Yadda na sayi Toyota Camry a kan N2,650 —Dan damfara
Dubunsa ta cika bayan ya damfari dillalin motar ya kai ta a canza mata fenti
Wani matashi da ya damfari masu sayar ta motoci inda ya sayi mota kirar Toyota Camry a kan Naira dubu biyu da dari shida da hamsin ya shiga hannu.
Matashin ya damfari wani daillalin motoci ne da kudin motar wadda kudinta ya kai Naira miliyan 2.6.a garin Osogbo na Jihar Osun.
Matashin na daga cikin wasu mutum 10 da ake zargi da aikata manyan laifuka da Rundunar ’Yan Sandan Jihar ta yi baje kolinsu a ranar Juma’a a garin na Osogbo.
A lokacin da Kwamishinna ’Yan Sandan Jihar Osun, Wale Olokode, ya gabatar da su, mutumin ya shaida wa Aminiya cewa ya je wurin masu sayar da motoci ne ya zabi motar kirar Toyota Camry wadda ake wa lakabi da ‘Muscle’, suka yi ciniki da mai ita har suka daidaita a kan Naira miliyan biyu da dubu dari shida da hamsin.
Bayan sun daidaita sai ya bukaci mai sayar da motocin ya ba shi lambar bankinsa ya tura mishi kudin, shi kuma ya ba shi.
Ya tabbatar wa Aminiya cewa a maimakon ya tura kudin motar, sai ya tura Naira dubu biyu da dari shida da hamsin, wanda bayan shigarsu ya karbi rasidin Naira miliyan 2.65 ya tafi da motar, bai tsaya ko’ina ba sai wurin da za a canza wa motar fenti.
Daga baya ne mai sayar da motocin ya bude sakon shiga kudin, ya ga ashe N2,650 matashin ya tura mishi ba Naira miliyan 2.65 ba.
Nan take ya sanar da ’yan sandan kuma suka yi nasarar kama wanda ake zargin tare da mai fentin motocin.
Kwamishinna ’yan sandan jihar ya ce ana ci gaba da gudanar da bincke a kan lamarin domin gurfanar da su a kotu.