Yadda na kirkiro maganin ciwon siga – Dokta Ibrahim

Dokta Muhammad Auwal Ibrahim malami a Tsangayar Kimiyyar Hada Magunguna da ke Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya  ya samu nasarar kirkiro maganin ciwon siga na gargajiya daga ganyyayaki da kuma tsirrai. Ya samu wannan nasarar ne a binciken da ya gudanar don samun digiri na uku a Jami’ar Kwazulu Natal da ke kasar Afirka ta […]

Yadda na kirkiro maganin ciwon siga – Dokta Ibrahim
Yadda na kirkiro maganin ciwon siga – Dokta Ibrahim

Dokta Muhammad Auwal Ibrahim malami a Tsangayar Kimiyyar Hada Magunguna da ke Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya  ya samu nasarar kirkiro maganin ciwon siga na gargajiya daga ganyyayaki da kuma tsirrai. Ya samu wannan nasarar ne a binciken da ya gudanar don samun digiri na uku a Jami’ar Kwazulu Natal da ke kasar Afirka ta Kudu. Malamin wanda dan asalin Jihar Kano ne, ya bayyana wa Aminiya gwagwarmayar da ya yi kafin ya kirkiro maganin.

Za mu fara da tarihinka?
Sunana Muhammadu Auwal Ibrahim, ni dan karamar Hukumar Dala da ke Jihar Kano ne. Na yi karatun firamare a Kano, na kammala sakandare a Sharada a Kano  shekarar 1998, a shekarar ni ne dalibin da ya fi samun kyakkyawan sakamako, daga nan sai aka ba ni takardar zama dalibin Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a bangaren kimiyyar hada magunguna, inda nan ma na kammala da kyakkyawan sakamako, sai aka dauke ni aiki a jami’ar saboda kyakkyawan sakamakon da na samu, daga nan na ci gaba da karatun digiri na biyu a jami’ar daga shekarar 2005 zuwa 2008. Bayan na kammala a shekarar 2010 sai na samu gurbin karo karatuna a jami’ar Kwazulu Natal da ke kasar Afirka ta Kudu.
Aminiya: Me ya ja hankalinka har ka gudanar bincike don gano maganin ciwon siga?
Dokta Ibrahim: Kafin in ce wani abu, da farko dai ina yi wa Allah godiya da Ya yi min jagoranci, kuma Ya ba ni basira da hikima a kan wannan bincike da na gudanar. Ina kuma yi wa Mataimakin Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello Farfesa Abdullahi Mustapha da Jami’ar Ahmadu Bello godiya bisa bisa gudunmuwar da suka ba ni wajen nasarar da na samu na kammala binciken da na yi a kan wadannan tsirran da ke maganin ciwon siga wato (Diabetics).
Abin da ya ja hankalina har na kirkiro wannan maganin kuwa shi ne, kasancewar masu fama da ciwon siga a Najeriya yawansu ya kai kashi uku da digo biyu cikin kashi biyar na masu fama da ciwon siga a kasashenmu na Afrika. Hakan ya kara ban i karfin gwiwar yin bincike don samo magungunan da za su taimaka wa masu fama da ciwon siga.  
Na yi bincike ne a kan abin da zai rage karfin ciwon ko kuma ya kawar da shi gaba daya. Na yi nazari mai zurfi inda na rubuta kasidu guda hudu, sannan malamai uku suka duba su, biyu daga ciki malaman da suka duba kasidun ba su yi mini gyara ba, na ukun ne ya ce in yi gyare-gyare. Dukkansu sun yaba da wannan binciken, kuma sun amince da shi, sannan suka ce babu wanda ya yi binciken da na yi a duniya, na yi binciken kwa-kwaf.
To cikin ikon Allah ya sa na gano wasu magunguna wadanda za su iya magance ciwon siga, wato magungunan na da damar da za su iya kawo sauki ga masu fama da ciwon siga, akwai sinadaran da nan gaba za a iya amfani da su wajen magance ciwon siga.
Aminiya: Yaya wadannan sinadaran suke?
Dokta Ibrahim: Ba zan bayyana su duniya ta ji ba, dalilin da ya sa ba zan bayyana su ba kuwa shi ne, akwai masana kimiyya wadanda idan sun ji na fade su, to yanzu za su dauki wannan fasaha tawa su yi amfani da ita, sannan su rika cewa su ne suka kirkiro ta, amma sinadaran akwai su a kusan ko’ina musamman a kasata Najeriya, kuma masu magananin gargajiya za su dauke su su yi kokarin hada su don samar da maganin, sannan su shigar da shi kasuwa ba tare da an inganta shi ba. Kuma ni ne mutum na farko a duniya wanda ya yi bincike a kan wannan tsirran da sinadaran wadanda za su kawar da ciwon siga gaba daya
Aminiya: Kai ne mutum na farko da ka fara kirkiro maganin ciwon siga, sannan ka yi batun wadansu sinadarai da nan gaba za su taimaka wajen kawar da ciwon siga gaba daya, jama’a za su so su ji karin bayani a kan wadannan sinadaran?
Dokta Ibrahim: kwarai ni ne mutun na farko da na kirkiro wannan sinadaran ta wajen bincike, to abin da zan fada wa mutane shi ne, a da za ka ga babu ko mutum daya mai ciwon siga a dangi, amma a yanzu sai ka ga a dangi daya sai ka samu mutane da yawa masu fama da ciwon siga, abin ma har ya fara wuce inda ba a zato, kowane gida sai ka samu mai ciwon siga, kuma wannan ciwo in an kamu da shi yau da gobe sai dai a dinga tarairaiyarsa har mutum ya mutu, amma ba a warkewa gaba daya, saboda haka ne na yi bincike har na gano hanyoyin da za a samu saukin wannan ciwon.
Idan ka samu mai wannan ciwon, kuma kuka yi hira zai fada maka ya fuskanci matsaloli masu yawa dangane da magunguna iri-iri da ya sha don ya rage karfin ciwon, magunguna ne wadanda suke da matsaloli, wadanda sai mai ciwon kawai yake fama da shi, wani zai fada maka cewar idan ya sha maganin zai dinga tusa, wani kuma zai barke da zawo, to saboda wadannan matsalolin ne sai ka ga marar lafiya yana gudun amfani da irin wadannan magunguna da ake amfani da su, saboda haka masana kimiyya suke matsawa a kan bincike a kullum, saboda su gano sababbin magungunan da ba su da wadannan matsaloli, yadda masu fama da ciwon za su iya amfani da su ba tare da sun samu wata matsala ba, kuma za su yi musu maganin da ake bukata.
Don haka wadannan tsirran da Allah Ya sa na gano duk wani mai dauke da wannan ciwo zai iya amfani da su cikin sauki ba tare da ya samu matsala ba.
Aminiya: Duk da cewa Najeriya tana daya daga cikin kasashen da mutane ke fama da ciwon siga ko wane tabbaci za ka ba masu fama da wannan ciwo na cewa nan gaba kadan za a magance wannan ciwo?
Dakta Ibrahim: Ai tabbas daga wannan bincike da na yi ya nuna mana cewar muna da tsirrai a wannan kasar tamu wadanda idan aka tsaya aka inganta su kuma aka yi amfani da su yadda suka kamata za a samu yadda ake so, kuma ba zan ce masu maganin gargajiya su dauka su kai kasuwa ba tare da sanin yadda za a yi amfani da su ba, kuma ba wai ingantar da wannan magungunan nake yi ba, abin da nake cewa shi ne, bincike kadai zai iya tabbatar da cewa wadannan tsirran za su iya maganin ciwon siga, kada a yi tsammani cewa masu maganin gargajiya za su iya bayar da su ba daidai ba ne, dole ne sai an yi bincike kafin a tabbatar da ingancinsu, sannan a kawo su kasuwa.
Aminiya: Ga shi ka kirkiro abin da zai amfani al’umma, wani shiri kake da shi ganin cewar ka karantar da dalibanka irin wannan fasahar?
Dakta Ibrahim: Babban burina shi ne idan an samu dalibai masu kwazo za mu sa su hanya, mu ga cewa sun yi amfani da damar da suka samu wajen inganta bincike don su kirkiro abin da zai taimaki al’umma, kuma za mu ba su duk irin gudunmawar da ta dace mu ba su, domin kasa ta ci gaba.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno