Yadda na ji bayan faɗuwa Zaɓen 2015 — Jonathan
Jonathan ya ce, da jin sakamakon zaɓen, sai ya ji motsin zuciyarsa, kamar duk duniya ta juya masa baya.
Tsohon shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan ya yi ƙarin haske dangane da yadda ya ji bayan shan kaye a zaɓen shugaban ƙasa na 2015.
Ana iya tuna cewa dai Jonathan wanda ya yi takara a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, ya sha kaye a hannun Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC, wanda ya samu ƙuri’u 15,424,921, yayin da ya samu ƙuri’u 12,853,162.
Zaɓen dai ya kasance mai muhimmanci la’akari da zamansa abun misali na farko a tarihin Nijeriya da wani shugaba mai ci ya sha kaye a zaɓen da yake takara karo na biyu.
Da yake jawabi a ranar Juma’a a wajen ƙaddamar da laccar marigayi Raymond Dokpesi, Jonathan ya bayyana faɗuwa zaɓen a matsayin ɗaya daga cikin ƙalubalen da ya fuskanta a rayuwarsa ta siyasa.
Ya bayyana cewa, da jin sakamakon zaɓen, sai da bugun zuciyarsa ya ƙaru yana mai ganin tamkar duk duniya ta juya masa baya.
Tsohon shugaban ƙasar ya kuma bayyana rawar da marigayi Raymond Dokpesi, tsohon shugaban kamfanin Daar Communications ya taka kafin ya miƙa wa Buhari mulki.
Ya ce, “Ba abu ne ba mai sauki ka faɗi zaɓe a matsayin shugaban ƙasa. Za ku yi tunanin duk duniya tana gaba da kai. Amma sai Dokpesi ya gayyace ni kafin in miƙa mulki. Na tuna abin da ya ce da ni lokacin da na faɗi zaɓe.
“Akwai manyan ’yan Nijeriya da yawa (dattijan ƙasa) da suka yi magana. Bayan na saurari duk zancen, ya taya ni murnar gama mulki lafiya tare da kwaɗaitar da ni muhimmanci fifita zaman lafiya da kwanciyar hankali ba tare da na so kaina ba.”