‘Yadda na haifi kunkuru’

Wata matar aure mai suna Misis Kathrine Abari da ke zaune a kauyen Mutum daya a Agyaragu da ke yankin raya kasa na Jankwe, a Jihar Nasarawa,  ta bayyana yadda ta haifi wani kunkuru, kamar yadda ta bayyana wa  Wakilin Aminiya da ya ziyarci kauyen, a ganawar da suka yi da matar game da lamarin.Ta […]

‘Yadda na haifi kunkuru’

Kathrine da maigidantaWata matar aure mai suna Misis Kathrine Abari da ke zaune a kauyen Mutum daya a Agyaragu da ke yankin raya kasa na Jankwe, a Jihar Nasarawa,  ta bayyana yadda ta haifi wani kunkuru, kamar yadda ta bayyana wa  Wakilin Aminiya da ya ziyarci kauyen, a ganawar da suka yi da matar game da lamarin.
Ta bayyana cewa:  “Lamarin dai ya auku ne a lokacin da na soma nakuda, inda na yi ta jin motsi da ban taba ji ba a mahaifa ta. Da misalin karfe 11 zuwa 12 na rana, ranar Asabar din makon da ya gabata, wato 23 ga watan Nuwamban 2013, inda maigidana ya kaini asibitin Janar da ke Agyaragu. Da aka kaini asibitin ne sai wani likita bayan ya gwada ni, sai ya sanar da ni cewa kodayake ina dauke da juna biyu, amma babu jariri a mahaifa na. Da jin haka ne, ni da maigidana muka tuntubi ‘yan uwanmu don neman shawarwarinsu, inda dukkansu suka shawarcemu cewa mu gayyaci wani likitan gargajiya, don a cewarsu su ne kawai za su iya magance lamarin. Hakan yasa muka gayyaci likitan gargajiyan daga garin Daudu da ke makwabtaka da mu, maisuna Dokta Samuel  Kwaga, wanda ya ba mu wasu magunguna. Da na dawo gida na sha magungunan ne sai na haifi wani kunkuru.”
 Misis Katirin ta kara da cewa cikin ta dai da farko ya yi ta yin girma, amma daga baya sai ba ta ga komai ba.   “A lokacin da cikin ke kimanin watanni bakwai, mun tafi wani asibitiin inda aka yi min gwajin gani har hanji, sannan aka sanar damu cewa ina dauke da juna biyu, amma babu jariri a ciki. Daga nan sai muka garzaya zuwa wani asibiti mafi kusa da mu, inda aka ce da ni za a yi min fida, amma mahaifina bai amince da haka ba.Tun daga wannan lokaci ne na fara yawaita jin jiri sannan cikina yana min nauyi,” inji ta.
 Mahaifiyar kunkurun ta ci gaba da bayyana cewa ta auri maigidanta mai suna Mista Emmanuel Abari ne kimanin shekaru uku da suka gabata, sannan Allah ya albarkacesu da da mai suna Samuel Emmanuel kafin aukuwar wannan abin al’ajabi. Mijin matar, wato Mista Emmanuel Abari mai kimanin shekaru 29, wanda ya kammala karatunsa a kwalejin ilimi da ke Gindiri a Jihar Filato, ya bayyana aukuwar lamarin a matsayin abin al’ajabi da kuma ikon Allah, inda ya kara da cewa kodayake tunda matarsa ta dauki ciki ya gano cewa cikin ba na Allah da annabi ba ne, amma bai taba yin tunanin za ta haifi wani abu makamancin kunkuru ba.
Mista  Emmanuel Abari Ya yi amfani da wannan damar inda ya gode wa Ubangiji dangane da kare matarsa Misis Katirin Emmanuel daga fuskantar wata babbar matsala sakamarkon wannan abin al’ajabi da ta fuskanta.
Shi ma ana sa bangaren likitan gargajiya Dokta Samuel Kwaga, wanda ya gana da Aminiya game da lamarin, ta bakin mai fassararsa ya ce “wani magidanci mai suna Mista Emmanuel Abari ya zo da matarsa da ke fuskantar matsalar haifuwa, inda na hada musu wasu magungunan gargajiya kamar yadda na saba ba wadanda ke fuskantan irin matsalarta, na bayyana mata yadda za ta yi amfani da magungunan. Bayan tasha ne sai ta haifi kunkuru.
Likitan asibitin Janar dake Agyaragu, wanda ya gwada Misis Katharine Emmanuel kafin a garzaya da ita zuwa gun likitan gargajiya Dokta Sunday Mutsu, ya bayyana wa Aminiya cewa: “Da aka zo da matar nan bayan na gwada ta, sai na gano cewa ba mutum ba ne a cikinta.
“Kodayake ban gano ainihin abin da ke cikin ta ba a lokacin, na shawarcesu cewa su je asibitin kwararru na dalhatu Araf dake Lafiya don samun cikakkiyar kulawa. Sai suka cemin za su nemi shawara agun ‘yan uwansu game da haka. Daga baya ne na samu labari cewa bayan sun tuntubi wani sanannen likitan gargajiya dake kauyen Daudu maisuna dokta Samuel Kwaga ya ba su magani sai ta haifi kunkuru,” inji shi.
Likitan gargajiyar da ya bai wa matar magani, ya tuntubi danginta da mijinta sannan suka amince aka binne kunkurun, wanda a mace matar ta haife shi da misalin karfe bakwai da rabi na daren ranar Asabar bayan an gudanar da wasu adu’o’i da harkokin gargajiya na musamman.
Likita, Dokta D. Innas na Asibitin Dalhatu Araf da ke Lafiya wanda shi ne mataimakin babban likita a bangaren haihuwa a asibitin, inda ya ce “a gaskiya kodayake ba a kawo matar nan ba, amma ina so in tabbatar maka cewa ba shi yiwuwa a ce mace ta haifi kunkuru ko kuma wata dabba”.
Shi kuwa kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Nasarawa, DSP Malam Garba Muhammed, ya bayyana wa Aminiya cewa rundunar ba ta samu wannan labari  ba. Saboda haka ba ya da abin da zai iya cewa game da lamarin.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan