Yadda na kulla abota da mutuwa – Fursuna Moshood

Aminiya: Za mu so ka gabatar da kanka? Ni dai an haife ni a garin Ibadan da ke jihar Oyo yankin Kudu Maso Yammacin Najeriya tun kimanin shekaru 62 da suka gabata. Na yi makarantar firamare da sakandire. Daga bisani sai na shiga aikin soja. Na fara aikin soja tun daga mukamin kurtu har zuwa […]

Yadda na kulla abota da mutuwa – Fursuna Moshood
Yadda na kulla abota da mutuwa – Fursuna Moshood

Aminiya: Za mu so ka gabatar da kanka?

Ni dai an haife ni a garin Ibadan da ke jihar Oyo yankin Kudu Maso Yammacin Najeriya tun kimanin shekaru 62 da suka gabata. Na yi makarantar firamare da sakandire. Daga bisani sai na shiga aikin soja. Na fara aikin soja tun daga mukamin kurtu har zuwa mukamin kofur. Na yi aiki a jihar Oyo daga bisani aka dawo da ni Legas. Na yi aure. Ina da mata daya da ’ya’ya shida. A yanzu ’yayana wadansu sun kammala makarantun gaba da sakandire.
Aminiya: Wane laifi ka yi har ta kai an daure ka a kurkuku?
To ni dai laifin da aka ce na yi shi ne wai fashi da makami. Kuma wadansu abokanaina ne suka jaza mani. Ka san idan ka yi alaka da abokainan banza to babu shakka kana cikin hadari. To ni dai ina cikin aikin soja aka zo aka kama ni cewa wai mun yi fashi da makami. Aka kai ni kotu, aka rika tafka shari’a. Daga bisani a shekarar 1992 aka yanke mani hukuncin kisa.
Aminiya: To yaya aka yi ka kasance a nan sashen a maimakon wancen sashe da ake kulle wadanda za a kashe?
Haka ne. Abin da ya faru shi ne, bayan da aka yanke mani hukuncin kisa, daga bisani sai aka mayar da shi daurin raid a rai a kurkuku. Saboda haka ina sa ran wata rana in dai ba Allah ba ne Ya dauki raina ba zan fita daga wannan wuri in ci gaba da rayuwa kamar yadda kowa yake yi. Ni musulmi ne kuma na yi imani da Allah cewa wata rana Allah zai fitar da ni daga wannan wuri.
Aminiya: Ya rayuwa ta kasance maka a nan?
To rayuwa a nan ni babu abin da zan ce sai dai na gode wa Allah da Ya bar ni da raina don da tuni an kashe ni, an manta da ni kwakwata, amma sai Allah Ya tsawaita rayuwa ta har yanzu ina nan. Akwai abokanaina da na sani da muka zauna da su a daki daya da aka kashe su. Da yawansu na riga su zuwa amma sai ya zamana an kashe su amma ni Allah Ya kare ni.
Aminiya: Ka ce akwai wadanda ka zauna da su a daki daya da aka kashe su, yaya ka rika ji a wannan lokacin da ake kiransu daya-bayan-daya ana kashewa?
Gaskiya na shiga tashin hankali don a kullum sai an zo an kira daya daga cikinmu, an tafi da shi an kashe shi. Akwai lokacin da muke daki daya mu takwas aka rika zuwa kullum ana kiran daya bayan daya sai da duk aka kashe su, sai ya rage sai ni kadai a dakin, ranar ban yi barci ba saboda tunanin gobe za a kashe ni.
Da gari ya waye na rika jira, ina ta kullen-kullen abin da zai faru da ni da kuma yadda kisan zai kasance, sai kawai na ga har dare ya yi amma ba a kira ni ba. Aka wayi gari, aka sake kwana ban ga an zo an kira sunana ba. Sai na rika yin mamaki, na rika cewa ko manta da ni aka yi?. Haka Allah Ya kare ni har na bar ginin babu abin da ya faru da ni. Aka dawo da ni nan ginin.
Aminiya: Me ya sa aka mayar da hukuncin kisan da aka yanke maka zuwa daurin raid a rai a kurkuku?
Ka san na gaya maka cewa an tafka shari’a a kotu kan zargin da ake yi mani. A lokacin da aka yanke mani hukuncin kisa ban karaya ba, na ci gaba da bin kadina, inda na daukaka kara kuma da taimakon Allah aka mayar da kisan ya zama daurin raid a rai a kurkuku. Ka ga wannan wata babbar nasara ce, don ina sa ran wata rana zan fita. Ba kowa ne yake samun wannan nasara ba sai mai tsananin rabo. Har yanzu ban debe tsammani ba da yardar Allah zan fita in ci gaba da rayuwa kamar kowa cikin ’yanci da walwala.
Aminiya: Me ya ba ka sha’awa ka shiga karatu har ka kammala digirinka na farko ga shi kuma a yanzu kana yin digiri na biyu?
Dalili shi ne lokacin da aka yanke mani hukunci ban karaya ba, sai na rika tunanin abin da zan yi a cikin kurkuku sai na ga babu abin da ya fi ilimi muhimmanci. Da ma na yi sakandire amma sakamakona bai yi kyau ba. Sai na sake zana jarabawar GCE a shekarar 2007, na yi nasara, jarabawa ta yi kyau.
Daga bisani sai na shiga jami’ar karatu daga gida da ake kira ‘Open Unibersity’ da ke jihar Legas, inda na samu gurbin karatun digirin farko a fannin nazarin zaman lafiya da sasanta rikici, wanda a turanci ake kira: ‘Peace Study and Conflict Resolution’. Na kammala a shekarar 2015. Na rubuta littafin kammala digiri na farko a kan ‘Amfani da doka a tsarin siyasar Najeriya’ wato ‘Application for the Rule of Law In Nigerian Political System’.
A yanzu na samu damar ci gaba da digiri dina na biyu a ita wannan jami’ar karatu daga gida ta Legas, a dai shi fannin ‘Zaman lafiya da sasanta rikici’.Kuma idan na kammala ina so in ci gaba da digirin digirgir dina a wannan fannin. Sannan kuma ina so idan na samu dama in karanta fannin Arabiya don in kara ilimina na Musulunci.
Aminiya: Ka ce kana sa ran wata rana za a fitar da kai daga kurkuku, idan ka samu damar fita, wace sana’a za ka ci gaba da yi a rayuwarka?
Na fi sha’awar shiga harkar samar da zaman lafiya da sasanta rikici a Najeriya. Shi ya sa nake ta kokarin zama kwararre a fannin. Ina so ya zama ina yi wa gwamnati ko wata ma’aikata mai zaman kanta bincike kan yadda za a bullo wa rikice-rikice da tashin hankalin da ake fama da shi a Najeriya baki daya.
Aminiya: Wace shawara za ka bai wa jama’a da ba su san zaman kurkuku ba?
Shawarar da zan bayar ga matasa da ke tasowa ne. Ya kamata su zama mutane na gari kuma su tsaya a kan hanyar gaskiya da rikon amana. Sannan kuma kada su yi gaggawa a rayuwarsu. Su bi rayuwa a hankali, su sani cewa nasara tana samuwa ne da hakuri da gaskiya da rikon amana. Kada su yi marmarin zuwa kurkuku don rayuwa a cikinsa tana cike da kalubale da tashin hankali da kuma fargaba.