Yadda na kafa talabijin din Nakowa a Legas – Sa’id Isa
Alhaji Sa’id Isa dan Sarkin Shuwa-Arab na Jihar Legas shi ne dan Arewa na farko da ya kafa gidan talabijin mai zaman kansa a Jihar Legas mai suna Nakowa Telebision. A tattaunawarsa da wakilinmu ya bayyana kalubale da matsalolin da ya fuskanta kafin ya bude gidan talabijin din, kuma ya bayyana yadda abin ya ba […]
Alhaji Sa’id Isa dan Sarkin Shuwa-Arab na Jihar Legas shi ne dan Arewa na farko da ya kafa gidan talabijin mai zaman kansa a Jihar Legas mai suna Nakowa Telebision. A tattaunawarsa da wakilinmu ya bayyana kalubale da matsalolin da ya fuskanta kafin ya bude gidan talabijin din, kuma ya bayyana yadda abin ya ba shi sha’awar shiga harkar jarida duk da ba fannin ya karanta ba:
Za mu so ka gabatar da kanka?
Sunana Sa’id Isa, dan Sarkin Shuwa-Arab na Jihar Legas. An haife ni a 1984 a karamar Hukumar Amawo-Odofin da ke nan Jihar Legas, a Legas na tashi, a nan na yi makaranta. Na fara makarantar firamare a makarantar Agidingbi da Sakandare ta Agidingbi Grammer, bayan na gama sakandare sai na tafi Maiduguri a Jihar Borno don na karanta fannin aikin lauya a Jami’ar Maiduguri, amma sai ban samu shiga makarantar ba. Na zauna har shekara guda domin na samu shiga Jami’ar Maiduguri amma ban samu shiga ba. Daga bisani sai na samu gurbin karatu a makarantar Koyon Aikin shari’a ta Jihar Borno wacce ake kira Borno State College of Legal Studies inda na karanta bangaren shari’a na tsawon shekara biyu na samu diploma. Daga nan sai na dawo Legas inda na ci gaba da neman karanta aikin lauya a jami’o’in da ke Legas amma ban samu ba. Duk da haka ban yi kasa a gwiwa ba, na ci gaba da nema, daga bisani sai na hakura.
Me ya sa ka dage sai ka karanta fannin lauya?
Dalili shi ne ni na dan kabilar Shuwa ne, a yankinmu da ke Maiduguri da wuya ka samu wanda ya yi karatun lauya. Shi ya sa na dage sai na zama lauya don na rika kwato ’yancin mutanenmu musamman wadanda ake danne wa hakki. To amma da na koma Legas a shekarar 2005 sai na shiga harkar kasuwanci inda na rika sayo raguna da shanu ina sayarwa a kasuwar kara. Ina matukar sha’awar wannan kasuwanci saboda kasuwancin da mahaifina yake yi ke nan, na tashi na ga yana gudanar da kasuwancin.
Yaya aka yi ka shiga harkar jarida?
Da ma ni mutum ne da nake sha’awar aikin jarida amma karatun aikin lauya shi ne farko. Lokacin da na nemi shiga Jami’ar Maiduguri da kuma jami’o’in nan Legas don na karanta lauya ban samu ba, sai na fara tunanin me zai hana na koma harkar jarida, tunda daga lauya aikin jarida nake sha’awa. Akwai shirin da nake saurara wanda Birila FM suke gudanarwa kuma ina sauraren wasu shirye-shirye da gidajen talabijin suke yi musamman ma gidan talabijin na MITb.
Kana nufin shirye-shiryen da kake saurara a gidajen rediyo da talabijin ne suka sa ka yi sha’awar shiga aikin jarida?
A’a ba su ba ne kawai. Ai na gaya maka cewa tun farko dama na kudurce cewa idan ban karanta lauya ba zan karanta aikin jarida. Wadannan su ne abubuwa guda biyu da nake sha’awa a raina. Yadda na ga fitaccen mai gabatar da shirye-shirye a gidan rediyon Bilira FM mai suna Cif Lanre yake yi sai ya ba ni sha’awa, sai na ce ni ma ai zan iya abin da yake yi, amma ba na so na yi shi a harshen Ingilishi, ina so na yi shi a wani harshe daban. Sai na yi tunanin na yi shi a harshen Hausa. Saboda haka sai na je gidajen talabijin da ke Legas, amma sai na tarar kudin da suke caji ya yi yawa. Sai na ce me zai hana ni ma na bude nawa gidan talabijin din na rika gudanar da shirye-shirye don amfanin jama’a. Da na dawo gida na yi bincike sai na gano cewa akwai gidan talabijin da ke yada shirye-shiryansa a kan tauraron dan Adam kuma suna gudanar da wani shiri mai suna YOTOMI da harshen Yarbanci. Sai ni na ce bari na fito da wani shiri da zai yi gogayya da shi a harshen Hausa. Saboda haka sai na kirkiro Nakowa Talabijin. A lokacin da na kammala tunanina, sai na tafi gidan talabijin din MCTb Cable da ke yada shirye-shiryensa ta tauraron dan Adam na yi wa shugaban gidan talabijin din bayanin abin da ke tafe da ni, sai ya gwada ni ya yi mini tambayoyi ya tabbatar na san abin da nake yi, sai ya ba ni damar na fara gudanar da shirye-shiryena a karkashin Nakowa Talabijin. Kuma Nakowa Talabijin shi ne gidan talabijin na farko da ke gudanar da shirye-shiryensa awa 24 a harshen Hausa a wannan lokaci. Na fara gudanar da shirye-shiryena a ranar 22 ga watan Mayu shekarar 2008. Shirye-shiryenmu sun hada da labarai da hira da mutane da kade-kade da raye-raye da wasannin gargajiya na Hausawa.
Me ya sa ka zabi gudanar da shirye-shiryenka a harshen Hausa duk da kai ba Bahaushe ba ne?
Dalilin da ya sa na zabi harshen Hausa shi ne, Hausa yare ne da ya fi karbuwa kuma ya fi yaduwa ba a Najeriya ba kawai har da sauran kasashen duniya. Ma’aikatana duk Hausawa ne da suka kware a harshen Hausa. Wadansu daga Arewa na samo su, wadansu kuma a nan Legas. Nakan samu labaraina daga Arewa da nan Legas ta hanyoyi da dama. Daga bisani sai aka dakatar mana da shirye-shiryenmu. Amma dai zan iya cewa ni ne dan Arewa na farko da na bude gidan talabijin na Hausa a Legas.
Me ya sa kamfanin MCTb ya dakatar da shirye-shiryenka?
Dalili shi ne suna son su kara shiryawa ne su sake wa kamfanin nasu tsari ta yadda zai yi gogayya da sauran kamfanonin talabijin na tauraron dan Adam.
Kafin ka kafa talabijin din Nakowa, ka samu horo ne na musamman?
Ban taba samun wani horo ba a aikin jarida. Na shiga ne da ka kuma Allah Ya ba ni sa’a har na kai inda na kai. Amma sirrina shi ne ina bibiyar yadda fitattu kuma kwararrun ’yan jarida suke gudanar da shirye-shiryensu kuma lokacin da nake makarantar koyon aikin shari’a ta Maiduguri ni ne nake karanta labarai a gidan rediyo na makarantar.
Lokacin da ka fara kafa gidan talabijin na Nakowa, yaya karbuwarsa yake ga jama’a?
Gaskiya mun samu karbuwa sosai a Jihar Legas da sauran wurare da yawa. Akwai mutanen da suka rika kirana daga kasashen wajen suna yaba mana. Kai har mun fara samun talla daga waje. Don akwai wata yarinya da za a yi aurenta ta ce mana tana so mu nuna shagalin bikinta a Nakowa Talabijin, na tambaye ta me ya sa take so a Nakowa, sai ta ce saboda muna yada shirye-shiryenmu a harshen Hausa kuma ita Bahaushiya ce.