‘Yadda na kashe yarinya na sayar da sassan jikinta Naira 8,500’
Wani mutum da ya ƙware a kisan mutane yana cire sassan jikinsu yana sayar wa matsafa, ya shaida cewa Naira dubu 8, 500 aka ba shi ladan kisan wata yarinya ’yar shekara 17; wacce ya yanke mata hanji, yatsu da zuciya da al’aurarta. Mutumin ɗan kimanin shekara 35 mai suna Yewunu Tanlaju ya shaida haka […]
Wani mutum da ya ƙware a kisan mutane yana cire sassan jikinsu yana sayar wa matsafa, ya shaida cewa Naira dubu 8, 500 aka ba shi ladan kisan wata yarinya ’yar shekara 17; wacce ya yanke mata hanji, yatsu da zuciya da al’aurarta.
Mutumin ɗan kimanin shekara 35 mai suna Yewunu Tanlaju ya shaida haka ne a ranar Litinin da ta gabata, a lokacin da rundunar ’yan sanda a Jihar Ogun ta gabatar da shi tare da sauran waɗanda ake zargi ga ’yan jarida, a hedikwatarta da ke Eleweron, Abekuta.
Ya ce yarinyar da ya kashe, ya same ta ne tana tallar fanke, inda ya yaudare ta da sunan zai saya. “Na yanka ta, na ciri sassan jikinta da mai maganin ya buƙata, na kai masa. Na jefa ragowar gangar jikin a rijiya, inda ya biya ni Naira dubu 8500, domin tun da farko ba mu yi yarjejeniyar adadin kuɗin da zai biya ni ba,” inji shi.
Ya ƙara da cewa a baya ma ya halaka wata mace ’yar kimanin shekara 40, a lokacin da matsafin ya buƙaci ya kawo masa sassan jikin mutum. Ya ce a wanccan lokacin Naira duba 10 ya biya shi ladan aikin kuma ya yi aikin cikin nasara ba tare da asirinsu ya tonu ba.
A nasa ɓangaren, matsafin ya musanta cewa shi ne ya ba shi aikin kisan yarinyar. Ya ce ya zo masa ne da sassan jikinta da nufin ya yi masa maganin kuɗi.
Da yake zantawa da ’yan jarida, mahaifin yarinyar, Jimoh Gusinu ya nemi da a tabbatar an hukuta waɗanda suka halaka masa ’yarsa. Ya ce muddin aka sake su zai ɗau doka a hannunsa.
Kwamishinan ’yan sanda a Jihar Ogun, Ahmad Iliyasu ya shida wa Aminiya cewa mahaifin yarinyar ne ya shaida masu ɓacewar ’yar tasa bayan ta fita tallar fanke. “Nan take muka tura mutanenmu da ke aiki a yankin Ogijo, inda suka yi haɗin gwiwa da ’yan sintirin yankin da sauran jama’ar gari. Nan muka kame mai maganin gargajiyar mai suna Asamo wanda ya haɗa baki da ƙarin nutum biyu da suka kashe yarinyar. Mun sami sassan jikinta a wajen mai maganin, yayin da muka fito da gangar jiki daga rijiyar da suka jefa, aka kai ta babban asibitin Ilaro domin faɗaɗa bincike. Za mu tabbatar an hukunta masu laifin kamar yadda dokar ƙasa ta tanada,” inji shi.