Yadda na rayu a kurukuku kwana 5 —Sanata Ndume
Sanata Ndume ya ce bai yi nadamar karbar belin Maina ba
Sakamakon gaza kai tsohon Shugaban Kwamitin Shugaban Kasa kan Sake Fasalin Fansho (PPRTT), Abdulrasheed Maina da ya tsaya wa beli gaban kotu, Sanata Muhammad Ali Ndume (APC, Borno ta Kudu) ya shafe kwana biyar a Kurkukun Kuje.
A tattaunawa ta musamman da Aminiya, Sanatan wanda shi ne Shugaban Kwamitin Sojin Kasa a Majalisar Dattawa ya ce bai yi nadamar karbar belin Maina ba, kuma ya bayyana yadda ya gudanar da rayuwa a kurukukun da huldarsa da manyan ’yan siyasa har da ’yan Boko Haram a kurukukun da sauransu:
Yaya za ka bayyana rayuwa a Kurukukun Kuje inda ka shafe kwana biyar saboda gaza kawo Maina kotu?
To tunanina ya ba ni cewa Mai Shari’a Okon Abang yana son ya daure ni, hakan ne ya zo min a zuciya.
Wannan ba daidai ba ne, amma a matsayina na Musulmi na yi imani Allah ne Ya hukunta hakan.
Kuma ba na kullace da kowa, ina da yakinin Allah Ya san dalilin yin haka.
Annabawan da Allah Ya zaba ma sun hadu da jarrabawa.
Don haka ban damu ba, kuma za ka ji mamaki idan na ce, na samu natsuwa da jin dadin kwana biyar da na yi a can.
Lokacin da aka sako ni na rika tunanin ko in kara wasu kwanaki ne a can.
Saboda na sani har cikin zuciyata ban aikata wani laifi ba, don haka ba ni da wani kunci a zuciyata.
Na karbi belin Maina ne saboda alkalin ya bukaci ni in yi belinsa, lokacin da ya sanya ka’idojin belin cewa tilas ne ya zamo sanata mai ci.
Kowane dan Najeriya kuma yana da sanata daya mai ci. Babu abin da ya hada ni da Maina, ba na da dangantaka da Maina.
Na fara haduwa da shi ne a rayuwata lokacin da na je kurukukun bayan ya dauki lokaci mai tsawo a can kuma ana yi masa jinya inda yake bukatar ya samu kula da lafiyarsa a wajen kurukukun.
Lokaci na biyu da muka hadu shi ne lokacin da ’yan sanda suka taso keyarsa daga Jamhuriyyar Nijar.
Kamar yadda na fada muku ina da nauyi a kaina kuma ni dan siyasa ne da aka san ni.
Kuma ka’idar da aka gindaya ta ce, mai yin belin wajibi ne ya kasance sanata mai ci.
Don haka mutane da dama daga mazabata suka yi ta rokon in yi belin sa.
Kuma laifin da ake zarginsa wanda ake iya bayar da belin sa ne, kuma tsarin mulki ya ce shi barrantacce ne har sai shari’a ta tabbatar da akasin haka.
Don haka ban san dalilin da ya yi abin da ya jawo aka tsare ni ba.
Kuma babu ta yadda za a yi alkali ya maye gurbin wanda ake zargi da mai belinsa.
Na tsaya beli ne kuma akwai dukiyar da na ajiye a matsayin yarjejeniyar belin, alkalin na iya neman ya ji dalilin da ba zan sallamar da dukiyar ba.
Amma kamar yadda na fada tun farko, Allah Yana da taSa manufar, kuma na ji mamakin martanin ’yan Najeriya da sauran jama’a a kan batun.
Me ya zo maka a zuciya lokacin da aka kai ka kurukuku?
Lokacin da nake zuwa kurukukun hankalina na kwance.
Bilhasali ma ba wannan ne karon farko na zuwa Kurukukun Kuje ba, a shekarar 2015 na shafe kwana 10 a can.
A matsayinka na dan siyasa ba za ka kware a siyasa ba musamman a kasashe masu tasowa in ba ka shiga kurukuku ba, don haka ban damu ba.
Amma ina gaya muku na ji dadin zaman. Hakan ya ba ni isasshen lokacin yin tunani da mayar da hankali a kan abubuwa biyu; Sallah da karanta littattafai.
Na huta sosai, saboda babu abin da ke damu na. Ba ni da tarho ko talabijin, ni kadai ne a dakina.
Na yi amfani da lokacina wajen bauta wa Allah domin na san jarrabawa ce kuma na roki in cinye ta.
Na tafi kurukukun ne a ranar Litinin ina yin azumi, bayan na sha ruwa sai na yi Sallar Magariba sannan Isha da sauran nafifili, sannan na kwanta barci da fatar in tashi cikin dare don wasu dalilai, sai na kwanta don in tashi da Asuba.
Na huta jinina ya sauka daga maki 150/90 lokacin da na je Kuje zuwa maki 135/80 lokacin da aka sallamo ni.
Ina shan magunguna ne a baya, don haka na yi raha cewa mai yiwuwa zama a kurukukun ne magani.
Na yi hulda da fursunoni daga dukkan sassa.
Mun haura 700, kuma abin da ya dame ni shi ne fiye da 600 suna jiran shari’a ne.
Akwai mutanen da suka shafe shekara takwas suna jiran a ci gaba da shari’unsu.
Wadanne ’yan siyasa ne ka hadu da su a kurukukun?
Wato muna da rukunoni, akwai na manyan fursunoni, shugabansu shi ne Rabaran Jolly Nyame tsohon Gwamnan Jihar Taraba, akwai Olisa Metuh da wani Yusuf daga Gombe da Iya Mashal Emmanuel.
Ka yi mu’amala da su?
Eh, na yi, muna da inda muke haduwa kullum da karfe 6:00 na safe zuwa karfe 6:00 na yamma.
Suna bari a motsa jiki duk da ni ban shiga cikinsu ba.
Olisa Metuh yana da kazar-kazar da haba-haba a wannan bangare kuma shi ne ko’odinetanmu.
Na hadu da rukunoni da dama kamar wadanda aka yanke wa hukuncin kisa da wadanda aka yanke wa hukuncin daurin rai-darai da wadansu kwamandojin Boko Haram, da aka daure su wajen 60.
Wadansu daga ’yan Boko Haram din suna nadamar abin da suka yi, amma wadansu kalilan suna nan da zafinsu.
Ko ka yi nadamar belin Maina?
A’a, ban yi ba.
Yadda lamarin yake a wannan hali da na samu kaina a wancan lokaci ba ni da zabi face in tsaya masa a matsayin mai beli.
Amma inda yanayin daban ne kuma bai fito daga mazabata ba, ba zan amince in yi ba.
Abin da ya faru an kaddara zai faru. Kuma ka san saboda yawan maganata, sai mutanena suka fara tunanin akwai wata manakisa a lamarin.
Amma ina tabbatar muku wannan ba gaskiya ba ne, kawai abin ya zo ne a arashi.
Wannan gwamnati, gwamnatina ce kuma ina kusa da Shugaban Kasa.
Amma akwai nauyi a kaina na in fada masa gaskiya kuma shi ne abin da nake yi.
Wannan bai mayar da ni ma’asumi ba, ko na fi kowa gaskiya ba, amma akwai bukatar in sanar da shi abin da ke cikin zuciyata.
Kuma a shirye nake in nemi afuwa ko in canja matsayina idan aka gamsar da ni cewa na yi kuskure, amma sabanin hakan, zan bayyana abin da ke cikin zuciyata.
Yaya kake kallon rashin tsaro da ke ci gaba a kasar nan?
Ni ina ganin batun tsaro da ke damun kasar nan ba magana ce ta Sufeto Janar ko Manyan Hafsoshin Tsaro ko Sanatoci ba; batu ne na tsaron rayukan mutanen kasarmu wanda shi ne manufar gwamnati.
Don haka ba na so mutane su rika suka ko dora laifi.
Ba haka ba ne, tsarin tsaron Najeriya ne ya sukurkuce, sannan kazar-kazar din sojoji da ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro ta yi kasa sosai, inda take bukatar mu farfado da ita.
Kamar ba mu da su ne; akwai bukatar mu dawo da sojoji da ’yan sanda da kazar-kazar din da aka san su da ita.
Suna bukatar a inganta su a samar musu da kayan aiki na zamani don gudanar da ayyukansu.
Wannan ne ya sa kananan masu laifi suke amfani da wannan dama suna hana mutane sakat.
An ba Shugaban Kasa damar ya yi wa kasa jawabi ta hanyar gayyatar da Majalisar Wakilai ta yi masa, amma aka shawarce shi kada ya je. Mene ne matsayinka kan wannan gayyata?
Bari in gaya maka, a gwamnatin da muke da rinjaye a majalisa, ba za mu sa Shugaban Kasa a tsakamai-wuya ba. In Buhari ya gaza APC ce har da Ndume suka gaza.
Don haka ba batu ne na Buhari ba, batu ne na APC domin ba shi kadai za mu dora wa laifi ba.
Shi ya sa na ce ba Shugaban Kasa ne kadai yake mulkin kasar nan ba, ba Shugaban Kasa ne komai ba, sai dai shi ne jagoran wannan gwamnati.
Gayyatar Shugaban Kasa ya zo ya tattauna al’amuran tsaro a gwamnatin da muke da rinjaye ba ita ce hanyar da ta dace ba.
Amma hakan ba ya nufin ba mu da ’yancin mu gayyaci Shugaban Kasar.
Sai dai a gayyaci Shugaban Kasa irin haka alhali muna jam’iyya daya ta hanyar bukata, to bukatar shawara ce, matsayar majalisa kamar ka ce ne muna shawartar Shugaban Kasa ya zo a tattauna batun tsaro, alhali kuna jam’iyya daya ce.
Me zai hana ku je ku zauna da shi ku tattauna hakan. Kuma a bangaren Shugaban Kasa ba za ka noke wa Majalisar Dokoki ta Kasa haka ba, Shugaban ya amince zai zo majalisa.
Alhakin shugabannin APC ne a majalisa su tabbatar duk lokacin da Shugaban ya zo majalisar ba su bari wani ya kunyata shi ba.
Lokacin da PDP ke da gwamnati suna yin taro a-kai -a-kai, amma matsalar ita ce akwai babban gibi a gwamnatin APC, wannan ne gaskiyar magana.
Ba mu aiki tare, akwai gibi sosai da yankewar sadarwa da alaka.
Ko a matakin jam’iyya akwai babban gibi, inda za a ga rikici nan da can, babu tsara abubuwa, babu alaka da shirya abubuwa.
Yaya za ka auna rawar da wannan gwamnati ta taka a bangaren tsaro?
Ba ni ya kamata ka yi wa wannan tambaya ba. Saboda ina daya daga cikin na gaba-gaba a wannan gwamnati, kana tunanin zan ce mun gaza? Ba zai yiwu ba, gwamnatin tana bakin kokarinta.
Kuma ban yarda Shugaban Kasa bai damu da halin da ake ciki ba.
A lokuta da dama nakan je mu tattauna da shi kan wadannan matsaloli wani lokaci ya gayyace ni saboda ya san na fito daga inda ya fi fama da ’yan ta’adda inda muke tattauna hanyar nemo mafita.
Muna tattauna wannan amma samun nasara wani batu ne na daban.
Kuma ba za ka kwatanta wannan gwamnati da wadda ta gabace ta ba.
Wannan gwamnati ta karbi mulki ne a 2015 inda a waccan lokaci an mayar da karamar hukumata hedkwatar Daular Boko Haram, amma a yau mahaifina ya koma Gwoza da zama. Sarkinmu ya koma Gwoza.
Ina tunawa lokacin da Boko Haram ke kan ganiyarta Sarkinmu ya gudu daga Gwoza ya yi tafiya a kasa zuwa Madagali (a Jihar Adamawa) kafin a ceto shi a kawo shi Abuja inda ya yi wata uku kafin a mai da shi Maiduguri.
Don haka ba za a kwatanta yanayin ba, domin mun fi samun sa’ida a wannan gwamnati.
Amma ba za a ce mun cimma abin da muke so ba. Saboda ba mu yi tsammanin samun nasara rabi-da-rabi ba a yaki da ta’addanci.
Mun sa ran samun nasara a yakin ne gaba daya a kankanen lokaci, amma sai ga shi ya ki ya kare.