Yadda na haifi ’yan 3, biyu a manne da juna

Haihuwarta takwas duk mata, kuma sun zo duniya cikin koshin lafiya.

Yadda na haifi ’yan 3, biyu a manne da juna

Wata matar aure, Suwaiba Hassan, ta haifi yara ’yan uku mata zalla, amma biyu daga cikinsu sun zo ne jikin a hade da juna.

Suwaiba da ke zaune a kauyen Gangara da ke Karamar Hukumar Giwa a Jihar Kaduna, ta shaida wa Aminiya cewa tun da Allah Ya sa ta sami cikinsu, ba ta taba ko da shan magani ba da sunan ciwo ko laulayi.

Ta kara da cewa ko a lokacin da cikin ya kai wata bakwai ta yi hotonsa kuma da daya hoton ya nuna; Saboda haka ko da ta fara jin nakuda ba ta da wata fargaba, saboda wannan ita ce haihuwarta ta takwas.

Malama Suwaiba ta shaida wa Aminiya cewa bayan da ta haihu a daki ita kadai, shi ne ta ga halin da biyu daga cikin jariran da ta haifa, wadanda dukkansu mata ne, suke ci.

Nan take ta tura ’yarta mai shekara takwas ta kira iyayenta, suka zo aka dauke ta dare da jariran, suka dunguma zuwa babban asibitin garinsu, Gangara.

Mai jego, Malama Suwaiba, dauke da biyu daga cikin ’yan ukun da suka zo a manne da juna. (Hoto: Aliyu Babankarfi).

Daga nan ne aka tura su zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahamdu Bello, inda wakilinmu ya iske mai jegon tare da jariran nata.

Ta bayyana masa cewa jariran nata da ta haifa kwana 40 ke nan yanzu, suna cikin koshin lafiya. Sai dai ta bayyana cewa a halin yanzu madara suke sha, saboda nononta ba zai wadatar da su ba.

A yanzu haka jariran su uku suna dakin kula ta kananan yara na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika inda suka samun kulawar likitoci.

Wakilinmu ya yi kokarin zantawa da likitocin da ke kula da jariran, amma aka bayyana masa cewa suna tattauanwa a dakin taro game da halin da jariran suke ciki. Sai dai har zuwa lokacin da wakilin namu ya baro asibitin ba su fito ba daga tattaunawar ba.