Yadda na samu motata bayan wata biyar da sace ta- Kamal S. Alkali

A ranar Juma’ar makon jiya ne motar fitaccen darakta Kamal S. Alkali ta dawo hannunsa bayan wata biyar da sace ta a Abuja. Idan masu karatu ba su manta ba mun kawo muku labarin yadda barayi suka bugar da darakta Kamal S. Alkali da mawaki Nazifi Asnanic a wani otal da ke Gwagwalada har suka […]

Yadda na samu motata bayan wata biyar da sace ta- Kamal S. Alkali

A ranar Juma’ar makon jiya ne motar fitaccen darakta Kamal S. Alkali ta dawo hannunsa bayan wata biyar da sace ta a Abuja.
Idan masu karatu ba su manta ba mun kawo muku labarin yadda barayi suka bugar da darakta Kamal S. Alkali da mawaki Nazifi Asnanic a wani otal da ke Gwagwalada har suka sace musu mota da laptop da wayoyinsu da kuma Naira dubu 40.
Daraktan ya yi wa wakilanmu bayanin yadda motar ta dawo wurinsa bayan wata biyar da sace ta.
Ya ce: “Bayan mun kammala jinya a gida da wadansu kwanaki, sai na ga an fara amfani da wayar Blackberry dina, lokacin da aka sace mana motar sun hada da laptop da kuma wayoyinmu ne. Wani soja ne ya fara amfani da ta Nazifi. Daga baya sai wata budurwa ta fara amfani da tawa. Blackberry tana da wata manhaja da idan kana chatting da abokanka sai kuma ka bari, sannan wani ya karbi wayar to zai iya ci gaba da chatting da abokanka. Don haka bayan an dauke tawa ne sai ban ci gaba da yin chatting din ba, wacce ta mallaki wayar daga baya sai ta ci gaba da amfani da wayar inda kuma ta ci gaba da chatting da abokaina.”
Ya ce, bayan ya gano hakan sai ya sanar da ‘yan sandan Gwagwalada wadanda suke bincike a kan al’amarin. Inda ya yi musu bayanin abokinsa ne yake soyayya da ita kuma tana Abuja, daga nan aka ba su takardar kama wacce ake zargi, inda suka zo gidansu da ke Legislators kuarters a Apo. Bayan sun je gidan ne mahaifinta ya fito suka yi masa bayanin komai, sannan ya yi alkawarin kawo ta ofishin ‘yan sandan.
“Bayan ya kawo ta ne ‘yan sanda suka yi mata tambayoyi, inda a nan aka gane saurayinta ne ya ba ta wayar, ashe kuma sun taho da saurayin. Shi kuma saurayin ya fadi wurin da ya samu wayar. Abin mamakin shi ne ya samu wayar ne a Makarfi Plaza da ke Kaduna bayan ya kai gyaran wayar budurwar tasa. Masu gyaran wayar ne suka ba shi aron wayata shi kuma sai ya kawo wa budurwarsa don ya faranta mata.
“Daga nan aka je Kaduna  aka taho da masu gyaran waya, inda daya daga cikinsu ya ce wadansu ne suka kawo masa, shi kuma ganin arha sai ya saya.  Bayan ‘yan sanda sun tsananta bincike ne sai suka gane ba shi da alaka da barayin da suka sanya mana guba, hakan ya sanya aka ba ni wayata da kuma laptop dina.” Inji Kamal.
Bayan ya dawo Kano sai wata ‘yar sanda da al’amarin yake hannunta a Gwagwalada ta kira shi ta shaida masa tana tsammanin Sashin Yakin da Fashi da Makami a Abuja (SARS) sun kama wadansu barayi kuma tana zaton har da barawon motarsa, amma dai ya je ofishinsu ya bincika. “Haka na je ofishinsu na dawo Kano ba tare da ganin wanda al’amarin yake hannunsa ba, amma na nemi lambarsa, na kuma kira shi, na yi masa bayani.”
“Daga baya ne na tura masa lambar injin motar da sauran bayanan da sai motar ne kawai zai iya saninsu, hakan ta sanya ya sanar da ni tabbas an kama barawon motar, amma ba shi ne wanda ya damfare mu ba, abokinsa ne, amma dai yana so ya gan ni a Abuja.” Inji shi.
Bai yi kasa a gwiwa ba ya tafi Abuja inda ya samu jami’in mai suna Sani Dabo, sannan ya sake yi masa bayani.  Jami’in ya ce suna da makamanciyarta. Daga nan ya hada shi da yaronsa mai suna Yobo suka je ofishin SARS din, aka nuna masa motocin da suka kama, “a nan na ga tawa, ciki farin cikin na yi sujudar yi wa Allah godiya.”
“A nan aka ci gaba da bincike, binciken da ya dauke su wata guda wanda  ya sanya suka ba ni motata a ranar Juma’ar makon jiya  bayan sun tabbata tawa ce.” Ya ce daga karshe.
Da aka tuntubi Babban Jami’in hulda da jama’a ta rundunar ‘yan sandan Najeriya Frank Mba ya tabbatar da faruwar al’amarin har ya ce an kai wadanda aka kama din kotu har an kusa kammala shari’a.