‘Yadda na kubuta daga hadarin da ya kashe mutum uku’

Wani mai suna Muhammadu Surajo da ke jinyar karaya biyu da ya samu sakamakon wani hadari da ya rutsa da shi a Jihar Legas, a makon da ya gabata, ya bayyana yadda ya kubuta daga hadarin, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum uku tare da raunata wasu da dama.Malam Surajo, wanda ke zaune a unguwar […]

‘Yadda na kubuta daga hadarin da ya kashe mutum uku’
‘Yadda na kubuta daga hadarin da ya kashe mutum uku’

Wani mai suna Muhammadu Surajo da ke jinyar karaya biyu da ya samu sakamakon wani hadari da ya rutsa da shi a Jihar Legas, a makon da ya gabata, ya bayyana yadda ya kubuta daga hadarin, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum uku tare da raunata wasu da dama.
Malam Surajo, wanda ke zaune a unguwar Markaz, a karamar Hukumar Agege ya bayyana wa Aminiya cewa, “Lamarin ya faru lokacin da wani likita ya kira ni domin mu tattauna wata matsala. Daga Agege, mun kai daidai titin Ilesi, sai muka tarar da cunkoson ababen hawa, sai na sauka na tsallaka na shiga cikin Ikeja da kafa. Ina cikin tafiya sai kawai na ga wata motar ’yan sanda na bin wani mai babur, suna cewa za su harbe shi idan bai tsaya ba. Sai suka nufo ni, wajen kokarin gudu, sai ga wata motar daukar nama tana kokarin kauce wa motar ’yan sandan, garin haka, sai ya yi karo da wata babbar mota da ke dauke da kwantena, sai kawai kwantenar ta fado wa motar naman ta danne ta. Shi kuma mai babur, garin gudu ya je ya shiga karkashin babbar motar; ni kuwa, ban san yadda aka yi ba, sai kawai gani na yi mutane sun taru suna yi min sannu. Sai aka kai ni asibitin gwamnati na Ikeja, inda aka dauki hotona daga bisani suka tabbatar da na sami karaya biyu a hakarkarina. Suka ce mana bayan mako daya mu dawo, sai muka yanke shawarar kiran mai dorin gargajiya, ya dora ni a gida”.
Ya bayyana cewa lokacin da ya farfado wata mata ta gaya masa cewa ya gode wa Allah domin ta ga gawarwakin mutum uku a karkashin motar.
Ya kara dacewa hadarin shi ne na farko da ya taba faruwa da shi a tsawon shekaru fiye da 50 da ya yi a duniya.
Wani kwamanda na hukumar lura da zirga-zirgar ababen hawa na Jihar Legas, Mista Adekunle Ajibade ya bayyana cewa rashin birkin tirelar ne ya janyo hadarin.