‘Yadda na kubuta daga kasancewa cikin masu tada bam a Maiduguri’
Wata yarinya da ta rako ’yan uwanta mata ’yan kunar bakin wake da ta sha da kyar mai suna Fatima Baba Gafciya da ba ta wuce shekara 20 ba, ta ce ta kubuta ne ba tare da sanin ’yan Boko Haram din ba. Fatima Baba Gafciya, ta cewa, “Tun farko na tafi Monguno a wani […]
Wata yarinya da ta rako ’yan uwanta mata ’yan kunar bakin wake da ta sha da kyar mai suna Fatima Baba Gafciya da ba ta wuce shekara 20 ba, ta ce ta kubuta ne ba tare da sanin ’yan Boko Haram din ba.
Fatima Baba Gafciya, ta cewa, “Tun farko na tafi Monguno a wani lokaci can a baya sai na ci karo da wadansu wai Boko Haram sai suka sace ni suka kai ni daji. To na tarar da mata biyar a wurin inda suka hada mu kuma suke kawo mana abinci, matansu su kawo mana abinci su kuma mazan su kawo mana ruwa, amma ba su taba yarda cewa mu san inda suke ba. Akalla na kwashe shekara daya a wajensu, shi ke nan sai kwanan nan suka kwaso mu a mota da nufin za su kawo mu garin Maiduguri don mu je mu sa bama-bamai a wasu wurare, shi ke nan sai ni kuma na yi tsalle na fita daga motar na fada daji ina ta gudu har na samu wani kauye, amma mutanen kauyen suka ce za su kashe ni, da suka caje ni ba su ga komai a jikina ba ne sai suka bar ni na karaso cikin gari ta wannan unguwa. Ba domin na tsere ba da ni ma ina cikin wadanda za su tayar da wadannan bama-bamai.”
Ta ce, ’yan Boko Haram din sun bar wadancan mata biyar da suke tar da da su, to amma sai kuma suka dauke ta suka hada ta da wasu mata biyar suka sa su a mota zuwa Maiduguri kuma kafin a zo ne sai ta dirko daga motar ta gudu tun kafin a kai ga sanya mata bam din a jiki balle su isa wurin da za su tayar da su.
“Na yi kokarin tsira da raina ne shi ne har kuka gan ni a nan, amma a can kuma in da nake tsare ba su taba ba ni wani abu na ci ba sai dai tuwo da miyan kubewa ko kuka. Wallahi sun ajiye mu ne a daji wanda ni ban san wurin ba, ba zan iya cewa ga wurin ba. Iyayena suna nan a Bulunkutu Tsallake, na taba yin aure na haifi ’ya daya, amma a can ba mu yi aure da su ba, kuma ba su koya mana wani abu ba, sannan ba su
taba ba ni wani abu na ci ba, har tsawon shekara. To amma a wannan lokacin sai suka dauko ni da nufin in je in sa bam a wani wuri shi ke nan sai na gudu,” inji ta.
A ranar Lahadi da Litinin ne wasu tagwayen bama-bamai suka tashi a Unguwar Jiddari Polo da ke garin Maiduguri, wadanda suka yi sanadiyyar rasa rayukan sama da mutum 30 tare da jikkata wasu da dama, kuma a daidai lokacin ne wasu bama-baman suka tashi a Jihar Adamawa inda jimillar wadanda suka rasu a jihohin biyu suka kai mutum 70.