Yadda na samu jari na fara kasuwanci
Ibrahim Alkasim, wani nakassashe ne da ya samu hadarin da ya sa har aka yanke masa hannunsa daya, amma ya nisanci bara, inda yanzu yake tireda ne a tsakiyar birnin Abuja. Aminiya: Mene ne tarihinka? Sunana Ibrahim Alkasim, ina da shekaru ashirin da biyar, kuma ni mutumin karamar Hukumar Dawakin Tofa ne da ke Jihar […]
Ibrahim Alkasim, wani nakassashe ne da ya samu hadarin da ya sa har aka yanke masa hannunsa daya, amma ya nisanci bara, inda yanzu yake tireda ne a tsakiyar birnin Abuja.
Aminiya: Mene ne tarihinka?
Sunana Ibrahim Alkasim, ina da shekaru ashirin da biyar, kuma ni mutumin karamar Hukumar Dawakin Tofa ne da ke Jihar Kano. Yadda na samu nakasa har na rasa hannu daya shi ne, muna karatun allo, kuma muna aikin dibar yashi da kai taki gona a kan jaki don neman na kai lokacin ina da shekaru goma, na kai taki ina dawowa a guje a kan jaki sai ya bi ta jikin wata itacen tsamiya, inda kafadata ta bugi bishiyar har na fado a kan hannun hagu na karye. Bayan an dora ni, amma dorin bai yi kyau ba. Da muka je asibiti aka kwance, sai aka ga hannun ya fara rubewa bayan na yi shekaru uku ina jinya. Aka yanke hannun aka yi min maganin har na warke.
Aminiya: Ya aka yi ka fara tireda a Abuja?
Shekaru hudu ke nan da zuwa na Abuja, na fara sayar da ruwan sha na roba watau “pure water” a Eriya Wan “Area One”, da na samu dan jari sai na koma sayar da jakunkunan mata, ina ratayawa, ina talla. Ana nan, anan sai wani wanda yake zuwa da kaya a tashar motar Nyanya da Maraba, mutumin Katsina shi ma nakassashe ne na kungiyar nakasassu, masu kasuwanci da ke Area one ya ce za shi ganin gida in zo in kula masa da kaya. Ya ce ya yarda da halaye na, ya ce ba zai yi lissafin kayan da ya bar min ko ya dawo ya tarar ba, amma abin da na samu in cire wahalata in aika masa da wani kaso ta banki, sannan in juya jari. Haka muka yi har ya dawo. Muna sayar da caja ta wayar salula, da buroshi na goge baki, da man kyasbi da na kurarraji da sauransu. Da ya dawo na bashi kayan da abin da ke hannu sai na tashi da Naira dubu goma, su na fara jari da su inda na ware gefe na dawo tsallake jikin katangar kamfanin kwangila gini-gine na Julius berger zuwa Utako a shekara daya da ta wuce.
Aminiya:Ya kake yi a lokacin damina?
Ina kwashe kayan ne in mayar a jaka, sannan in rataya zuwa karkashin gadar-sama ta berger in fake da sauran marasa mota, har sai ruwan ya dauke. In dare ya yi in hau mota Naira dari in koma masauki in kwana, da safe in biya Naira dari in dawo.
Aminiya: Ya kuke da tsaron kayanku maganin barayi a inda kuke ajiya da gun da kuke kasuwanci?
Inda nake ajiye kayan amintattu ne, kuma muna ta addu’a.
Aminiya: Ya kuke fama da jama’a iri daban-daban na Abuja, inda kusan kowa mai gaugawa ne?
Abin ai dace ne, wani ka ce masa sannu “Kwastoma” watu mai ciniki ya amsa, wani kuma ya yi biris da kai. Abin mamaki shi ne, idan don sabo, wasu in sun tarar da ni ina barci, sai su tashe ni, su sayi kaya, wasu kuma su wuce. Ina son in jari ya samu in kama hayar shago a kasuwa.
Aminiya: Wacce shawara za ka ba masu matacciyar zuciya?
Ai komai kankantar ta sharawata ita ce su rika neman na kansu, kada a raina sana’a kowace iri ce. A bar yin bara, don an hana yin bara a Abuja, kuma a daina yin dan hali, wato sata, don doka na aiki kwarai a Abuja.