Yadda na kera motata – Auwal Muhammad

Auwalu Muhammad yana daga cikin matasan da suke da fasaha a kasar nan, inda a kwanakin baya ya kera wata mota mai ban sha’awa. Aminiya ta tattauna da shi kan matsalolin da ya fuskanta kafin ya kera motar. Ya tabo batutuwa masu dama dangane da kayayyakin da ya yi amfani da su wajen kera ta, […]

Yadda na kera motata – Auwal Muhammad

Auwalu Muhammad yana daga cikin matasan da suke da fasaha a kasar nan, inda a kwanakin baya ya kera wata mota mai ban sha’awa. Aminiya ta tattauna da shi kan matsalolin da ya fuskanta kafin ya kera motar. Ya tabo batutuwa masu dama dangane da kayayyakin da ya yi amfani da su wajen kera ta, sannan ya bayyana burinsa na zama fitaccen mai zayyanar mota a duniya. Ga yadda hirar ta kasance:

 

 Auwal a cikin motar da ya qeraAminiya: Za mu fara da tarihinka?
Sunana Muhammad Auwal, an haife ni a garin Jama’are da ke Jihar Bauchi. Asalin gidanmu makera ne, domin tun ina dan shekara 10 na fara kirkirar abubuwa daban-daban. Na fara ne da kera kekuna daban-daban, ga shi yau har Allah Ya nufe ni da kera motar shiga.

Aminiya: Mene ne abin da ya ja hankalinka har ka yi tunanin kera mota?
Babban abin da ya ja hankalina wajen ganin na kera motar shiga a rayuwata shi ne, a kullum burina bai wuce in zamo daya daga cikin irin mutanen da al’umma suke amfana daga fasahar da Allah Ya ba su ba.

Aminiya; Tsawon wani lokaci ka kwashe kafin ka kera wannan motar?
Na dauki tsawon wata 5 kafin in fara hawanta, sabodanya ba ita kadai na sanya a gabana ba, amma da ita kadai na sa a gaba, kuma a ce akwai isassun kayan aiki, a mako biyu zan iya kammala aikinta.

Aminiya: Da wadanne kayayyaki ka hada wannan mota abar burgewa?
Kayayyakin da na hada motar da su sun hada da karfen Skuare pipe da tayoyin bubur, sannan injin ma na babur ne Honda, sauran abubuwan kuma yawancinsu da kaina na yi su, kamar irinsu sitiyari da bamfa da sauransu.

Aminiya:Wannan motar takan ci kamar litar mai nawa?
Lita 10 tankinta yake dauka.

Aminiya: Batun mitar da ke nuna maleji fa? Ta yaya kake gane zangon gudunka?
Maleji yana aiki sosai. Nakan yi tafiya da ita tsawon kilomita 45, sai dai wani lokaci idan ina gudu nakan ji kamar za ta tashi sama, saboda rashin nauyinta, amma hikimar yinta hakan yana da alaka da sama wa injin saukin janta.

Aminiya: Yanzu ga shi ka kera mota za a iya cewa burinka ya cika ke nan?
Babban burina a nan gaba shi ne in zama kwararren mai zayyana mota a duniya, kamar Jelani Aliyu.

Aminiya: Komai mutum ya sa a gaba a yawanci lokuta yana fuskantar kalubale, ko ka fuskanci wadansu matsaloli a lokacin da kake aikin hada wannan motar?
Na fuskanci matsaloli da dama, daga ciki a lokacin da na rika kai kukana wurin wadansu daidaikun mutane don su taimaka mini, don kada aikin ya tsaya, amma sam na rasa mai tallafa min, har sai da ta kai ga na sayar da wadansu abubuwana kafin na kammala aikin hada motar.

Aminiya: Yaya yanayin yadda motar take shan mai?
Motar tana shan mai daidai da yadda babur Jincheng (roba-roba) yake shan mai, saboda da kafiretonsa na yi amfani.

AminiyaNa ga motar taka babu wefa, hakan na nufi idan ana ruwa ba za a iya tuka motar ba ke nan?
Rashin wefa ba matsala ba ce a motar, domin gilashinta ko da ruwa ya hau ba zai hana ka kallo ba.

Aminiya: Ga bangaren batirin motar fa?
Na yi amfani da karamin batiri mai girman 50 megawat, sannan karfinsa na sanya fitilun motar su haska mini hanya ta yadda zan iya kallo komai dare. Sannan karfin kafafunta sun fi na babur, domin na inganta su sosai wajen yi musu madauki na gaske.

Aminiya: Wane kira kake da shi ga gwamnati kan ire-irenku da suke da fasahar kera abubuwa?
Yana da kyau gwamnati ta rika kula da wadannan al’amura na kimiyya da fasaha, sannan ta rika tallafawa da kayan aiki ko kudi, ko kuma uwa uba, a yi wa mutum hanyar fita waje domin ya koyo anihin yadda aikin yake a ilimance, to ina ganin ta haka ne Najeriya za ta samu ci gaba da wadatuwar kayan more rayuwa, kamar irin su jirgi da mota da babur da da sauransu, ko da kasashen waje su ma da haka suka ci gaba, don haka kirana ga gwamnati shi ne, ta taimaka wa kasar nan wajen tallafa wa masu baiwa ta kirkira.