…Yadda na kubuta daga harin Boko Haram – Sarkin Askira
Mai martaba Sarkin Askira da ke Jihar Borno Alhaji Mai Abdullahi Ibn Muhammadu, wanda wakili ne a wurin taron kasa ya bayyana yadda samu kansa a hannun Boko Haram a lokacin da suka kai musu hari a makon jiya. Sarkin tare da sarakunan Gwoza da Uba an kai musu hari ne a ranar Juma’ar da ta […]
Mai martaba Sarkin Askira da ke Jihar Borno Alhaji Mai Abdullahi Ibn Muhammadu, wanda wakili ne a wurin taron kasa ya bayyana yadda samu kansa a hannun Boko Haram a lokacin da suka kai musu hari a makon jiya.
Sarkin tare da sarakunan Gwoza da Uba an kai musu hari ne a ranar Juma’ar da ta gabata a kan hanyarsu ta zuwa Gombe don halartar jana’izar marigayi Sarkin Gombe Alhaji Shehu Abubakar lokacin da aka kai musu hari.
Sarkin na Askira ya bayyana wa zauren taron cewa: “Kamar yadda wakilan suke sane, mu sarakuna uku daga Jihar Borno, ni Sarkin Askira da marigayi Sarkin Gwoza da Sarkin Uba mun kama hanyar zuwa Gombe, kuma niyyarmu mu tsaya a Biu don mu tafi tare da Sarkin Biu da na Shani. Jim kadan da barin Garkida da ke iyakar jihohin Adamawa da Borno, sai aka yi mana kwanton bauna. Da za mu tafi saboda mun dade ba mu ga juna na tsawon lokaci ba, sai muka yanke shawarar shiga mota daya, sauran motocin su biyo mu.”
Ya ce, “Mu ukun muna cikin wata Jeep, kwatsam sai muka ji an bude wa motarmu wuta ta ko’ina. Duka muna cikin motar, kimanin mutum 40 (’yan Boko Haram) suka rika harbi a lokaci guda. Kuma abin takaici saboda karfin harbe-harben, sai motar ta mutu. Direban ya yi kokarin tayar da ita amma ta ki, ganin halin da muke ciki, zabin da ya rage mana mu fice daga motar.”
Ya ci gaba da cewa: “Na fice daga motar suna ta harbi, Allah Ya yi ikonSa na fita, sauran motocin suka koma da baya, yadda aka yin a fada cikin wata mota ban sani ba; rabin jikina yana waje, rabi na ciki. Ta haka muka kokarta muka koma da baya, muka tsira.”
Sai dai ya ce, Sarkin Gwoza bai samu nasarar kubuta ba.