Yadda na kafa gidan rediyona

Wani mai sana’ar gyaran rediyo a garin Abdullahi a yankin garin Dadin-Kowa a karamar Hukumar Yamaltu Deba a Jihar Gombe, mai suna Akilu Gyara Sa’a, ya kafa gidan rediyon  na kashin kansa. A lokacin da yake zantawa da Aminiya a Gombe ya shaida yadda aka yi ya fara sana’ar har ya samar da gidan rediyon. […]

Yadda na kafa gidan rediyona
Yadda na kafa gidan rediyona

Wani mai sana’ar gyaran rediyo a garin Abdullahi a yankin garin Dadin-Kowa a karamar Hukumar Yamaltu Deba a Jihar Gombe, mai suna Akilu Gyara Sa’a, ya kafa gidan rediyon  na kashin kansa. A lokacin da yake zantawa da Aminiya a Gombe ya shaida yadda aka yi ya fara sana’ar har ya samar da gidan rediyon. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Aminiya: Ko za mu ji takaitaccen tarihinka?
Sunana Akilu Gyara Sa’a, an haifeni a garin Abdullahi a nan na fara gyaran rediyo, sai dai kuma ni da kaina na koyi gyaran ba wani ba ne ya koya mini. Tun ina yaro nake daukar rediyon babana, ina gyarawa idan ta baci. San nan kuma ina yin hade-hade na wajen jona masa Ehriya, na kamo masa tashoshin rediyon Jihar Sakkwato da Katsina da Kano da rana yaji su ras, kamar tashar rediyon Gombe. Tun yana mun fada har ya daina da haka ina yi har na kware wajen gyaran rediyo.
Aminiya: Wadanne nasarori ka samu albarkacin wannan gyara?
Eh gaskiya da wannan gyara na rediyo Allah Ya daukaka sunana. Kuma na samu rufin asiri daidai gwargwado domin na mallaki kayan noma irin su shanu da garmar huda. Na yi aure har ina iya biyawa ‘ya’yana kudin makaranta. Wani abu kuma yanzu shi ne bullowar wayar nan ta salula, ita ma na iya gyara ta.
Aminiya: Ko kana da magaji a cikin ‘ya’yanka wato wanda ka koyawa wannan sana’a?
Akwai daya daga cikin ‘ya’yana muna wannan sana’a da shi. Kusan ma yanzu shi ne mai yin gyaran saboda ni ayyuka sun yi mun yawa. Kodayake, har gyaran Satilat yake.  A wannan sana’a babu abin da ba zai gyara maka idan ka kawo masa ba, saboda ni ba na gyaran Satilat amma shi yana yi kusan ma shi ne yake rike da shagon. Har ila yau, a cikin ’ya’yana akwai  wanda yake harkar kasuwanci daya kuma bakanike ne.
Aminiya: Ka kafa gidan rediyonka mai suna Gyara Sa’a ko za ka bayyana  mana yadda aka yi ka kafa shi?
Gaskiya sha’awa ce da gwazo da kuma na ci ya sa na bude wannan gidan rediyon ta hanyar mafarki kuma duk fadin garinmu da yankin Dadin-Kowa ana kama shi. Kuma ina gaya maka yanzu  haka idan da zan samu tallafi wannan rediyo za’a iya kamashi a duk fadin Jihar Gombe, sai dai saboda canjin rayuwa na irin yadda ake fito da rediyo masu zagin shugabanni ya sa na watsar har sai na samu goyon baya da kulawa daga wajen gwamnati.
Aminiya: Wane irin tallafi kake bukata daga wajen al’umma da kuma  gwamnatin?
Ina bukatar karatun kwamfuta wanda zai kara mini basira a zamanan ce da kuma samun wanda zai tsaya mini a matsayin ubangida da duk abin da ya taso zai tsaya mini.
Har ila yau, zan so a ce gwamnati ta taimaka mini da kayayyakin aiki na zamani da za su taimaka mun wajen dauko wannan hikimomin da na ajiye wanda zai ba ni dama na taimakawa kasa da al’umma baki daya.
Aminiya: Akwai wani gidan rediyo da ya taba nemanka don ka taimaka musu a bangaren na’urarsu?
Eh, akwai Gidan Rediyon Gombe ya taba turo wani ma’aikacinsu, mai suna Zubairu Musa Zambuk, inda ya same ni na kunna masa rediyon na ce ya yi tafiya iya tafiyarsa ya ji nisansa ya kusa kure garin Dadin-Kowa yana jin wannan tashar har nayi magana ya ji sannan ya dawo ya je ya gayawa Hukumar Gidan Rediyon, amma sai dai ba su yi komai ba a kai, sai dai hakan ya zama wata sila na shiga ta gidan rediyon ina gabatar da shirye-shirye.
Aminiya: A karshe me ye shawaranka ga matasa?
Ina mai bai wa matasa shawarar su nemi sana’a domin bana son ganin matasa suna zaman banza hakan ne ma ya sa a shagon nan nawa na koyawa matasa fiye da 15 wannan sana’a ta gyara, ba tare da samun tallafi daga wajen gwamnati ba.