Yadda na mayar da Naira dubu 582 da na tsinta – Matukin Keke Napep
Saura kadan in haukace – Mai kudin A ranar Asabar da ta gabata ne wata mata mai suna Kelechi Ehandiba wadda aka fi sani da Mama Ejimeh ta manta kudinta Naira dubu 582 da 450 a cikin Keke Napep, inda matukin mai suna Bashir Usman ya mayar ma ta kudin. A lokacin da Aminiya ta […]

Saura kadan in haukace – Mai kudin
A ranar Asabar da ta gabata ne wata mata mai suna Kelechi Ehandiba wadda aka fi sani da Mama Ejimeh ta manta kudinta Naira dubu 582 da 450 a cikin Keke Napep, inda matukin mai suna Bashir Usman ya mayar ma ta kudin.
A lokacin da Aminiya ta tattauna da Bashir Usman ya bayyana cewa a lokacin da aka manta kudin a keken nasa ba shi da kudin da zai ciyar da iyalinsa. Ya bayyana cewa kudin da aka manta din sun kai dubu 582 da 450, “Na dauki matar wadda daga baya na gane sunanta Maman Ejimeh a layin Butcher dake kusa da Masallacin ’Yan Taya zuwa Hedikwatar ECWA, na dauke ta ne tare da wata abokiyarta, inda bayan sun sauka ne na ci gaba da ayyukana. Na dai fahimci an manta wata jaka, bayan na yi Sallar Magriba ke nan na nufi Titin Ring Road inda na sauke fasinjojina na karshe, bayan na je can ne na tambaye su sai suka ce ba na su ba ne,” a cewarsa.
Bayan ya isa gida ne suka bude jakar shi da matarsa ko za su ga wani abu da zai iya sa su gano mai jakar. “Abin da muka fara gani cikin jakar shi ne, katin shaidarta, ga dai sunanta, amma babu adireshin wurin da za a same ta, bayan mun ci gaba da dubawa sai muka ga Naira dubu 80 a cikin wata leda, sannan muka sake ganin Naira dubu 350 a cikin wata ledar, sai kuma Naira dubu 150 daban, inda kuma karamar jakarta akwai Naira dubu 3 da 450, sannan a cikin jakar akwai katin cire kudi (ATM) da magunguna da dama da sauransu.”
Ya bayyana cewa a lokacin da ya ga kudin hankalinsa ya tashi, domin a lokacin yana cikin mawuyacin hali, kasancewar ba shi da kudin da zai ba matarsa don ta sayi kayan abinci washegari. “A daren ranar ban iya barci ba, wata zuciyar tana ce mini in ci kudin don in magance matsalolin da suka sha kaina, yayin da wata zuciyar kuma ta rika ce mini in nemi mai kudin, na yanke hukuncin in nemi mai kudin ne bayan na tuna wani Hadisi da ya ce kada Musulmi ya ci haram. Don haka washegari sai na fita don in ci gaba da aiki bayan na kai wa mai Keke Napep din balas tukuna. Da rana bayan na koma gida sai matata ta tambaye ni ko na samu mai kudin sai na sanar da ita ai yau Lahadi ne mutane ba su cika fitowa da wuri ba, amma dai zan ci gaba idan an kai ga samun mai kudin zan sanar da ita,” in ji shi.
A ranar da abin ya faru ya dauki fasinjoji da yawa, “amma cikin ikon Allah sai na tuna fasinjojin da na dauka, inda na gane yawancinsu ba masu kaya ba ne, wasu daga cikin matan da na dauka suna dauke da karamar jaka ne, yayin da mazan kuma babu. Wadanda na dauka masu kaya su ne na sauke su a Ring Road, kuma na koma wurinsu sun ce ba jakarsu ba ce, cikin ikon Allah dai sai na tuna na dauki matar da abokiyarta a Layin Butcher, kuma sun shiga cikin babur din nawa da kaya.”
Ya ce, don haka sai ya nufi Layin Butcher, sai ya tambayi wani mai tura baro, shi kuwa ya ji labarin wata mata da ta manta kudinta a cikin Keke Napep, “sai ya ce mini ai sunanta Mama Ejimeh, shagonta na ciki, ya dai yi mini kwatancen shagonta, na bi kwatancen har na isa, a lokacin ban same ta ba, sai yaronta, shi ne ya kira ta a waya, ta ce tana zuwa.”
Ya bayyana cewa a lokacin da ta gan shi ta yi farin ciki sosai, inda ita da sauran mutanen kasuwar suka ba shi tukwuicin Naira dubu 27, sannan aka ba shi katan din Spaghetti da buhun shinkafa da na Semobita, sannan aka ba shi kyautar Madara da Milo da sabulai da sauransu.
A nata bangaren, Kelechi Ehandiba wadda aka fi sani da Mama Ejima, ta bayyana cewa daren da al’amarin ya faru ta kasa barci, inda ta rika yawo kamar mahaukaciya. “Ina da ’ya’ya biyu wadanda ’yan biyu ne, ina da shago a kasuwar Terminus, inda nake sayar da kayan masarufi. A yanzu shekarata 30, kuma a ranar da al’amarin ya faru ban iya barci ba.”
Ta ce mantuwar ta samo asali ne saboda tana da wani mutum da yake ba ta kayayyaki bashi, to sai ya bukaci ta kai masa kudin. “Mutumin yana sanya mini ranar da zan biya shi, kuma shi ya sanya ranar Juma’ar da abin yab faru. To a ranar kudin bai cika ba, shi kuma yana ta kirana in kai masa kudinsa, a ranar Asabar ya sake kirana yana so in kai masa kudin, bayan na kai masa kudin shagonsa a ranar Asabar din sai yarinyar shagonsa ta ce baya nan, na tambaya aka ce ya tafi wurin daurin aure.
Ta ce sai a lokacin ta tuna cewa za ta je wurin biki daya da shi, sai ta ce bari ta kai masa kudin wurin bikin kawai. “Na damu in kai masa ne saboda ba na so in samu matsala da shi, domin yana taimakona. Daga nan ne muka dauki dan keke daga Masallacin ’Yan Taya zuwa Hedikwatar ECWA. “Mun je wurin sai muka ga wadansu sun tashi daga bikin, inda suke kwashe rumfuna da kuma kujeru, hakan ya sa muka rude, muna tsammanin mun makara har an tashi. Sai na sauka daga babur din na tambayi wani sai ya yi mana kwatancen inda ake bikin. Ina juyowa sai na ga babu dan keken, na tambayi abokiyata sai ta ce mini ta biya shi har ya tafi, na ce mata to ina jakata? Sai ta ce ita kawai abubuwan da muka saya za mu ba ma’auratan ta dauko, ba ta san na ajiye jakata a ciki ba,” in ji ta.
Ta ce hankalinta ya tashi, ta rasa inda za ta sa kanta, daga nan “muka dauki wani mai keken muka bi hanyar ba mu same shi ba, muka sake bin wata hanyar ba mu gan shi ba. Sai na rika kuka, domin ban san ta yadda zan fara yi wa mai kudin bayani har ya gamsu ba. Na san da yawa ba za su yarda na manta kudin ba, za su ga kamar ba na so in ba da kudin ne. Washegari muka je tashar musu keke dake Terminus ko Allah zai sa mu gan shi amma ba labari, sai aka ba mu shawara muka kai cigiya gidan rediyo.”
Ta ce gidan rediyon ya ce sai mun biya kudin kafin a sanya cigiyar, to a lokacin ba ta da kudin, domin wannan zirga-zirgar ma aro suka yi. Washegari muka koma gidan rediyon don mu biya su kudin sanarwar da suka yi, ina kokarin biyan mai Napep din ke nan sai na ga kira daga yaron shagona, bayan na dauka sai ya ce mini an samu kudina, mai Keke din ya kawo. A lokacin na ji kamar mafarki nake yi, inda kuma kafin mu zo shagona an kai shi ofishin shugaban kungiyarmu ta ’yan kasuwa. A lokacin da na ga Bashir sai ta rungume shi, sannan na yi masa addu’a.