Yadda na shafe kwana 5 a hannun masu garkuwa da mutane – Manajan Kamfani

Manajan wani kamfanin harkar sayar da kayan aikin gona a garin Suleja Jihar Neja ya kubuta daga masu garkuwa da mutane bayan ya shafe kwana biyar a hannunsu a wani daji da ke kusa da garin Fadaman Abuchi, kamar yadda ake kyautata zato.  Da yake bayyana wa Aminiya lamarin a ranar Talata da ta gabata, […]

Yadda na shafe kwana 5 a hannun masu garkuwa da mutane – Manajan Kamfani

Manajan wani kamfanin harkar sayar da kayan aikin gona a garin Suleja Jihar Neja ya kubuta daga masu garkuwa da mutane bayan ya shafe kwana biyar a hannunsu a wani daji da ke kusa da garin Fadaman Abuchi, kamar yadda ake kyautata zato. 

Da yake bayyana wa Aminiya lamarin a ranar Talata da ta gabata, Manajan mai suna Malam Muhammad Nasir ya ce ya ci karo da mutanen ne a ranar Larabar makon jiya a yankin Chaza da ke bayan garin Suleja bayan ya kai ziyara a gidan wani Baffansa da misalin karfe 8 na dare tare da matarsa da kuma wata ’yar uwarsa a motarsa.

Ya ce “Bayan tafiya ta dan lokaci sai na ji harbin bindiga sannan aka sake harbawa, da farko na dauka karar abin wasan yara ne kafin harbi na uku wadda na gane harbin bindiga ce sannan na rage gudu. Nan take suka sa wa motarmu waigi bayan na tsaya sai kawai suka jawo mu waje suka bukaci matata da ’yar uwata su kwanta.”

Ya ce da suka gane wace ce matarsa sai suka sallami ’yar uwar tasa da ke tare da danta sannan suka ja shi zuwa cikin daji tare da matarsa, kafin daga bisani ita ma su sallame ta bayan sun gane cewa tana dauke da tsohon ciki saboda ba ta iya sauri.

“Mun yi tafiya kamar ta awa biyu kafin mu kai inda sansaninsu yake kuma a wurin ne na shafe kwana biyar, inda da safe muke gangarowa wani wuri da ke bakin rafi a gefen tsauni sannan idan gari ya waye mu shiga cikin kurmi inda suke rufe fuskata kuma su daure ni a jiki bishiya.” 

Ya ce Fulatanci suke yi duk da cewa ba ya gane abin da suke fada, idan suna tattaunawa. 

Ya ce da farko mutanen sun bukaci fansar Naira miliyan 20 daga hannun iyalansa kafin su sassauto zuwa Naira miliyan biyar, a karshe kuma suka sake shi bayan sun karbi Naira miliyan biyu a ranar Litinin da ta gabata ya bar inda suke rike da shi da misalin karfe 7 na yamma ya isa gida da misalin karfe 10 na dare.