Yadda na samar wa masu lafiya ayyukan yi – Nakasasshe

Jaridar Aminiya ta zanta da wani matashi nakasasshe a rabin jikinsa ta yadda daya daga cikin hannunwansa bai aiki sosai, mai suna Akinyemi Olalekan, wanda ya mallaki makarantar nazare da firamare ta Mighty Hands a garin Abeokuta, Jihar Ogun, inda ya fadi irin fadi-tashin da ya yi har ya kai ga mallakar makarantar, kuma ya […]

Yadda na samar wa masu lafiya ayyukan yi – Nakasasshe

Jaridar Aminiya ta zanta da wani matashi nakasasshe a rabin jikinsa ta yadda daya daga cikin hannunwansa bai aiki sosai, mai suna Akinyemi Olalekan, wanda ya mallaki makarantar nazare da firamare ta Mighty Hands a garin Abeokuta, Jihar Ogun, inda ya fadi irin fadi-tashin da ya yi har ya kai ga mallakar makarantar, kuma ya dauki ma’aikata da ke taya shi aiki:

 

Mene ne takaitaccen tarihinka?

Sunana Akinyemi Olalekan, an haife ni a1979 a garin Agege a Jihar Legas. Na samu matsalar nakasa ce ina da shekara uku a duniya a 1983 sakamakon ciwon kyanda.

Yaya aka yi ka samu kwarin gwiwa har ka mallaki makaranta?

Hakika da taimakon iyayena da kuma sha’awata ga karatu na samu kwarin gwiwa har na yi  karatu a Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Legas inda na samu takardar malanta ta kasa (NCE), bayan na yi firamare a makarantar Saint Sabiour da sakandare a Jubril Martins a Agege.

Ko akwai kalubalen da ka fuskanta lokacin karatunka kasancewarka nakasasshe?

A gaskiya ban samu kalubale da yawa ba lokacin karatuna. Sai dai matsalar rashin kudi kana ba na iya yin rubutu cikin hanzari. Amma da taimakon mahaifiyata da na malaman makaranta na samu damar cimma burina na karatu, domin mu hudu mahaifiyarmu ta haifa, ni kadai ke da nakasa, kuma ni kadai na samu zarafin yin karatu.

Ka taba yin bara kasancewarka mai nakasa?

Ban taba  yin bara ba, domin bara kaskanci ce. Na fara aikin koyarwa tun bayan da na kammala karatun sakandare har na kai ga mallakar makarantata, wacce na faro ta daga yi wa yara darussa a gida. Makarantar nazare da firamare ta Mighty Hands, muna da dalibai sama da 50 wadanda shekarunsu ya fara daga biyu zuwa 10, kuma na dauki ma’aikata da dama da ke aiki a karkashina. Baya ga malaman makaranta, ina da ma’aikatan da ke kula da yara kanana idan sun yi fitsari ko kashi sannan ina da wadanda ke ayyukan share- share da goge-goge. Na kama hayar ginin makarantar ce, burina nan gaba in mallaki filin da zan gina katafariyar makaranta domin in ci gaba da bada gudunmawata ga al’umma. Kuma akwai shirin da nake yi domin daukar nakasassu aiki domin cusa masu akidar dogaro da kai tare ba su horo.