga da za a ce Allah shi ne ‘kabidut taubi wa gafiriz zambi.’ Wannan suna ne na Allah ba suna ne na siffa ba. Daga bisani sai ya gamsu da cewa ‘Zuljalali’ ba sunan Allah ba ne siffar Allah ne.
Wadanne matakai malam ya dauka wajen ganin cewa wannan littafi ya yadu cikin al’umma?
Gwargwado kamar yadda muka fada, wa’azi ne da na yi a Unguwar Festac da cewa mutane su rika kiyaye sunayen Allah da ba su da inganci da kuma masu inganci. Shi ne mutumin ya ce ya kamata na rubuta littafi karami don na fadakar da jama’a. To shi ya sa ka ga na wallafa wannan dan karamin littafin da bai wuce shafi 25 ba.
Idan mutum ya ji wannan wa’azi zai iya canja sunansa ko sunan dansa?
Ai ana iya canja suna kai saye ba tare da an sake yanka rago ba. Saboda haka idan mutum ya sanya wa dansa sunan Allah da ba shi da inganci kuma daga bisani ya ji cewa bai kamata ba, to zai iya canja sunan nan take ba tare da wata matsala ba. Don akwai wanda mahaifinsa ya sanya masa sunan ‘Gobara’ sai Sayyidina Umar ya ce masa ya canja sunan, sai ya ce shi ba zai canja ba saboda haka mahaifinsa ya sanya masa, sai ya ce masa idan ba ka canja ba, za ka je gida ka tarar gidanku ya kama da wuta. Da ya je kuwa sai ya tarar gidan ya kama da wuta. Saboda haka sanya suna marar kyau ko kuma wanda bai kamata ba ga da yana bin mutum, ma’anarsa ta yi tasiri.